Ambaton Allah madaukakin sarki


6189
Surantawa
Zikiri ga zuciya kamar ruwa ne ga kifi, yaya kifi zai kasance idan babu ruwa? Haqiqa addinin musulunci ya kwadaitar wajen sadadda mutum da ubangijin sa, domin zuciyar sa ta rayu, kuma ransa ya tsarkaku, kuma ya nemi temako da dacewa daga ubangijin sa. Dalilin haka nema abubuwan da zasu janyo hankalin jamaa zuwa ga ambaton Allah a kowane irin yanayi suka zo a qurani da sunna, tare da sanya nauoi da dama na zikiri a lokuta daban-daban.

Manufofin huxubar

Bayanin girman sha’anin zikiri a rayuwar musulmi.

Kwaxaitarwa a kan ambaton Allah a kowane hali.

Qarfafa alaqar bawa da Ubangijinsa.

Gargaxi kan gujewa ma’abota gafala da mantuwa

Huxuba Ta Farko

Dukkan Yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma mua neman tsarinsa daga sharrin kawukanmu da munanan aiyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar dashi, wanda kuma ya atar babu mai shiryar da shi, kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai allah, shi kaxai ne bashi da abokin taraiya, kuma ina shaidawa cewa Annabi Muhammad bawansane manzonsane, (Yaku waxanda kuka bada gaskiya kuji tsoron Allah yadda ya cancanta aji tsoronsa, kada ku mutu face kuna Musulmi). (Yaku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicce ku daga rai guda xaya kuma ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga gare su (su biyu) kuji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya dashi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Ya ku waxanda suka yi imani kuji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku aiyukanku, kuma ya gafarta muku zunubanku. Wanda ya bi Allah da manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawun shiriya shiriyar Annabi Muhammadu (ﷺ) kuma mafi sharrin al’amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wata bidi’a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta.

Bayan haka, ina yi muku wasiyya ya ku mutane, da kaina da tsoron Allah Mai buwaya da xaukaka, ku ji tsoronsa a voye da sarari, ku ji tsoronsa, ku bauta masa, ku yi sujadda a gare shi, ku aikata alheri, tabbas za ku rabauta.

Ya ku mutane! Haqiqa zukatan 'yan Adam kamar sauran abubuwa ne masu rai, suna da buqatar abubuwan da duk mai rai yake da buqatar don ya rayu, ya havaka. Kuma duk masu hakali sun haxu a kan cewa zukata kan yi tsatsa kamar yadda qarfe kan yi tsatsa, kuma suna jin qishirwa kamar yadda tsiro kan ji qishirwa. Kuma suna bushewa kamar yadda hantsa kan bushe. Don haka, su ma suna buqatar a riqa goge masu tsatsarsu. A shayar da su a gusar musu da qishi. Mutum a wannan rayuwa, kewaye yake da maqiya ta kowane gefe, ga zuciyarsa mai yawan umartarsa da mummuna aiki, tana tura shi ramin hallaka. Hakan nan son zuciyarsa da shaixaninsa suma suna nasu qoqar. Don haka yake cikin matuqar buqatar abin da zai kare shi ya amintar da shi, ya kwantar masa da tsoro, ya sanya nutsuwa a zuciyarsa. Kuma mafificin abin da yake yaye irin waxannan cututtuka, yake karewa daga maqiya, shi ne ambaton Allah, da yawaita wannan ambaton ga mahaliccinta abin bautawarta. Domin Shi ne, mai goge zukata, mai darje su, kuma maganininsu idan cututtuka su sun lulluve su.

Ibnulk Qayyim Allah ya jiqansa ya ce “Na ji shakhul islam Ibn Taimiyyah Allah ya tsarkake sirrinsa, yana cewa: ”Zikiri ga zuciya kamar ruwane ga kifi, yaya kifi zai kasance idan ya rasa ruwa?”

Ya ku bayin Allah! Alqa tsakanin bawa da Ubangijinsa ba ta taqaita a kan lokacin ganawa da shi da safe ba ko da yamma kawai. Sannan daga nan kuma mutum ya tafi harkarsa ta duniya yana abin da ya ga dama ba tare da wani qaidi ko takunkumi ba. Sam a’a, yin haka addini ne na boge ba na gaskiya ba. Alaqa ta gaskiya tsakanin bawa da Ubangijinsa ita ce, mutum ya ambaci Ubangijinsa ako ina yake, kuma wannan zikirin ya kasance yana sa masa takunkumi na bin umarnin Allah da haninsa, kuma yana wa xan adam bushara da rauninsa, kuma yana taimaka masa a wajen fakewa zuwa Ubangijinsa cikin duk abin da zai biyo masa.

Ya ku bayin Allah!

Haqiqa addini maiqaqqe ya zaburar a kan musulmi ya kasance qulla alaqa da Ubangijinsa, don ruhinsa ya rayu, zuciyarsa ta tsarkaka, ya sami taimako da dace daga gare shi. Don haka, nassosi da suke kira zuwa ga ya waita zikiri suka zo a cikin Alqur'ani da sunnar Annabi (ﷺ). Allah Ta’ala Ya ce

( يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا اذْكُرُوا اللَّهَ ذِكْرًا كَثِيرًا 41 وَسَبِّحُوهُ بُكْرَةً وَأَصِيلًا 42 ) [الأحزاب: 41 - 42]

(Ya ku waxanda suka yi imani, ku ambaci Allah ambato mai yawa. Kuma ku tsarkake shi da safiya da maraice).

Hakanan Allah ya ce,

( وَالذَّاكِرِينَ اللَّهَ كَثِيرًا وَالذَّاكِرَاتِ أَعَدَّ اللَّهُ لَهُمْ مَغْفِرَةً وَأَجْرًا عَظِيمًا 35 ) [الأحزاب: 35]

(Da masu ambaton Allah maza, da masu ambato Allah mata, Allah ya tanadar musu da gafara da lada mai girma). Kuma Allah Ya ce,

( وَلَذِكْرُ اللَّهِ أَكْبَرُ ) [العنكبوت: 45]

(Kuma lalle ambaton Allah shi ne mafi girma).

Ya ce, (kalmomi biyu ababen so ne ga Allah mai rahama, sauqaqa ne a kan harshe, masu nauyi ne a kan ma’auni: subhanallahi wabihamdihi, subhanallahil azim). Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.

Kuma ya ce “Yanzu ba na ba ku labarin mafi alherin ayyukanku ba, kuma mafi tsarkakarsu a wajen Mamallakinku ba, kuma mafi xaukaka ga darajarku, kuma mafi alheri a gare ku fiye da zinare da azurfa, kuma mafi alheri fiye da ku gamu da abokan gabarku ku doki wuyayensu, su ma su doki wuyayenku! Suka ce, “Wannan mene ne kuwa, ya Ma’aikin Allah?”. Sai ya ce, “Ambaton Allah Mai buwaya da xaukaka”. Ahmad ne ya raiwato shi.

Kuma Annabi (ﷺ) ya ce, “Wanda ya ce, Subhanallahi wa bi hamdihi za a dasa masa dabinai a Aljanna”. Tirmizi ne ya rawaito shi.

Ya bayin Allah! Da zikiri ne ake ije cututtuka, ake yaye baqqan ciki, kuma masifu kan zama masu sauqi a kan wanda suka aukawa. Allah ya qawata harasan masu zikir da shi, kamar yadda ya qawata ganin masu gani da haske. Gafalallen harshe, kamar makahon ido ne, ko kurman kunne, ko shanyayyen hannu.

Ambaton Allah mai buwaya da xaukaka buxaxxiyar kofa ce tsakanin bawa da Ubanagijinsa, matuqar bawa bai rufe ta da gafalarsa ba.

Hasannul Basari Allah ya jiqansa ya ce, “Ku nemi daxin xanxano cikin abubuwan uku: cikin Sallah, da zikiri da karatun alqur’ani, idan kun samu to, in ba haka ba to ku sani cewa qofar a rufe take”.

Ya ku musulmi! Haqiqa zunubai manyansu da qananansu ba zai yiwu ‘yan’adam su aikata su ba face sai cikin hali na gafala da manta ambaton Allah; domin ambaton Allah Ta’ala, tsani ne na cikakkiyar rayuwa wanda zai yi wuya, mutum yana tare da ita, kuma ya jefa kansa cikin tanderun jahimu, ko fushi da uqubar Ubangiji mai girma. A xaya gefen, mai barin zikiri, da mai manta shi, shi matacce ne, shaixan bai damu a wane juji zai jefa shi ba.

Allah Ta’ala ya ce:

( وَمَنْ يَعْشُ عَنْ ذِكْرِ الرَّحْمَنِ نُقَيِّضْ لَهُ شَيْطَانًا فَهُوَ لَهُ قَرِينٌ 36 ) [الزخرف: 36]

(Kuma duk wanda ya makance ga barin ambaton mai rahama za mu hore masa shaixani sai ya zama abokinsa).

Kuma Allah Ta’ala ya ce,

( وَمَنْ أَعْرَضَ عَنْ ذِكْرِي فَإِنَّ لَهُ مَعِيشَةً ضَنْكًا وَنَحْشُرُهُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ أَعْمَى 124 ) [طه: 124]

(Duk wanda ya kau da kai ga barin ambaton Allah mai rahama, to yana da rayuwa mai qunci, kuma za mu tashe shi ranar alqiyama a makaho).

Ibn Abbas (R.A) ya ce “Shaixan a gurfane yake da a kan zuciyar xan adam. Idan ya gafala ya yi rafkanarwa sai ya yi masa wasi-wasi, idan kuwa ya mabaci Allah sai ya noqe”

Wani mutum ya kasance a bayan Manzon Allah (ﷺ) a kan wata dabba, sai dabbar ta yi tuntuve da su, sai mutumin ya ce “Shaixan ya tabe”. Sai Annabi (ﷺ) ya ce masa, “Kada ka ce, Shaixan ya tabe, domin alokacin zai ciko har ya zama kamar girman gidan nan. Ka dai ce, Bismillahi, to alokacin sai ya qanqance har ya koma tamkar quda” Ahmad ne ya rawaito da Abu Dawud kuma ingatancce ne.

Ibnul Qayyum Allah ya jiqansa ya rawaito daga sashin magabata; cewa, idan zikiri ya kankama a zuciya, to idan shaixan ya kusanto mutum, sai mutumin ya kada shi, kamar yadda shaixan yake kada mutum. Sai shaixanu su taru a kansa, suna cewa, me kuma ya sami wannan? Sai a ce, ai mutum ne ya shafe shi”

Yawaita ambatun Allah maganin munafunci ne, kuma ‘yantuwa ne daga ribatar son zuciya, kuma dama ce da ke sadar da bawa zuwa yardar Ubangijinsa, da abin da ya tanadar masa na ni’ima madauwamiyya. Zikiri makami ne da ake ba wa mutum, daga makamai na yaqi waxanda ba sa dakushewa. Domin hadisi ya tabbata daga Annabi (ﷺ) game da buxe Qusxanxiniyya, ya ce, “Yayin da suka zo ganuwarta, sai su sauka, ba za su yi yaqi da makami ba, ba za su yi jifa da kibiya ba. Za su ce, la’ilaha illaha wallahu akbar: sai xaya daga vangarorinta biyu na ganuwa ya faxi. Sannan su qara cewa, La’ilaha illallah, wallau akbar, sai xaya vangaren kuma shi ma ya faxi. Sannan su faxa a karo na uku: la’ilaha illallah wallahu akabar, sai a buxe musu, sai su shige ta, su sami ganima…” Muslim ne ya rawaito shi.

Ya ku mutane! Ambaton Allah Ta’ala shi ne mafi darajarar abin da zai xarsu a zuciya, kuma mafi tsarkin abin da baki zai furta, kuma mafi xaukakar abin da hankalin wayayyan musulmi zai haskaka da shi. Mutane gabaxaya sukan sami damuwa a rayuwarsu, ko su sami kasawa, saboda damuwa da za ta kewayesu ta ko’ina, alhali su raunana ne ba za su iya xauke wa kansu wannan wahalhalun ba idan sun sauko musu, ko su ije su idan sun kusa afko musu. Duk da haka ambaton Allah yana raya jin girman Allah a zukatansu, da jin cewa shi mai iko ne a bisa kowane abu, kuma babu wani abu da zai kuvuce daga qarfinsa, kuma shi ne yake yaye abin da ya sami mutum na wahala. A yayin nan ne mai zikiri zai ji farin ciki da nutsuwwa sun lulluve zuciyarsa da gavvansa. Allah yana cewa,

( الَّذِينَ آَمَنُوا وَتَطْمَئِنُّ قُلُوبُهُمْ بِذِكْرِ اللَّهِ أَلَا بِذِكْرِ اللَّهِ تَطْمَئِنُّ الْقُلُوبُ 28 ) [الرعد: 28]

(Waxanda suka yi imani kuma zukatansu ke nutsuwa da ambaton Allah. A saurara lallai da ambaton Allah ne zukata kan nutsu).

Ya kai musulmi! Ba za ka ji tsoron wani vacin rai ba ko damuwa, matuqar kana tare da ambaton Allah. Allah mai girma da xaukaka yana faxa a xikin hadisi qudusi; “Ni ina nan wajan zaton bawa ne, kuma ina tare da shi idan ya ambace ni, idan ya ambace ni a ransa zan ambace shi a raina. Idan ya ambace ni a cikin taro, zan ambace shi a ciki taro mafi alheri daga wannan taron nasa”. Bukhatari da Muslim ne suka rawaito shi.

Sayyadina Ali da Nana Faxima (R.A) sun kai kuka wajen Manzon Allah na abin da take fuskenta na niqa da aiki mai wahala, sai ta roke shi xan aiki, sai Manzon Allah ya ce, “Yanzu ba na shiryar da ku zuwa abin da ya fi xan aiki alheri ba, idan za ku kwanta, ku yi Tasbihi talatin da uku, ku yi Tahmidi talatin da uku, ku yi Takbiri talatin da huxu, wannan xari kenan a harshe amma dubu a ma’auini. Aliyu ya ce “Ban tava barin su ba tun da na ji su daga Annabi (ﷺ), wani mutum ya ce “Har a daren yaqin Siffin?" Ali ya ce, "Har a daren yaqin Siffin". Ahmad ya rawaito shi. Daren Siffin: shi ne daren yaqi mai tsanani da ya afku tsakaninsa da abokan faxansa, mutanen Sham. Allah ya yarda da su baki xaya.

Ya ku bayin Allah! Da xayanmu zai kallafawa kansa ganin wani abu da kan faru akai-akai, wato irin mutane da gafala da qarancin zikiri kan halakar da su. Yanzu dubi irin duhun gidajen da suka wafinta daga ambaton Allah! yanzu dubi marasa lafiya galavai tattu, Allah ya sallamasu ga kaeukansu, yayin da suka manta shi. Sai ba suka kasa xora qashin da Allah ya karya. Suka qara cuta a kan cutarsu, yanzu dubi waxanda ake yi wa sihiri maza da mata, hannayensu masu sihiri da dabo da maqaryata 'yan damfara sun kai ga cimma su. Sun raba su da jin daxin rayuwa. sun raba su da kwanciyar hankali, sun rushe musu gidan rayuwa na sa'ada gabaxaya.

Me ya hana xayanaku ya yi tunani a game da waxannan da aka jarrabe su da shafar maridan aljanu ba shaixanun suna jin raxaxi suna birgima kamar masu birgima a kan qonannanan rairayi. Shaixanu suna makarsu. Sun kasa zama guri guda, kuma sun kasa samun kwanciyar hankali. Ku faxa min gaskiya – Ya ku bayin Allah - xayanku ba zai tambayi kansa cewa, mai hana waxannan wahalallu ambaton Allah ne? Me hana su fakewa a cikin qarfafan ganuwoyi na Ubangiji, waxanda su ne za su magance musu duk wata cuta mai karya garkuwar jiki?! Shin waxannan ba su sani ba, cewa shiga gida da fita daga cikinsa yana da zikiri? Shin ba su sani ba cewa, bacci yana da zikiri, hakanan tashi daga barci yana da nashi? Shin ba su sani ba cewa, safiyar kowace rana tana da zikiri, hakanana ma maraice, kai hatta tarawa da iyalinsa akwai zikiri, kai har shiga ban xaki da fitowa daga cikinsa? Kowanne abu yana da zikiri, yadda ya zo mana daga ma’aiki (ﷺ) wanda ya sani ya sani, wanda ya jahilta ya jahilta.

Ya ku musulmi ku ji tsoron Allah “Ku ambaci Allah ambato mai yawa, tabbas za ku rabauta.

Ina faxar abin da kuke ji, kuma ina neman gafarar Allah ga kaina da sauran musulmi daga duk zunbai. Ku nemi gafararsa. Lallai shi mai gafara nema mai yawan rahama.

Godiya ta tabbata ga Allah, yabo daddaxa mai albarka kamar yadda Ubangijinmu yake so kuma Ya yarda. Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kaxai, ba shi da abokin tarayya. Yabo da kirari nasa ne a duniya da lahira. Kuma ina shaidawa cewa Muhammadu bawansa ne kuma Manzonsa ne, ya aiko shi da rahama da shiriya, Allah ya yi tsira da aminci a gare shi, da iyalinsa tsarkaka, da sahabbansa masu girma, da mabiyansu, da waxanda suka biyo bayansu da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.

Ya ku bayin Allah!

A cikin mutane akwai waxanda suke ambaton Allah, sai dai su ba su fahimtar ma’anar zikirin, sai zukatansu suka kasa sanin girman Allah da haqiqanin matsayinsa, alhali shi ambaton Allah zance ne da tsigar masu tsoron Allah ke tashi da shi, sannan fatar jikinsu da zukatansu su tausasa zuwa ga ambaton Allah. Sai dai mutane saboda abin da suka saba da shi, da abin da suka jahilta na ma’anarsa, suna nanata ambaton Allah abakinsu kamar yadda suke nanata kowace irin magana ta yau-da-gobe. In ba haka ba shin wani ya tava tunanin ma’anar (Allahu Akbar) wadda take ita ce jigon Takbiri, kuma ita ce farkon abin da aka xorawa Manzo (ﷺ), yayin da aka umarce shi da gargaxi, Allah ya ce,

( يَاأَيُّهَا الْمُدَّثِّرُ 1 قُمْ فَأَنْذ 2 وَرَبَّكَ فَكَبِّرْ 3 ) [المدثر: 1 - 3]

.

(Ya kai wannan na lulluve. Ka tashi ka yi gargaxi. Kuma ka girmama Ubangijinka).

Lallai ita kalma ce mai girma, tana raya matacciyar qasa. Sautinta yana da rugugi kamar rugugin kogi mai tumbatsa, ko ma ta fi haka. Lallai ita kalma ce da ya wajaba ta yi rugugi a kunnen duk wani varawo, don hannunsa ya raurawa, jikinsa ya girgiza. Hakanan ta yi rugugi a kunnen duk wani azzalumi xan ta’adda mai girman kai, don ya wa’azantu in yana cikin masu wa’zantuwa, ya san cewa akwai wani Ubangijin da ya fi shi qarfi, kuma wanda ya fi girma sama da dabararsa da izgilinsa da makircinsa. Shi ne wanda kamunsa ya kire kamun duk wani xan-adam da makircinsa da yaudararsa. Allah Shi ne mafi girma ga duk wani mai girma.

Ku ji tsoron Allah ya ku Musulmi, ku ambaci Allah da yawa, lallai za ku rabauta. Ka ji tsoron Allah ya kai musulmi gafallale, idan kai bayan jin wannan huxuba, ka ji cewa kana daga cikin wanda ya rasa zuciyarsa, saboda gafalarsa, to kada ka yanke qaunar dawo da ita da ambaton Allah, domin Allah Yakan haxa waxanda suka rabu bayan sun yi dukkan zaton cewa ba za su sake haxuwa ba.

Mai tambaya yana iya tambaya: Me ya sa ambaton Allah (S.W.T) tare da sauqinsa a kan harshe da qarancin wahalarsa, ya zamo mafi amfani da falala, a cikin jimillar ibadu tare da wahalhalu masu maimaituwa a cikinsu.

Amsa: Allah ya sanyawa ragowar ibadu gwargwado, ya sanya musu lokuta iyakantatu, amma shi zikiri bai sanya masa gwargwado ko lokaci ba, kuma ya yi umarni da a yawaita shi dmin gijon zikiri shi ne albaqiyatus salihat, saboda abin da ya tabbata daga Annabi (ﷺ) ya ce, “Ku riqi garkuwarku”. Muka ce, “Ya Manzon Allah, daga wani abokin gaba ne da ya zo? Ya ce, “A’a, garkuwarku daga wuta, ku ce, Hasbunallahu, walhamdulillahi, wala’ilaha illallah, wallahu akbar, domin su za su zo ranar alqiyama suna masu kuvutarwa, kuma ababen gabatarwa, kuma su ne wanzazzun ayyukan alheri (Albaqiyat Assaliha)”. Hakim ya rawaito shi, kuma ya inganta shi.

Sannan kowane musulmi na gari ya sani cewa, mai tasiri mai amfani shi ne, zikiri a kan harshe tare da halartowar zuciya, domin harshe shi ne mai bayanin abin da ke cikin zuciya, ita kuwa zuciya ita ce taskar da ake aje sirruka a cikinta. Sha’anin qirji kuwa shi ne ya yalwata da ambaton abin da ke cikinsa, kuma jefa shi a kan harshe yakan yi daxi, kuma ba zai tsaya da ambatonsa a zuciya kwawai ba har sai harshensa ya amayar da shi, yana mai aiki da faxar Allah ta’ala, inda yake cewa,

( وَاذْكُرْ رَبَّكَ فِي نَفْسِكَ تَضَرُّعًا وَخِيفَةً وَدُونَ الْجَهْرِ مِنَ الْقَوْلِ بِالْغُدُوِّ وَالْآَصَالِ وَلَا تَكُنْ مِنَ الْغَافِلِينَ 205 ) [الأعراف: 205]

(Kuma ka ambaci Ubangijinka a cikin zuciyarka kana mai qasqantar da kai da tsoro, ba tare da xaga murya ba, safe da marece. Kuma kada ka zama daga cikin gafallalu).

Amma yin zikiri da harshe, alhali zuciya tana wasa, amfaninsa kaxan ne, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Ku sani cewa, Allah ba ya amsa addu’a daga zuciya mai wasa.” Hakim da Tirmizi ne suka rawaito shi, kuma Tirmizi ya kyautata shi.

Hakanan halartowar zuciya a wani lokacin yayin zikiri, tare da gafalarta a mafi yawan lokaci, shi ma amfaninsa kaxan ne, domin zuciya za ta yi ta waiwaye ne zuwa da sha'awa-saha'awan duniya, kuma abu ne sananne cewa mai waiwaye ba ya isa da wuri ba. Don haka halartar zuciya a kowane lokaci ko mafi yawan lokaci shi ne abin gabatarwa a kan dukkan ibadu, kai! Da shi ne ma ragowar ibadu kan yi daraja. Kuma shi ne moriyar ibadu na aikace.

Saboda haka ne ma Annabi (ﷺ) ya yi gargaxi a game da fashewar majalisai ba tare da an ambaci Allah a cikinsu ba. Ya ce; “Babu wasu mutane da za su tashi daga wani majalisin da ba su ambaci Allah a cikinsa ba, face sun tashi kamar daga kan mushen jaki ne, kuma wannan majalisin zai zame musu asara a gare su.” Abu Dawud da Hakim ne suka rawaito shi.

To don haka ka ga Manzon Allah (ﷺ) yana nuna qinsa ga majalisin gafalallu, kuma yana yin hani a bisa duk wani taro da ya wofinta daga ambaton Allah, kuma duk wani majalisin da ake manta ambaton Allah a cikinsa. Sannan kuma majalisin ya tarwatse bayan hayaniya mai tsawo, a kan neman abinci da sha'awar rayuwa, cikin kacaniya da hayaniya, da zunxe da yafice. Irin waxannan majalisai masu wari ne. Don haka mai tsira da amincin Allah ya ce, “Duk wanda ya zauna a wani mazauni da hayaniya ta yawaita a cikinsa, sai ya ce kafin ya tashi! Tsarki ya tabbata a gare Ka ya Ubangijinmu, da yabonka, na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai kai, ina neman gafararka, ina tuba zuwa gare ka. Sai Allah Ya kankare masa abin da ya kasance a wannan majalisin nasa.” Tirmizi da Ibn Majah ne suka rawaito shi.

Ina neman tsarin Allah daga shaixan tsinanne:

( يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا لَا تُلْهِكُمْ أَمْوَالُكُمْ وَلَا أَوْلَادُكُمْ عَنْ ذِكْرِ اللَّهِ وَمَنْ يَفْعَلْ ذَلِكَ فَأُولَئِكَ هُمُ الْخَاسِرُونَ 9 ) [المنافقون: 9]

“Ya ku waxanda suka yi imani kada dukiyoyinku da ‘ya’yanku su shagaltar da ku daga ambation Allah, duk wanda ya aikata haka to waxannan su ne asararru).

Ku yi salati! Allah Ya yi muku rahama! A bisa mafificin halitta mafi alherin ‘yan adam.





Tags:




Mishary Rashid Al-afasy