Falalar goman farko na zul-hijja


6776
Surantawa
Mafi albarkan lokaci shine goman farko na watan zulhijja saboda matsayi da suke dashi mai girma a wajen Allah madaukakin sarki,wanda hakan ke nuna soyuwar su a wajen sa, da basu fifiko da yaye.wadannan ranaku masu matukar albarka ne, masu yawan lada ne, masu karancin lefuka ne, masu matsayi ne me girma, masu nauoi daban-daban ne ne lada, Allah yayi rantsuwa dasu, kuma baya rantsuwa saida abu mai girma, sannan ya sanya su mafifitan ranakun duniya gaba-daya.

Manufofin huxubar

Bayanin cewa Allah yana halittar abin da ya so kuma yana zava

Tunatar da mutane da lokuta na alheri, da cin moriyarsu cikin aiyuka na kwarai

Bayanin falalar waxannan kwanaki goma

Bayanin yalwar rahamar Allah, da falalarsa a kan bayinsa

Huxuba Ta Farko

Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma mua neman tsarinsa daga sharrin kawukanmu da munanan aiyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar dashi, wanda kuma ya atar babu mai shiryar da shi, kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai allah, shi kaxai ne bashi da abokin taraiya, kuma ina shaidawa cewa Annabi Muhammad bawansane manzonsane, (Yaku waxanda kuka bada gaskiya kuji tsoron Allah yadda ya cancanta aji tsoronsa, kada ku mutu face kuna Musulmi). (Yaku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicce ku daga rai guda xaya kuma ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga gare su (su biyu) kuji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya dashi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Ya ku waxanda suka yi imani kuji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku aiyukanku, kuma ya gafarta muku zunubanku. Wanda ya bi Allah da manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawun shiriya shiriyar Annabi Muhammadu (ﷺ) kuma mafi sharrin al’amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wata bidi’a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta.

Bayan haka: Ya ku musulmi, ku ji tsoron Allah wanda yake halittar abin da ya so kuma yake zavi, ya halicci sammai kuma ya zavi ta bakwai daga ciki. Ya halicci aljannatai ya zavi firdausi daga cikinsu. Ya halicci mala’iku kuma ya zavi mala’ika Jibrilu da Mika’ilu da Israfilu daga cikinsu. Ya halicci mutane ya zavi muminai daga cikinsu. Ya zavi Annabawa aga cikin muminai. Ya zavi Manzanni daga cikin Annabawa. Ya zabi Ulul azmi daga cikin Manzanni. Ya zavi badaxai biyu daga cikin ulul azmi. Ya zavi Annabi Muhammadu (ﷺ) daga cikin bada xai guda biyu. Ya halicci garuruwa, ya zavi Makka daga cikinsu. Ya halicci kwanaki ya zavi watan Ramadan daga cikin watanninsu. Daga kwanakinsu kuma ya zavi yinin juma’a. Daga sa'o'insu kuma ya zavi wata wata sa'a a ranar juma’a. Daga gomin kwanakinsu ya zavi goman farko na watan zul-Hijjah.

Yaku bayin Allah! Haqiqa kwanaki goma na zul Hijjah, suna da cikin kwanaki masu matuqar albarka, saboda suna da matsayi mai girma a wajan Allah ta’ala da suke nuna qaunarsa gare su, da girmamawarsa gare su. Su goma ne masu albarka, masu qarancin munanan ayyuka, masu maxaukakan darajoji, masu mabanbantan ayyukan biyayya.

Waxannan kwanaki goma suna falala mai yawa, kaxan daga ciki, su ne:

Allah ta’ala ya rantse da su sai ya ce,

( وَلَيَالٍ عَشْرٍ 2 ) [الفجر: 2]

(Kuma ina rantsuwa da darare goma).

kuma Allah ta’ala ba ya rantsuwa sai da abu mai girma.

Sannan kuma Allah ta’ala ya gwamata da mafificin lokuta. Allah ya haxa su da alfijir, da adadi cika, da mara, da dare wajen rantsuwa.

A cikinsu Allah ta’ala ya cika addini, da cikar wannan addini ne Musulmi sukan samu kamala suma, kuma ladansu ya cika, su rayu cikakiyar rayuwa wadda za su samu kariya acikinta daga munanan aiyuka, kuma su ji daxin ayyukan biyayya. Da kuma cikar addini ne sunna ke yin nasara, a rinjayi bidi’a. Imani ya yi qarfi, munafunci ya mutu. Da cikar addini ne mutum ke cin nasara a kan zuciyarsa mai yawan umarni da mummunan aiki, don ta zama rai mai nutsuwa, tana bautawa Allah kamar yadda ya yi umarni, tana ko yi da Annabawa, tana abokantakar mutane na-gari, tana xabi’antuwa da kyawawan halaye. Da cikar addini ne mutum kanci nasara a kan shixaninsa wanda yake kautar da shi daga tafarki madaidaici. Ya ci nasara a kan san zuciya da sha’awoyi. Haqiqa addini ya cika. Kuma Manzo (ﷺ) ya bar mu a kan farin tafarki, daransa kamar ranarsa ne, babu mai karkacewa daga kansa sai halakakke tavavve. Haqiqa yahudawa sun mana hassada a bisa wannan kamala. Wani malami daga malaman yahudawa ya cewa Umar (R.A), wata aya xaya a cikin littafinku, da mu a ka saukarwa ita, da mun riqi ranar a matsayin idi: Ayar tana cewa, (A yau na cika muku addiniku, kuma na cika mukku ni’imata, kuma na yardar muku musulunci a matsayin addini), Umar ya ce: "Ni na san yaushe ta sauka, da inda ta sauka, ta sauka ranar arfa, ranar juma". Bukhari ne ya ruwaito shi. Cikar addini na nuna cikar al’umma da kasancewarta mafificyar al’umma.

Kuma yana daga fallarsu cewa, Allah ya cika ni’imarsa. Kuma yana daga falalarsu cewa, Zukata za su sami ni'ima kala-kala, ta hanyar ayyuka na qwarai, na magana da na aikin gavvai. Kuma yana daga cikar ni’imar cewa, Allah ya buxe zukatan bayi ga musulunci, mutane suka riqa shiga addinin Allah jama’u-jama’u, sai ga shi sun haura dubu xari. Kuma yana daga cikar ni’imar cewa, Allah ya rinjayar da musulunci a kan sauran addinai, a lokacin da ake da dangogin addinai a tsibirin larabawa, daga ciki akwai yahudanci da nasaranci, da bautar wuta, da bautar gumaka da munafinci, sai duk musulunci ya rinjayesu, Allah ta’ala ya ce:

( هُوَ الَّذِي أَرْسَلَ رَسُولَهُ بِالْهُدَى وَدِينِ الْحَقِّ لِيُظْهِرَهُ عَلَى الدِّينِ كُلِّهِ وَكَفَى بِاللَّهِ شَهِيدًا 28 ) [الفتح: 28]

(Shi ne wanda ya aiko manzonsa da shiriya da addinin gaskiya, don ya rinjayar da shi a kan dukkanin addinai, kuma Allah ya isa mai shaida).

Kuma yana daga cikar ni’ima, hana kafirai shiga harami, da kevantar musulmai daga haka. Sai kan musulmai ya haxu har suka zama kamar jiki xaya, suka xayanta abin bautarsu, kalmarsu ta haxu, hanyarsu ta haxu. Lallai wannan ni’ima ce mai girma ka ga cewa ma’abota imani sun yi rinjaye, ma’abota kafirci sun tarwatse.

Kuma yana daga cikin falalar waxannan kwanaki, cewa, ibadu kan tattaru a cikinsu, a cikinsu akwai salloli kamar yadda suke a wasunsu, a cikinsu akwai zakka ga wanda shekara ta kewayo masa, a ciki akwai azumi ga wanda ya yi nufin nafila, ko bai samu hadaya ba. A cikinsu akwai hajji zuwa xaki mai alfarma, wanda ba ya kasancewa a wasunsu, akwai zikiri, da talbiya da addu’ar dake nuna tauhidi. Tattaruwa ibadu a cikinsu xaukaka ce da ba ta da makamanci a wasu kwanakin.

Yana daga falalolinsu cewa, su ne mafifincin yininnika na duniya duka. Su ne mafi soyuwar kwanki zuwa Allah ta’ala. Kuma Allah ya fi son ayyukan kirki a cikinsu. Lokac ne na riba, kuma tafarkin tsira, kuma fagen gasa na aikin lherai. An karvo daga Ibn Abbas (R.A) ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, (babu wasu kwanaki da aikin alheri ya fi soyuwa zuwa ga Allah a cikinsu kamar waxannan kwanaki). Sahabbai suka ce, ya Manzon Allah ko da jihadi a tafarkin Allah? Ya ce, (Koda jihadi a tafarkin Allah, sai mutumin da ya fita da ransa da dukiyarsa sannan bai dawo da ko xaya ba) Bukhari ne ya ruwaito shi. Wannan yana nuna cewa aiki a cikin kwanaki goma shi ya fi jihadi da rai kawai, ko da dukiya kaxai, kuma ya fi yin jihadi da su, a dawo da su, ko xaya daga cikin su. Domi ba abin da ya fi aiki a cikin waxannan kwanaki sai wanda ya fita da ransa da dukiyarsa amma bai dawo da ko xaya ba.

Sannan Ranar Arfa a cikinsu take, wato ranar tara ga Zul-Hijjah. Ranar Arfa yini ne da aka san shi da falala da yawan lada, da gafarta zunubai. Shi yini ne mai girma, ana sanin ma’abotansa da tauhidi, dominsu suna faxan: La’ilaha Illallahu, ga shi Manzon Allah (ﷺ) ya ce, (kuma mafificin abin da na faxa ni da Annabawa gabanina: La’ilaha illallahu). Malik da Tirmizi ne suka ruwaito shi. Kuma Tirmizi ya inganta shi. Kuma mutum yana sanin raunin kansa yayin da yake yawaita addu’a, yake naci ga Allah wajen addu’a, ya zo a cikin hadisi: (Mafificiyar addu’a ita ce addu’ar ranar Arfa), kuma yana sanin ‘yan uwansa musulmi wanda suka taru daga ko ina a fili xaya, yana sanin maqiyinsa wanda ba’a tava ganin shi cikin wulaqanci da qasqanci ba kamar a ranar Arfa. Mutum yana sanin yawan gafarar Allah a wannan rana saboda yawancin hanyoyin gafara na kaxaita Allah da kiransa, da kiyaye gavvansa da azuminsa idan ba mai aikin hajji ba ne. Kuma shi ne ranar hajji babba, Annabi (ﷺ) (Hajji ita ce tsayuwar Arfa). Abu Dawud da Nasa'i da Tirmizi da Ibn Majah ne suka ruwaito shi, daga Abdurrahman xan Ya’amur Addili (R.A). A zumtar wannan yini na nafila kan kankare zunuban shekara biyu: wadda ta wuce, da mai zuwa. Ban kuwasan wata rana mai wannan falalar ba.

Yana daga falalarsu cewa, ranar laiya a cikinsu take, wato ranar goma ga Zul Hijja, wadda ita ce goma ga zul hijja, kuma mafificin ranaku kamar yadda yazo a hadisi, (mafificin kwanaki ranar laiya). Mafi girman aiyukan hajji irin su jifa, da aski kai, da yanka hadaya, da xawafi, da sa’ayi, da sallar idi, da yanka laiya, da haxuwar musulmi a sallar idi, da yiwa junansu barka, duka a cikin waxannan kwanaki goma suke.

Bayin Allah, haqiqa falalar kwanaki goma suna da yawa, bai kamata Musulmi ya tozartar da su ba. Ya wajaba ya ci moriyarsu, ya yi gasa na aikin alheran da ke cikinsu, ya tafiyar da su cikin aiki nagari. Ina faxan abin da kuke ji, kuma ina neman gafar allah ga kaina da ku daga kowane zunubi, ku nemi gafarsa, lallai shi mai gafara ne mai jinqai.

Huxuba Ta Biyu

Yabo ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da aminci su tabbata ga cikamakin Annabawa, da alyensa da sahabbansa da waxanda suka tafi a kan tafarkinsa har ya zuwa ranar sakamako. Bayan haka:

Ya ku bayin Allah, yana daga ayyukan da aka shar’anta cikin waxannan kwnaki zikiri. Allah ta’ala yana cewa:

( لِيَشْهَدُوا مَنَافِعَ لَهُمْ وَيَذْكُرُوا اسْمَ اللَّهِ فِي أَيَّامٍ مَعْلُومَاتٍ عَلَى مَا رَزَقَهُمْ مِنْ بَهِيمَةِ الْأَنْعَامِ ) [الحج: 28]

(Domin su halarci amfanuunka gare su, kuma su ambaci sunan Allah cikin sanannun kwanaki, saboda abin da ya azurtasu da shi na daga dabbobin ni’ima).

Kuma Imamu Ahmad ya rawaito daga ibn Umar cewa, Annabi (ﷺ) ya ce, (babu wasu kwanaki mafiya girma, da kuma aikin da ya fi soyuwa zuwa ga Allah a cikinsu kamar waxannan kwanaki guda goma, don haka ku yawaita hailala da kabbara da hamdala a cikinsu).

Abu Huraira da Ibn Umar sun kasance idan goma ga Zulhijjah suka shigo suna fita kasuwa, suna kabbara, kowa shi kaxai, yayin da mutane suka ji su sai su tuna kabbara, sai kowa shi kaxai ya yi kabbara. Wannan kabbara ce zalla, kuma ana so mutum ya yawaita tasbihi da hailala da hamdala da zikiri tare da kabbara. Ya yawaita karanta Alqur’ani domin shi ne mafificin zikiri, kuma acikinsa shiriya da rahama da albarka mai girma da tasiri, da warraka suke. Kuma musulmi ya san cewa zikiri shi ne mafi soyuwar zance zuwa Allah ta’ala, kuma shi ne dalilin tsira a duniya da lahira kuma dalilin rabauta, kuma mai kiyaye ma’abocinsa daga kafrici da shaixan da wuta. Da shi ake ambaton bawa a wajan Ubangijinsa, kuma Allah da Mala’ikunsa suna yin sallati ga mai zikiri kuma shi ne mafi qarfin makami. Shi ne mafificin ayyuka, mafi tsarkakarsu, mafi xaukakarsu a daraja, mafifici a kan ciyarwa, da shi ne Allah yake nununka lada, ya yafe laifi, ya nauyaya ma’auni.

Kuma ya gwama shi da sallar juma’a, Allah ya ce,

( فَإِذَا قُضِيَتِ الصَّلَاةُ فَانْتَشِرُوا فِي الْأَرْضِ وَابْتَغُوا مِنْ فَضْلِ اللَّهِ وَاذْكُرُوا اللَّهَ كَثِيرًا لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ 10 ) [الجمعة: 10]

(To idan an gama sallah, to ku watsu cikin qasa, kuma ku nemi falalar Allah, kuma ku ambaci Allah diyawa).

Kuma ya gwama shi da azumi Allah ya ce,

( وَلِتُكْمِلُوا الْعِدَّةَ وَلِتُكَبِّرُوا اللَّهَ عَلَى مَا هَدَاكُمْ وَلَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ 185 ) [البقرة: 185]

(Kuma ku cika adadin azumi, kuma ku girmama Allah saboda shiryar da ku da suka yi).

Kuma aya ta gwama shi da hajji sai ya ce,

( فَإِذَا قَضَيْتُمْ مَنَاسِكَكُمْ فَاذْكُرُوا اللَّهَ كَذِكْرِكُمْ آَبَاءَكُمْ أَوْ أَشَدَّ ذِكْرًا ) [البقرة: 200]

(Kuma idan kun idar da ayyukan hajjinku ku ambaci Allah kamar yadda kuke ambaton iyayanku, ko fiye da haka).

Kuma yana daga mafifitan ayyukan a waxannan kwanaki - ya bayin Allah - yin talbiyya da hajji da neman kusanci zuwa Allah da azumin Arfa ga wanda bai ya aikin hajji, an karvo daga Abi qatadata (R.A) ya ce, an tambayi Annabi (ﷺ) game da azumin ranar Arfa, ya ce, "Yana kankare shekarar da ta wuce da shekara mai zuwa". Muslim ne ya rawaito.

Ya ku bayin Allah! Ana so Musulmi ya yawaita azumi akwanaki gomxa, da zai azumci kwana tara, to babu ya laifi a shari'a, domin azumi yana daga aiki na gari. Abin da ya zo daga Nana Aisha cewa, ba ta tava ganin Manzon Allah (ﷺ) ya yi azumin kwanaki goma na zulhijja ba, to ita ta na ba labarin abin da ta sani ne, domin kwananta a cikin kwanaki tara xaya ne tak. Da yawa kuma yakan bar abu don tsoron kada a wajabtawa al’ummarsa, yakan bar shi don uzurin rashin lafiya ko tafiya ko jihadi ko makamantansu.

Ya wajaba ga musulmi, idan goman zulhijja ta shigo yana da nufin laiya kada ya ciri wani abu daga gashinsa, ko fatarsa, ko farcansa. Haka ya zo daga Manzon Allah. Amma waxanda za a yi musu layya ne, to babu laifi su, su ciri wani abu daga waxancan abubuwa, domin Annabi ya yi hani ne ga wanda zai yi laiya, su kuwa mutanen gida za a yi musu laiya ne, basu suke yi ba. Don haka ba mu san cewa Annabi yana hana iyalinsa su ciri wani abu daga haka ba, tare da cewa yana yin laiya a madadinsu. Saboda Allah ya yana yin layya kashi biyu ne; xaya ga kansa, da iyalansa, xaya ga al’ummarsa gaba xaya, Allah ya saka masa da alheri a madadinmu, ya san ya mu daga mabiyansa, sarari da voye, ya tashe mu cikin tawagarsa, ya shayar da mu daga tafkinsa, ya haxa mu da shi a aljanna, lallai shi mai karamci ne mai kyauta ne.

Ku yawaita salati da sallama ga Annabin ku Muhammadu, ku yawaita yi masa salati a kowane lokaci, domin haqqinsa a kanku yana girma sosai. Ku yawaita salati a gare shi domin shi ya umarce ku da haka; ku yawaita salati a gare shi domin ku sami lada mai girma dayin haka; domin duk wanda ya yi salati sau xaya a gare shi, Allah zai masa salati goma.

Ya kamata musulmi ya yi rigegeniya da kowane aiki na qwarai a waxannan kwanaki goma, ya yawaita addu’a da istigfari, ya nemi kusanci zuwa ga Allah da duk wani aiki mai kusantarwa ga falalar Allah, ku ribace su, kada ku yi nawa ko kasala. Mu sani cewa, Allah ta’ala yana da kyaututtuka a cikin kwanakinsa, to mu ribaci dama, mu yawaita kyawawan aiyuka, ko Allah ya yi mana afuwa game da kura-kuranmu da munanan aiyukanmu.

Allah ka shiryar da mu zuwa ga mafi shiryuwar zantuttuka da aiyuka, babu mai shiryarwa gare su sai kai. Allah ka nesanta mu daga munanan maganganu da ayyuka da soye-soyen zukata da cututtuka, babu mai nesanta mu daga munanansu sai kai, Allah ka shiryar da mu ka daidaita mu.

Allah ya yi min albarka da ku, da Alqur’ani mai girma, kuma ya amfane ni, da ku da abin da ke cikinsa na daga ayoyi da wa'azi mai hikima, ya amfane mu da shiriyar Shugabannin Manzanni, da miqaqqiyar maganarsa.





Tags:




Taqaitaccen Bayani A Kan Aikin Hajji