Goman qarshe na ramadan


6438
Surantawa
Watan Ramadan wata ne mai girma, wata ne da ake bude kifofin aljanna a cikin sa, hakanan ake kulle kofofin wuta. Haqiqa Allah ya kebanci wannan wata da doriyar falala kasantuwar sanya dare daya da yayi a cikin shi ya zama mafi alheri akan watanni dubu, wato lailatul qadari, wanda yake dare ne cikin dararen goman qarshe. Don haka ne ma manzon Allah s.a.w yake dagewa da ibada cikin wannan ranaku irin dagewan da baya irin sa a wasun su don yayi gamdakatar da wannan dare. Saboda haka ya zama wajibi ga dukkan musulmi ya kara kwadayi kwarai da gaske wajen ribatar wadannan darare masu albarka,musamman yayi itikafi cikin su,don yana cikin mafifitan ayyuka a cikin wadannan darare.

Manufofin huxubar

Tunatar da mutane falalar wannana goman qarshen.

Bayanin ayyukan sunnah da ake so a aikata a wannan goman.

Qarfafa alaqar bawa da Ubangijinsa da qoqari wajen neman kusanci gare shi

Huxuba Ta Farko

Yabo da godiya da kirari sun tabbatar da Allah, taimakonsa da gafararasa muke nema, muna neman tsarinsa daga sharrin kawunanamu da munannan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar to babu mai vatar da shi, wanda kuma ya vatara to babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kaxai ne ba Shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa Annabi Muhammadu bawaqn sa ne manzon sa ne (ya ku waxabda suka yi imani kuji tsoron Allah yadda ya cancanci a ji tsoronsa, kada ku mutu face kuna musulmai) (ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanad ya halicce ku daga rai guda xaya, kuma ya halicci matarsa daga gare su (Su biyu). Ku ji tsoron Allah wanda kuke yiwa junaku magiya da shi, (kuma ku kiyaye) zumunci, lalle allah mai akula ne da ku). (ya ku waxanda suka yi imani ku tsi tsoron Allah kuma ku faxi Magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku ayyukanku, kuma ya gafatar muku zunubanku. Wanda yabi da manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawun shiriya shiriyar Annami Muhammad (ﷺ) kumamafi sharin al’amura (a addini) qagaggunsu. Kuma duk wani qagaggen abu (a addini) bidi’a ce, kuma duk warta bidi’a vata ce, kuma duk wani bata yana wuta.

Bayan haka, ya ku mutane ina muku wasiyya da ni kaina da tsoron Allah mai buwaya da xaukaka, domin tsoron Allah, shi ne mafi girman abin da kuka voye, kuma mafi kyawun abin da kuka baiyana, kuma mafificin abin da kuka taskance. Allah ya taimake mu a bisa lazimtartasa, kuma ya wajabta mana ladanta.

Ya ku musulmi, waxannan su ne kwanankin watanku na Ramadan ga su suna raguwa, ga dararensa masu daraja suna qarewa, suna raguwa suna qarewa, alhalin yi musu shaida a bisa ayyukanku, masu kiyayewa ga abin da kuka ba su ajiya, kuma sito-sito ne ababen kiyayewa, za a kirawo ku ranar alqiyama (Ranar da kowace rai za ta sami abin da ta aikata). Ubangijiku zai yi kira, (Ya ku bayina kaxai waxannan ayyukanku ne nake qididdige su a gare ku, sannan na biya ku a kansu. Duk wanda ya sami alheri to ya gode wa Allah, wanda kuwa ya sami savanin haka to kada ya zargi kowa sai kansa).

Wannan shi ne watanku, kuma ga qarshensu ya zo, Mutane diyawa sun fara zumi, amma sun rasu kafin gama shi. Wasu kuma sun fatan ganin na gaba. Amma Allah bai nuna musu ba. Shin kuna lura kuwa da ajali da wucewarsa?! Kuma shin kuna kula da yadda guri yake yaudara masu shi?!

Ya ku ‘yan uwa! In dai akwai mai tsawatarwa cikin rayuka, kuma da mai wa’azi cikin zukata, to ‘yan kwanaki sun rage daga kwanankinsa, kuma ragowa masu tarin girma, su ne kwanakin goma raguwar da Annabinku Muhammadu (ﷺ) yake kulawa da su dukkanin kulawa, a cikin ashirin da suke sallah da barci amma yayin da goman (qarshe) suka shiga sai ya himmatu, ya qoqarta ya xaura xamara, ya qauracewa shimfixarsa, ya tashi iyalinsa yana qwanqwasa qofar Faxima da Ali Allah ya qara yarda a gare su yana mai cewa “Yanzu ba kwa tashi ku yi sallah ba?” Yana kwankwansa qofar yana mai karanta faxar Allah:

( وَأْمُرْ أَهْلَكَ بِالصَّلَاةِ وَاصْطَبِرْ عَلَيْهَا لَا نَسْأَلُكَ رِزْقًا نَحْنُ نَرْزُقُكَ وَالْعَاقِبَةُ لِلتَّقْوَى 132 ) [طه: 132]

(Kuma ka umarci iyalinka da sallah, kuma ka yi haquri a kanta, ba ma tambaye ka arziqi ba, mu ne masu azurtaku. Kuma kyakkyawan qarshe ya tabbata ga masu tsoron Allah).

Kuma yana zuwa xaukuna na matanyensa yana umarni da cewa, “Ku tashi ma’abota xakuna, da yawa rai mai sutura a duniya amma matsaraiciya ranar alqiyawa”. Bukhari ya ruwaito shi.

Annabi kasance idan kwanan goma ya rage daga Ramadan, ba ya barin wani da yake da ikon tashi daga iyalinsa face ya tashe shi.

Yana daga sunnonin waxanda kwanaki, qoqari wajen tashi da daddare da abin da ke cikin haka na cikasa abin da ya kuvucewa mutum na cikon farilla.

Game da qiyamullalli wani na iya cewa “Wannan tsayuwar daren nafilace. Ni in na kiyaye farillai ya ishe ni. Amsar da za a ba shi ita ce, haqiqa a cikin kiyaye farillai akwai alheri mai yawa, kuma shi kaxai za a tambayi musulmi, amma wa ya sanar da kai cewa ka ba da farillan yadda ya kamata?!. Haqiqa kai kana buqatar nafilfili don cike tawayar da ke cikin farillan. Kuma game da ranar alqiyama. Adu Dawud da waninsa sun rawaito cewa, “Allah Ta’ala zai ce “Duba sallar bawana, shin ya cikata ko ya tauyeta? To idan ta kasance cikakkiya ce sai a rubuta ma sa ita cikakkiya, idan kuma wani abu ya tawaya daga cikinta sai ya ce: “Ku duba bawana shin yana da nafilla?” Idan ya kasance yana da ita, sai ya ce: “Ku cikawa bawana farillarsa”. Sannan a a qarvi ayyuka a wannan yanayi.

Allah (S.W.T) ya wajabta farilla, kuma ya san cewa daga cikin bayins akwai waxanda za su taqaita wajen cikata, sai ya shar’anta musu nafiloli don ya xora wannan karaya, don jinqan da ya ke musu. Mu xauka ma ka cika farillai, ka ba su haqqinsu, to ai an umarce ka da koyi da Annabinka (ﷺ). Allah Ta’ala Ya ce,

( لَقَدْ كَانَ لَكُمْ فِي رَسُولِ اللَّهِ أُسْوَةٌ حَسَنَةٌ لِمَنْ كَانَ يَرْجُو اللَّهَ وَالْيَوْمَ الْآَخِرَ وَذَكَرَ اللَّهَ كَثِيرًا 21 ) [الأحزاب: 21]

(Lallai abin koyi kyakkyawa ya tabbata gare ku, game da Manzon Allah, ga wanda ya kasance yana qaunar (samun yardar) Allah, da ranar lahira).

Ya ku bayin Allah! Kuma yana daga falalolin wannan goman cewa, ana fatan dacewa da daren lailatul kadari a cikinta, daren da Allah Ta’ala Ya ce game da shi:

( لَيْلَةُ الْقَدْرِ خَيْرٌ مِنْ أَلْفِ شَهْرٍ ) [القدر: 3]

.

(Daren lailatul qadari ya fi wata dubu alheri).

Malam Annakha’i yana cewa, “Aiki a cikinsa ya fi wata dubu alheri, banda shi daern” Wata dubu kuwa - ya ku bayin Allah - shekara tamanin da uku da wata huxu ne. Don haka aiki a wannan dare ga wanda Allah ya datar da shi ya fi aikin cikin shekara Tamanin da uku da wata huxu. Hadisi ya zo a cikin Bukhari da Muslim, daga Abu Huraira (R.A) Annabi (ﷺ) ya ce, “Duk wanda ya sallaci daren lailatul qadari yana mai ba da gaskiya da neman lada, to za a gafartamasa abin da ya gabata na zunubansa”. Fadinsa “yana mai ba da gaskiya” yana nufin “yana mai ba da gaskiya da abin da Allah ya yi alqawari game da shin a ladan masu qiyamullaili a cikinsa, da neman lada, da bixar sakamako”. Wannan dare xaya ne daga dararen goman qarshe na Ramadan a bisa zance mafi rinjaye. Haqiqa Allah (S.W.T) ya voye wa bayi saninsa don jin qai a gare su; domin su yi qwazo wajen nemansa, a cikin waxannan darare masu girma, ta hanyar sallah da zikiri da addu’a, sai su qara kusanci ga Allah. Kuma ya voye wannan dare ga bayi, don gane wanda yake mai qoqari wajen nemanta, mai qwaxayi a kanta, da wanda yake mai kasala ko mai sakaci. Duk kuwa wanda ya yi qoqari a bisa wani abu to zai same shi.

Ya ku bayin Allah! Lailatul qadari tana da alamomi da ake gane ta da su, sai dai mafi ingancin abin da ya zo dangane da alamointa su ne, rana za ta fito a safiyar wannan rana mai haske sosai, babu dallarin haske a gare ta, domin ya zo cikin sahihu Muslim daga Ubayyi bin Ka’ab (R.A) ya ce “Manzon Allah (ﷺ) ya ce “Kuma alamarta rana za ta fito a safiyar yininta fara babu dallarin haske gare ta.”

Wannan alama tana kasancewa bayan wucewar daren. Hikimar hakan, don mutane su yi qoqari wajen nemanta, kuma masu qoqari su yi farin ciki da qwazonsu da aikinsu. Kuma haqiqa sunna ta nuna cewa daren Lailatul Qadari a kan iya sanin sa ta hanyar mafarki na gari. Domin ya zo a cikin Bukhari da Muslim daga Ibn Umar cewa wasu mazaje daga Sahabban Annabi (ﷺ) an nuna musu daren Lailatul Qadari cewa, shi a cikin bakwan qarshe yake, sai mai tsira da amincin Allah ya ce “Ai ga mafarkinku ya haxu a cikin bakwai ta qarshe, to duk wanda zai lalube ta, to ya lalube ta a cikin bakwai na qarshe”.

Kai kacokan ma an nunawa Annabi (ﷺ) yaushe ne daren Lailatul Qadari, domin ya zo a cikin Bukhari daga Abi Sa’id Alkhudri, ya ce “Manzon Allah (ﷺ) ya ce, "Haqiqa ni, an nuna min daren Lailatul Qadari, sannan aka mantar da ni shi, don haka, ku neme shi a goman qarshe, kuma ni na gan ni ina sujjada cikin ruwa da tavo” Abu Sa’id ya ce” Sai na ga Annabi (ﷺ) yana sujjada a cikin ruwa da tavo, har sai da na ga a alamun tavo a goshinsa”.

Ya ku ‘yan’uwa masu girma! Haqiqa yana daga sunnonin waxannan kwanaki goma: Shiga I’itikafi, wanda shi ne zama cikin masallaci na tsawon wani lokaci na waxannan kwanaki masu albarka, don kevanta, domin bauta ga Allah mai buwaya da xaukaka, Allah Ta’ala Ya ce:

( وَأَنْتُمْ عَاكِفُونَ فِي الْمَسَاجِدِ ) [البقرة: 187].

(Kuma alhali ku kuna masu I’itikafi a cikin masallatai).

Kuma Bukhari ya ruwaito daga Abu Sa’id Alkhudri cewa, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Duk wanda zai yi I’itikafi tare da ni, to ya yi I’itikafi a goma na qarshe, domin ni. an nuna min wannan daren sannan aka mantar da ni shi”. Don haka ya kamata ga wanda ya sami ikon haka, sai ya yi saboda lada mai girma da horar da kai a kan bin Allah da ke cikin yin hakan.

Shi mai itikafi ya tsare kansa ne don biyyaya ga Allah da ambatonsa, ya yanke kansa daga duk wani abu mai shagalarwa da zai shagaltar da shi game da Allah. Ya duqufa da zuciyarsa da jikinsa da aikata abin da zai kusanta ga Allah. Babu abin da ya rage masa face Allah da abin da zai janyo masa yardarsa.

Ma’anar I’itikafi da haqiqaninsa, shi ne, yanke alaqoqi da halittu, don saduwa da hidimar mahalicci, kuma duik lokacin da sanin Allah ya qarfafa da sonsa, da matsawa gare shi sai su gadarwa da mai su yankewa zuwa ga Allah, a kowane lokaci.

Kuma yana da sunnonin goman qarshe na Ramadan: Qoqari wajen sauke Alqur’ani mai girma don koyi da Annabi (ﷺ), da yawaita sadaka, wadda ita ce sunnar mala’ika Jibrilu tare da Annabi (ﷺ) domin Jibrilu ya kasance yana bitar alqur’ani a kowace shekara a watan Ramadan tare da Manzon Allah (ﷺ), har yayin da shekrar qarshe ta raytuwarsa (ﷺ) ta zo sai Mala’ika Jibrilu ya yi bitar Alqur’ani tare da shi a cikinta sau biyu. Bukhari da Muslim ne suka rawaito daga Ibn Abbas (R.A).

Kuma Bukhari ya ruwaito hadisi daga Ibn Abbas (R.A) ya ce “Annabi (ﷺ) ya kasance mafi kyautar mutan. Kuma lokacin da ya fi kyauta shi ne a Ramadan lokacin da Mala’ika JIbrilu yake haxuwa da shi, yana bitar alqur’ani tare da shi. Lallai Manzon Allah ya fi sakakkiyar iska kyauta yayin da Jibrilu ya gamu da shi”.

Da dai waxanda suka imani da girman ladan sadakar da Annabi ya faxa, suna kwaxayin ba da sadakar su, da zakkar fidda kansu ga mabuqata da faqirai da sun kasance sun gabatar da alheri ga kawukansu, kuma sun nuna mihammancin koyarwar Manzo (ﷺ) Sun zama rayayyar al'umma, wacce take yin ilimi. Kuma tana aiki da iliminta, tana samun ribar ta fuskar gyaruwar halayenta da xabi'unta.

Huxuba Ta Biyu

Godiya ta tabbata ga Allah, Ubanjigin talikai. Tsira da amincin su tabbata a bisa mafi darajar manzanni, Annabinmu Muhammadu da alayensa da sahabbansa gaba xaya, bayan haka:

Ya ku bayin Allah! Haqiqa I’itikafi yana da falala mai girma, daga cikinta:

Akwai cewa a cikin waxannana dararen goma waxanda suka fi watanni dubu alheri. Annabi (ﷺ) ya kasance yana I’itikafi a goman farko, sannan ta tsakiya. Sannan wata rana ya leqo da kansa ya yi wa mutane magana, mutane suka matso, ya ce “Haqiqa ni na yi I’itikafin goman farko, ina neman wannan dare, sannan na yi I’itikafin goman tsakiya, sannan aka ce min, daren yana cikin goman qarshe, don haka wanda a cikinku yake so ya yi I’itikafi to ya yi”. Muslim ne ya rawaito shi.

Daga ciki falalar i'itikkafi, akwai cewa, Annabi (ﷺ) bai tava barin I’itikafi ba. Ya kasance yana I’itikafi a kwana goma kowace shekara. Yayin da shekarar da ya rasu ta zo, sai ya yi I’itikafin kwana ashirin. Yayin da matansa suka yi gasa a kan I’itikafi, sai ya bar shi, ya rama shi a goman farko na shawwal. Bukhari ne ya rawaito shi.

Daga ciki falalar, akwai cewa Annabi (ﷺ) ya kasance yana barin abin da yake halaliyarsa ne, wato bacci da mata. Da wannan ne aka fassara faxin A’isha (R.A) “Sai ya qara xaura xamara”. Ma’ana yana barin bacci shi da kusantar matarsa.

Daga ciki falalar, akwai cewa, Annabi (ﷺ) yana aikata abin da ya yi hani a kansa. Domin ya yi hani a bisa savi-zarcen azumi. Wato jinkirta sahur har zuwa lokacin sahur (ma’ana mutum ya qi cin komai bayan azumi har lokaci xaukar wani azumin). Amma ya kasance yana aikata haka musamman ma a cikin goman qarshe.

Kuma yana daga cikin falalar: cewa, matayen Annabi (ﷺ) sun yi I’itikafi bayansa, har Nana A’isha (R.A) tana cewa “Wata mata mai jinin Istihadha daga matayen Annabi (ﷺ) ta yi I’itikafi tare da shi, sai ta kasance tana ganin jaja-jaja da fatsi-fatsi, har wani sa’in muka kasance muna sanya tasa a qarqashinta yayin da take Sallah. Bukhari ne ya rawaito shi.

Ya ku Musulmi! Haqiqa Allah ya sanyawa I’itikafi wasu dokoki da hukunce-hukunce daga cikinsu;

Ya wajaba mai I’itikafi ya tabbatar da manufar yin I’itikafi ya ta hanyar bin shiriyarsa.

Idan mai I’itikafi ya yi niyyar I’itikafi, wajabi ne sai ya kai karshe, ya hallata ya katse shi, musamman idan ya ji tsoron yin riya da aikinsa.

Babu wani hadisi da ya zo cikin iyakance mafi qaranci lokacin yin I’itikafi.

Shuwagannin huxu, da jamhurum malamai na da, da na yanzu sun tafi a kan cewa, mai I’itikafi zai shiga I’itikafi ne kafin faxuwar rana a daren da yake son ya shiga I’itikafi a cikinsa.

An so ga mai I’itikafi ya riqi waje na musamman ga kansa, domin ya kevance da Ubangijinsa, kuwa ya huta a gurin, kuma don kada wani ya faxo masa, yayin da yake canja tufafi, ko tarbar wanda yake son ya ziyarce shi daga iyalinsa.

Ya halarta mai I’itikafi ya yi kai-kawo a masallaci. sai dai an fi so kada ya yawaita kai-kawon saboda dalilai guda biyu.

Cewa, Annabi (ﷺ) ya an yi masa wata lema a cikin masallaci, baya fitowa daga cikinta sai don sallah, kuma mafificiyar shiriya ita ce shiriyarsa.

Cewa, Annabi (ﷺ) ya ce “Mala’iku suna yi wa xayanku addu’a matuqar yana zaune a gurin da ya yi sallarsa. Bukhari ne ya rawaito shi.

Amma matsalar fita daga masallaci, ta ya kasu kashi uku:

Na farko: Wanda ya halatta, shi ne fita saboda lamari da ya zama babu makawa a shari’a ko a xabi’a, kamar fita don sallar juma’a, ko ci da sha, idan bai sami wanda zai zo masa da shi ba.

Na biyu: Fita domin aikin biyaiya wanda bai wajaba a gare shi ba, kamar duba mara lafiya, da halarta jana’iza, idan ya sharxanta shi tun farko to ya halarta. In ba haka ba bai halarta ba.

Na uku: Fita domin abin da ya savawa I’itikafi; wato kamar fita domin saye da sayarwa, da tarawa da iyalinsa, da makamancinsa, wannan bai halatarba.

Bayin Allah! Ya wanda ya yi nishaxi tun farkon wata har yayin da lamari ya girmama kaka ta yi sai ya bar tsaiwar dare, ya kasha dararensa cikin wasa da wargi da savon Allah, ya kaucewa taren kyaututtukan Ubangijinsa mai yawan kyauta. Ina gargaxinka ka bar kasala a kan abin da ka fara watanka da shi na tsaiwar dare da azumi.

Ya ma’abotan gafala, ku faxaka, ya ahlussunna ku farka, wallahi asara ce da rashin dace a ce an ba ka labarin wani dare da bauta a cikinsa ta fi bautar shekara tamanin da uku, sannan ba za ka tashi kana mai bauta ga Ubangijinka ba, kana mai sujjada.

Kashedinka daga ruxuwa da abin da ka aikata. Ka kasance kamar waxanda Allah ya bayyana halayensa da cewa,

( كَانُوا قَلِيلًا مِنَ اللَّيْلِ مَا يَهْجَعُونَ 17 وَبِالْأَسْحَارِ هُمْ يَسْتَغْفِرُونَ18 ) [الذاريات: 18]

(Sun kasance xan barci kaxan suke yi da daddare. Kuma suna neman gafara a lokacin sahur).

Ba su nemi gafara ba sai domin suna ji a jikinsu cewa, sun tauye wani abu na haqqin Allah, duk da tsayawarsu a mafi yawan dare. Ka zamo kamar wanda Allah mai buwaya da xaukaka, Ya ce a game da su,

( وَالَّذِينَ يُؤْتُونَ مَا آَتَوْا وَقُلُوبُهُمْ وَجِلَةٌ أَنَّهُمْ إِلَى رَبِّهِمْ رَاجِعُونَ 60 ) [المؤمنون: 60]

(Da kuma waxanda suke aikata abin da suke aikatawa (na xa’a ga Allah) alhali zukatansu suna masu jin tsoron cewa su masu komawa ne zuwa Ubangijin su).

Ka tuna cewa abin da kake cikinsa da falalar Allah da datarwarsa. Wanda ya ba ka, kuma ya datar da kai, shi ne ya haramtawa waninka, kuma ya hana shi. Don haka, ka faxi kamar yadda salihai suka ce,

( وَقَالُوا الْحَمْدُ لِلَّهِ الَّذِي هَدَانَا لِهَذَا وَمَا كُنَّا لِنَهْتَدِيَ لَوْلَا أَنْ هَدَانَا اللَّهُ ) [الأعراف: 43]

“Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya shiryar da mu ga wannan, kuma ba mu kasance za mu shiriya ba ba don Allah ya shiryar da mu ba”.

Ka lura da abin da Allah ya faxa ga bawansa kuma Annabinmu (ﷺ):

( وَلَئِنْ شِئْنَا لَنَذْهَبَنَّ بِالَّذِي أَوْحَيْنَا إِلَيْكَ ثُمَّ لَا تَجِدُ لَكَ بِهِ عَلَيْنَا وَكِيلًا 86 إِلَّا رَحْمَةً مِنْ رَبِّكَ إِنَّ فَضْلَهُ كَانَ عَلَيْكَ كَبِيرًا 87 ) [الإسراء: 87]

(Da dai mun so da mun tafi da abin da muka yi wahayi gare ka, sannan ba za ka sami wani mai yi maka wakilci a kanmu ba. Sai domin rahama daga Ubangijinka lallai falalarsa ta kasance mai girma a gare ka).

Har wasu daga magabata suka xauki wannan ayar a matsayin gargaxi mafi girma a littafin Allah. Kasance mai qasqan da kai, mai qoqari a cikin biyayya, mai tsoron kada a qi karvar aikinsa, domin babu mai amincewa makircin Allah sai mutane asararru. Kaxai Allah yana karva ne daga masu taqawa. Kuma kai ba ka sani ba ko kana cikinsu.

Sannan ku sani ya bayin Allah cewa, A’isha matar Annabi (ﷺ) ta tambaye shi idan na riski daren Lailatul Qadari me zance a cikinsa, sai ya ce ki ce, ”Ya Ubangiji haqiqa Kai mai afuwa ne, kana son afuwa, ka yi afuwa a gare ni.”

Ya Allah ka datar da mu a cikin waxannan kwanaki masu albarka, Allah kai ne mai afuwa ka yi mana afuwa, ka gafarta mana da waxanda suka gabace mu da imani, kada ka sanya qullata a cuciyarmu ga waxanda suka yi imani, ya Ubanginmu kai ne mai gafar mai tausayi.





Tags:




Ali Hajjaj Souissi