Hikimomi Da Sirrin Dake Cikin Aikin Hajji


4081
Surantawa
Shin akwai wanda ya taba ganin hajji da irin tumbatsar sa, da imani da irin hasken sa, da irin tarin jamaar da tazo domin girmama Allah da godiya gare shi? Haqiqa taron hajji taro ne me ban mamaki, musulmi suna masu farin-ciki da walkatuwa dashi, hakanan makadaita suna daukaka dashi. Don haka yaku musulmai menene manufofin hajji tattare daku?

Manufofin huxubar

Tunatar da mutane sirrikan Hajji da hikimominsa

Tunatar da su da ni’imar musulunci

Bayanin zamantowar addini tilas ne da muhimmancin ibada ga mutum xaya da al’umma

Bayanin cewa gyara ba ya yiwa sai da addinin gaskiya

Huxuba Ta Farko

Yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma muna neman tsarin sa daga sharrin kawukanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar da shi, wanda kuma ya vatar da shi babu mai shiryar da shi; kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kaxai ne ba shi da abokin taraiya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi Muhammadu bawansa ne Manzonsa ne (Ya ku waxanda suka yi imani ku ji tsoron Allah yadda ya cancanci a ji tsoronsa ne. Kada ku mutu face kuna musulmi). (Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicce ku daga rai guda xaya, kuma ya halicci matarsa daga gare shi, kum aya yaxa maza da mata daga garesu (su biyu). Ku ji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya da shi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Ya ku waxanda suka yi imani ku ji tsoron Allah kuma ku faximagana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku ayyukanku, kuma ya gafarta muku zunubanku. Wanda ya bi Allah da Manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawun shiriya shiriyar Annabi Muhammadu (ﷺ). kuma mafi sharrin al’amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wani qagaggen abu (a addini) bidi’a ne, duk wata bidi’a vata ce, duk wani vata yana wuata.

Bayan haka:

Ya ku mutane, shin kun ga aikin hajji da irin girmansa, shin kun ga imani da haskakawarsa, kun ga cincirindon jama’a yadda suka zo suna girmama Allah suna kambama shi suna yabonsa? Lallai kallon taron hajji abu ne mai ban mamaki, abin kallo ne mai ximauta hankali. Muminai suna farin ciki da shi, masu tauhidi sun xaukaka da shi. Masu laifi sun shaqe da shi. Gafalallu sun razana da shi. To menene manufar aikin hajji ne ya ku musulmi? Ba na tsammani waxannan tarurruka manya suna wucewa ba tare da izini ba, ko wannan adadi mai girma yana shuxewa ba tare da la’akari ba. Haqiqa waxannan cincirindo na mutane sun zo ne don su amsa kiran da Allah ya yi musu, sun zo suna girmama Allah, Allah yana cewa,

( وَلِلَّهِ عَلَى النَّاسِ حِجُّ الْبَيْتِ مَنِ اسْتَطَاعَ إِلَيْهِ سَبِيلًا وَمَنْ كَفَرَ فَإِنَّ اللَّهَ غَنِيٌّ عَنِ الْعَالَمِينَ 97 ) [آل عمران: 97]

(Kuma Allah ya wajabtawa mutane ziyartar xaki ga wanda ya sami iko zuwa gare shi).

Taro ne babba da duniya kan girgiza saboda shi, maqiya su tsorata da shi, yahudu da nasara su razana, shin kun kiyaye haka? Shin kun ji girman wannan addini, da girman wannan al’umma?

Ya ku ‘yan uwa, haqiqa hajji ya zamo fage ne na haxin kan Al’umma bayan rabuwanta, kuma wata matashiya ta girman wannan al’umma bayan wulaqantuwarta, kuma alamar rayuwarta da samuwarta. Bai kamata al’umma ta gafala daga hikimomin aikin hajji ba da sirrinkansa, domin shi ne maxaurin alaqoqi. Fage na sanin juna da jaddada imani, da zurfafa alaqoqi da zumunci; domin a cikinsa ne musulmi yake sanin xan uwansa daya zo daga guri mai nisa, sai ya ji daga gare shi; ya amayar masa da damuwarsa, ya taimaka masa wajan biyan buqatunsa. Ya ku bayin Allah, haqiqa tsayawa kaxan tare da ayoyin aikin hajji cikin littafin Allah ta’ala ya isa ya baiyyana mana wani abu na sirrikan hajji da hikimominsa, da abin da ya qunsa na ma’anoni tare da tsaftace halaiya, da hanyoyin rabuwa da munanan halaye da ke bayuwa zuwa ado da kyawawa.

Wannan tsokaci yakan baiyana ne cikin mafi girman hikimomi da manufofi na wannan ibada mai girma. Haqiqa tsayuwa ce tare da kaxaita Allah mai girma da xaukaka, wanda aka gina xaki dadaxxe saboda shi, kuma aka sanya nufatarsa daga sassan duniya dan havaka ibdar tauhidi da tsarkake ta ga Allah (S.W.T) wanda ba shi da abokin taraiya. Allah yana cewa,

( وَإِذْ بَوَّأْنَا لِإِبْرَاهِيمَ مَكَانَ الْبَيْتِ أَنْ لَا تُشْرِكْ بِي شَيْئًا وَطَهِّرْ بَيْتِيَ لِلطَّائِفِينَ وَالْقَائِمِينَ وَالرُّكَّعِ السُّجُودِ 26 ) [الحج: 26]

(Kuma yayin da muka ajiye Ibrhaimu a wajan xaki, muka ce, kada ka haxa bauta ta da wani abu, kuma ka tsarkake xaki na ga masu xawafi da masu tsayuwa da masu yin ruku’u, masu yin sujjada).

Haqiqa tataccen tauhidi shi ne qashin bayan halifancin mutum a bayan qasa, kuma mafificin abin da ake nema, mafi girman abin da ake kwaxayi, mafi darajar abin da ake dangantuwa gare shi. Ba a kafa mulki mai qwari sai a kan turaku na tauhidi, kuma ba ya gushewa ya tafi sai don vacewar tauhidin. Daular musulunci ba ta xaukaka ba sai da yaxuwarsa, kuma ba ta qaskanta ba, ba ta tozartaba sai da barbajewarsa.

Shi ne tataccen tauhidi wanda yake tattara mutane zuwa tudun kwanciyan hankali da kariya daga guguwar shirka ga Allah cikin bautarsa, da ayyukansa, da shisshigi cikin sunayensa. Tauhidi ne da ya tattaro kyakkyawan fata wajen Allah, da tsoronsa, da neman taimako da agaji wajensa, kuma kada a yi hukunci aban qasa sai da abin da ya shar’anta (S.W.T). Tauhidi ne da yake mamaye zukatan musulmi da yaqini, wanda aka shar’anta hajji saboda shi, Allah Subhanahu yana cewa,

( حُنَفَاءَ لِلَّهِ غَيْرَ مُشْرِكِينَ بِهِ وَمَنْ يُشْرِكْ بِاللَّهِ فَكَأَنَّمَا خَرَّ مِنَ السَّمَاءِ فَتَخْطَفُهُ الطَّيْرُ أَوْ تَهْوِي بِهِ الرِّيحُ فِي مَكَانٍ سَحِيقٍ 31 ) [الحج: 31].

(Suna masu bin miqaqqen addini, ba masu tara bautarsa da wani ba, kuma duk wanda ya yi shirka da Allah, to kamar ya rikito ne daga sama, sai tsuntsaye su fyauce shi, ko iska ta sulmiya da shi cikin wani guri mai zurfi).

Don haka Allah ya sanya Ka’aba xakin Allah mai alfarma don tsayuwar maslahar mutane. Shi kuwa hajarul Aswadu alama ce ta gane mafara da aka sanya a cikin wannan gini mai albarka. Ba wai guri ne na neman albarka a wjan duwatsu ba, in ban da koyi da Annabi wajan sumbantarsa, da kewaya xaki. Haqiqa Umar Alfaruk (R.A) ya bayyana wannan kyakkyawar fahimtar da faxinsa: (haqiqa ni nasan cewa kai dutse ne da ba ka cutarwa ba ka amfanarwa, kuma ba don ina ganin Manzon Allah yana sumbantar ka ba, da ban sumbace ka ba).

Ya wajaba musulmi ya sani sani na sakankancewa yayin da yake yin xawafi a xaki, ya ke sumbatar Hajarul Aswadi, yake shafar Rukunul Yamani cewa mai amfanarwa da cutarwa shi ne Allah ta’ala shi kaxai. Kuma duk wani tasgaro ga wannan ma’ana yana jefa mutum ne cikin farautar shirka da Allah wanda ba a kafa daxaxxen xaki ba sai don kore shi da gusar da shi. Don haka ne Annabi (ﷺ) ya aiki Abubakar (R.A) a shekara ta tara bayan hijira don ya yi kira cikin mutane, ranar layya cewa kada wani mushriki ya yi hajji daga bana, kuma kada wani mutum ya sake xawafi tsirara. Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.

( ذَلِكَ وَمَنْ يُعَظِّمْ حُرُمَاتِ اللَّهِ فَهُوَ خَيْرٌ لَهُ عِنْدَ رَبِّهِ وَأُحِلَّتْ لَكُمُ الْأَنْعَامُ إِلَّا مَا يُتْلَى عَلَيْكُمْ فَاجْتَنِبُوا الرِّجْسَ مِنَ الْأَوْثَانِ وَاجْتَنِبُوا قَوْلَ الزُّورِ 30 ) [الحج: 30].

(wannan kenan, kuma wanda ya girmama alfarmomin Allah to shi ne mafi alheri gare shi. Kuma an halatta muku dabbobin ni’ima, sai fa idan abubuwan da ake karantawa a gare ku, don haka ku nisanci qazanta daga gumaka, kuma ku nisanci maganar qarya).

Wani la’akarin - Ya bayin Allah - tare da ayoyin hajji; shi ne inda Allah mai buwaya da xaukaka ya sanya hukunce-hukuncensa da ladabansa, don mutane su san abin da ya wajaba a gare su a waxancan farfajiyoyi, da abin da ya wajaba na girmama umarnin Allah da barin wasa da shi, ko kasala da sakaci, domin ibada ba guri ne na wasa, ko tasgaro ba ta kowace fuska ba, don haka faxin Allah subhanahu wata’ala ya zo yana mai gargaxi ga mai tauyewa a cikinta, yana sakaci da ita, inda yake cewa bayan jero wasu abubuwa na daga hukunce-hukuncen aikin hajji. Kamar inda Allah yake cewa,

) ذَلِكَ لِمَنْ لَمْ يَكُنْ أَهْلُهُ حَاضِرِي الْمَسْجِدِ الْحَرَامِ وَاتَّقُوا اللَّهَ وَاعْلَمُوا أَنَّ اللَّهَ شَدِيدُ الْعِقَابِ 196 ) [البقرة: 196]

(Wannan ga wanda iyalinsa ba su kasance mahalartan masallaci mai lafarma ba. Kuma ku ji tsoron Allah, kuma ku sani cewa, Allah mai tsananin uquba ne), Bai ce: Ku sani cewa Allah mai gafara ne mai rahama ba. Wannan kuwa don qarfafa alfarmar hajji ne da kyautata aiwatar da shi yadda ya kamata; domin yana aukuwa ne cikin iyakokin Allah ta’ala da ya shar’anta. Shi ne kuwa yake cewa:

( وَمَنْ يَتَعَدَّ حُدُودَ اللَّهِ فَأُولَئِكَ هُمُ الظَّالِمُونَ 229 ) [البقرة: 229]

(Wanda ya tsallake iyakokin Allah to waxannan su ne azzalumai). Kuma don muminai su lura da gaske cewa, uquba tana tare da sakaci.

Wani la’akari tare da ayoyin hajji, shi ne, su na bayyana aikin hajji a matsayin wani bigire ne na taimakekeniya, da kyauta, da jin abin da wasu ke ji, da toshe buqatunsu, har a guraren ibada. Aya ta zo a jerin bayanin hajji tana nuna girman taimakekeniya, da buqatuwa zuwa tausayawa ga talakawa, da mayunwata da toshe yunwarsu, Allah ta’ala yana cewa,

( لِيَشْهَدُوا مَنَافِعَ لَهُمْ وَيَذْكُرُوا اسْمَ اللَّهِ فِي أَيَّامٍ مَعْلُومَاتٍ عَلَى مَا رَزَقَهُمْ مِنْ بَهِيمَةِ الْأَنْعَامِ فَكُلُوا مِنْهَا وَأَطْعِمُوا الْبَائِسَ الْفَقِيرَ 28 ) [الحج: 28]

(domin su halarci anfani gare su, kuma su ambaci sunan Allah a cikin kwanaki sanannu, a bisa abin da ya azurtasu na daga dabbobin ni’ima. Ku ci daga gare su, kuma ciyar da matalauci faqiri). A cikin wata ayar kuma yana cewa:

( فَإِذَا وَجَبَتْ جُنُوبُهَا فَكُلُوا مِنْهَا وَأَطْعِمُوا الْقَانِعَ وَالْمُعْتَرَّ كَذَلِكَ سَخَّرْنَاهَا لَكُمْ لَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ 36 ) [الحج: 36]

(Idan gefensu ya faxi to ku ci daga gare su, kuma ku ciyar da wanda yake mai kamewa (daga tambaya) da mai bijirowa (da yinta). Hakane muka yassare muku su tsammaninku za ku gode). Shi alqani’i: shi ne wanda baya roqon mutane don jin nauyi tare da jin yunwarsa da talaucinsa, shi kuwa almu’utar shi ne talakan da yake roqon mutane.

La’akari na huxu: Shi ne, martabar taqawa da girman tasirinta, da cewa ita ce ma’auni wanda ake auna ayyuka da shi, ake auna mutane da shi, don haka wasiyya da taqawa ta yawaita a cikin ayoyin hajji, domin haqiqa Allah ta’ala ya ce,

( وَاتَّقُوا اللَّهَ وَاعْلَمُوا أَنَّ اللَّهَ شَدِيدُ الْعِقَابِ 196 ) [البقرة: 196].

(Kuma ku ji tsoron Allah, kuma ku sani Allah mai tsananin uquba ne).

Kuma ya ce,

( وَتَزَوَّدُوا فَإِنَّ خَيْرَ الزَّادِ التَّقْوَى وَاتَّقُونِ يَا أُولِي الْأَلْبَابِ 197 ) [البقرة: 197]

(Kuma ku yi guzuri, domin mafi alherin guzuri shi ne tsoron Allah. Kuma ku ji tsorona ya ma’abota hankali).

Kuma Allah Subhanatu wata’ala ya ce,

( فَمَنْ تَعَجَّلَ فِي يَوْمَيْنِ فَلَا إِثْمَ عَلَيْهِ وَمَنْ تَأَخَّرَ فَلَا إِثْمَ عَلَيْهِ لِمَنِ اتَّقَى وَاتَّقُوا اللَّهَ وَاعْلَمُوا أَنَّكُمْ إِلَيْهِ تُحْشَرُونَ 203 ) [البقرة: 203]

.

(Wanda ya yi gagagwa a kwana biyu babu laifi a kansa, wanda ya jinkirta shi ma babu laifi a kansa, ga wanda ya ji tsoron Allah). Kuma ya ce,

( ذَلِكَ وَمَنْ يُعَظِّمْ شَعَائِرَ اللَّهِ فَإِنَّهَا مِنْ تَقْوَى الْقُلُوبِ 32 ) [الحج: 32]

(Kuma wanda ya girmama alamomin bautar Ubangiji to yana cikin jin tsoron Allah na zukata). Kuma subhanahu ya ce,

( لَنْ يَنَالَ اللَّهَ لُحُومُهَا وَلَا دِمَاؤُهَا وَلَكِنْ يَنَالُهُ التَّقْوَى مِنْكُمْ 37 ) [الحج: ٣٧].

(Namansu da jinayansu ba sa samin Allah, sai dai tsoron Allah ne daga gare ku zai riske shi).

Tsoron Allah - ya bayin Allah - shi ne matattarar alheri gaba xaya.

Haqiqa kai msulmi, idan ka bautawa Allah a kan haske, kana fatan ladan Alah, ka bar haramtattun abubuwan da Allah ya haramta, a bisa haske daga Allah, kana tsoron uqubarsa, haqiqa ka tabbatar da tsoron Allah xungurungum xinsa a rayuwar ka, wanda qarqashinsa za ka tabbatar da haqqoqin da aka rataya maka game da mahaliccin ka, da ‘yan uwanka a addini.

Dukkan kujuba-kujuba ta ayyukan hajji - Ya bayin Allah –suna nuna wannan manufa, domin musulmi kamar jiki xaya ne, kamar gini ne da sashinsa kan qarfafar sashi. musulmai a farfajiyoyin hajji mai albarka suna rayuwa a lokutan da ma’anar taqawa da take fitar da tushen yan uwantaka mai qaqqarfan maxauri ke tabbata. Wadda take haxa kan musulmi tare da savanin garuruwansu da harasansu, a yayin da alhazai ke canja tufafinsu na yau da kullum, su sa tufafin hajji iri xaya, su fito cikin kama xaya, su fuskanci Ubangiji xaya, da talbiya xaya, su jefar da duk wani kirari a qasa, da wani take na vangaranci, su rungumi wannan talbiyya, suna kewaya xaki xaya, suna aiwatar da ibada xaya. Lallai wanna hoto mai rai na amafanin taqawa, da kuma yake nunawa mutane cewa babu wasu dalilai na hankali da za su sa su su riqa rayuwa cikin qiyayya da qyamar juna, da rarrabuwa dama da hauni. Babu wasu dalilai da za su sa masu girmankai za su yi girman kai, masu xagawa su yi xagawa. Babu wasu dalilai da za su ba da damar yin alfahari da dangi ko laqabila. Kai idan taqawa ta ginu a zuciyar bawa za ta sanya shi yana halarto da cewa Allah ta’ala ya sanya nasabar mutane da jinsunansu duk ga iyaye biyu, don ya sanya mahaifar Nana Hauwa’u wata mahaxa ce mai faxi wadda zumunce-zumunce kan sassarke a jikinta, kuma alaqoqi kan qarfafu da ita. Allah ya ce,

( يَا أَيُّهَا النَّاسُ إِنَّا خَلَقْنَاكُمْ مِنْ ذَكَرٍ وَأُنْثَى وَجَعَلْنَاكُمْ شُعُوبًا وَقَبَائِلَ لِتَعَارَفُوا إِنَّ أَكْرَمَكُمْ عِنْدَ اللَّهِ أَتْقَاكُمْ إِنَّ اللَّهَ عَلِيمٌ خَبِيرٌ 13 ) [الحجرات: 13]

(Ya ku mutane haqiqa mun halicce ku daga namiji, da mace, kuma mun sanya ku al’ummai da qabilu don ku san juna).

Ya ku bayin Allah! Lalle akwai hikimomi a cikin aikin hajji da bai kamata su vuya ga ma’abota hankali ba.

Daga ciki akwai cewa, shi aikin hajji gagarumin taro ne na musulunci da yake kira zuwa haxin kan al’umma da hunqulewarta. Alhazai sukan taru a guri xaya, a fili xaya, suna bautar Allah, bayan sun haxu gabanin haka a sallah xaya, sun yi azumin wata xaya, suna yin sahu suna daura da juna. Duk waxannan abubuwa ne da suke nuna haxuwar kan al’umma, kuma cewa ita wannan al’umma ba za ta rabauta ba sai da haxuwa da curewa. Sannan kuma tsawatarwa ce a kan jayayya da rarrabuwa, kuma cewa musulmi ba a rinjayesu ba sai saboda rarrabuwarsu da xaixaituwarsu, kuma maqiya suna samin nasara yayin da musulmi suka kasa magana da kalma xaya, suka yi garuruwansu a yaga, kowa ya yanki qasarsa mai zaman kanta. Allah ta’ala ya ce,

( وَأَطِيعُوا اللَّهَ وَرَسُولَهُ وَلَا تَنَازَعُوا فَتَفْشَلُوا وَتَذْهَبَ رِيحُكُمْ ) [الأنفال: 46].

(Kuma kada ku yi jayayya sai ku yi asara, kuma qarfinku ya tafi).

Daga cikin hikimomin aikin hajji akwai jaddada imani da gyara zuciya. Cututtukan fitinu da sha’awoyi kan bijirowa mutane, shi ko hajji yana tumbatsa da alamomi na tauhidi, dake goge kurakuri, ya cika kyawawan ayyuka. Ya zo a cikin hadisi cewa, (wanda ya yi hajji, sannan bai yi batsa ba, bai yi fasiqanci ba, zai komo daga zunubansa kamar ranar da mahafiyarsa ta haife shi). Bukhari da Muslimu ne suka rawaito.

Yana daga cikin hikimomin hajji cewa, shi jajircewa ne a lokacin qasqanci, kuma tsayawa ne kyam a lokacin rauni. Domin an kewaye wannan al’ummar ta ko ina, ana tuhumarta a cikin addininta, su kuwa mabiyansa kan xauki wannan da rauni da karvar kaye. To a wannan hali ne alhazai ke zuwa da wannan taro don su raya ma’anonin dagewa da sadaukantaka. Musulmi suna xaukaka bayan rauninsu, su yi qarfi bayan kayan da aka yi musu, su haxa kai bayan rarrabuwarsu. Allah ya ce,

( وَاعْتَصِمُوا بِحَبْلِ اللَّهِ جَمِيعًا وَلَا تَفَرَّقُوا ) [آل عمران: 103].

(Kuma ku yi riqo da igiyar Allah kada ku rarraba).

Yana daga cikin hikimomin hajji cewa, shi saqone zuwa duniyar kafirai cewa wannan al’ummar ba za ta tava saurarawa ba game da addininta, ba za ta yi ciniki a bisa akidunta ba. Mai qarfice tare da Ubangijinta, mai buwayiya ce da addininta. Kafirai sau dadama sukan firginta su tsorata saboda ganin irin wannan dandazo na jama’a. Sau tari mai niyar cin zarafin wannan al’umma yakan yi shiru ya fasa ganin irin wannan haxuwa ta musulmi. Lallai al’ummar mu tana shelanta riqonta da addininta da qanqamewarta ga Alqur’aninta ta hanyar wannan aikin hajjin. Wannan addini shi ne rayuwarta, kuma alamar wanzuwarta, mavuvvugar girmanta da bayyanarta. Allah yana cewa,

( لَقَدْ أَنْزَلْنَا إِلَيْكُمْ كِتَابًا فِيهِ ذِكْرُكُمْ أَفَلَا تَعْقِلُونَ 10 ) [الأنبياء: 10]

(Haqiqa mun saukar muku da wani littafi wanda xaukakar ku ke ciki yanzu ba kwa hankalta ba).

Su ma’abota imani duk da abin da ke shigarsu na rauni da qasqanci sai dai suna riqo da addininsu, kuma suna da abin da zai farkar da su ya raya zukatansa cikin ibadunsu. Kamar hajji da abin da ke cikinsa na yawan talbiya da yankan hadaya da layya, da tauhidi da sakankancewa, da addu’a, da tsoron Allah da qanqan da kai.

Ina faxan abin da kuke ji, kuma ina neman gafarar Allah ga kaina da ku, ku nemi gafararsa daga kowane zunubi, lallai shi mai gafara ne mai jin qai.

Huxuba Ta Biyu

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, kyakkyawan qarshe yana ga masu tsoron Allah, kuma babu sakamakon wuce gona da iri sai a kan azzalumai. Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kaxai, ba shi da abokan taraiya, majivincin salihai, kuma ina shaidawa cewa Annabi Muhammadu bawansa ne kuma manzonsa ne, kuma cikamakin Annabawa.

Bayan haka, Ya ku mutane! Lallai yana daga cikin hikimomin aikin Hajji cewa shi, tunatarwa ne zuwa ga lahira da faxakarwa zuwa wannan ranar mai tsanani. Allah yana cewa,

( رَبَّنَا إِنَّكَ جَامِعُ النَّاسِ لِيَوْمٍ لَا رَيْبَ فِيهِ إِنَّ اللَّهَ لَا يُخْلِفُ الْمِيعَادَ 9 ) [آل عمران: 9]

(Ubangijinmu lalai kai mai tattara mutane ne ga yinin da babu kokonto a cikinsa, lalle Allah ba ya sava alkawari).

Ranar Arfa qaramin hoto ne filin tashi ranar Alqiyama. A cikinsa akwai tunatarwa ga taruwar mutane a gaba ga Ubangijinsu, da qasqantar da kansu gare shi, alhali wahala da gajiya ta sa me su.

Yana daga cikin hikimomin hajji cewa, aikin hajji wata alama ce ta zahiri kuma ta musamman dake nuna riqo da addini da ibada. Babu wata al’umma daga al’ummomi da aka bawa irinta, wannan kuwa yana nuna darajar wannan al’ummar, da kuma cewa, ita ce al’umma madauwamiya, domin duk abin da zai same ta na masifofa ba zai kawar da ita ba matuqar ta fuskanci Ubangijinta, ta nufi xakinsa da alfarmarsa. To don menene za mu xebe qauna alhalin ga hajji kuwa yana jaddada haxinkai da mahabba tsakaninmu? Don me muke baqin ciki ga hajji kuwa yana xaure dangantaka, yana qara mana dunqulewa da soyaiya.

Ya ku Musulmi, lallai wanda duk zai nufi wannan xaki zai ji qarin alfahari da jin girma, kuma imanisa kan haskak a yayin da zai ga wannan xaki, da zai ga turmutsetseniyar mutane a wajansa, yana ganin irin kwaxayinsu ga bin koyarwar Annabi, alhali sun zo daga gurare masu nisa. Wanda zai lura da wannan hajji, zai riski kasancewar wannan al’umma mafificiyar al’umma ce, kuma za ta iya kamuwa da cuta, amma ba za ta mutu ba, tana iya yin rauni amma ba za ta valvalce ba. Tana dai buqatar wanda zai farkar da ita, ya shiryar da ita, ya nuna mata abin da zai amfane ta, ya gyara mata halinta.

Yana daga cikin hikimomin hajji, cewa shi taro ne da sunan musulunci, Allah ya tattara su a kan addininsa, ya tattaro su a kan shari’arsa, ba kishin qabila ko launi ko jinsi ne ya tara su ba. Wannnan addinin ne ya tattara su, imani ne ya haxa kansu. A cikin wannan akwai qarfafa cewa wannan al’umma ba abin da zai iya haxa kanta sai musulunci, ba mai tattara xaixaicewar ta sai imani, domin shi ne addinin haxinkai, da taimakekeniya da rungumar juna.

Haqiqa a cikin ayoyin hajji Allah yana tuna wa musulmi cewa, wannan addini abu ne da ba makawa sai sun riqe shi, kuma yana tuna musu cewa, duk wata al’umma da take watsi da lalmarin addinin, ta take wofintar da shari’ar Ubangijinsa, ko ta riqe shi tana jin kunya, ko tana ganin addini ne da ya riqe mata wuya, to fa ta yi watsi ne da mafi girman qarfinta, da tushen xaukakarta, da sakin hanyar samun babban rabo a duniya da lahira. Kuma kowace al’umma da ta rasa addininta a cikin zamantakewarta, ko ta rungumi tutar ci-baya, to za ta kasance cikin ruxani ba makawa, za ta yi ta bankaura, Allah ya musanya xaukakarta da qasqanci, ya musanya kwanciyar hankalinta da tsoro, idan ta juya baya sai Allah ya canza ta da wasu mutanen da ban, sannan ba za su zamo kwantankwacinsu ba.

Al’ummar da ba ta jin vuqatuwarta zuwa lazimtar addini, wannan al’umamce da ba ta da imani, sannan ta yi nisa daga rahamar mai rahama; domin Annabi yana cewa: (Abu uku duk wanda ya same su to ya sami zaqin imani; wanda Allah da Manzonsa suka zamo mafi soyuwa gare shi daga waninsu. Kuma ya so mutum, ba don komai ba sai don Allah. Kuma ya qyamaci komawa kafirci bayan Allah ya tserar da shi daga gare shi kamar yadda yake qyamar a jefa shi cikin wuta). Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi. Lallai babu mafi qasqanci gurin Allah daga al’ummar da yin addini bai shiga lokon zuciyarta ba, ba ratsa jininta da tsokarta ba, sannan za ta yi ta raguwa ne tana wulaqanta, ta faxa rauni bayan qarfi. Haqiqa ba kowa ne yake samun shiriyar Allah ba, sai dai ita wata baiwa ce daga Allah ta rahamarsa. Ya wajaba ga wanda aka ba shi ita ya riqe ta gam-gam. Kuma kada burace-buracen zukata da farfagandar maqiya su sami hanyar raunana shika-shikan addinin a cikin zukata, ko muryoyin masu kira da ajuyawa addini baya da sunan ‘yanci da kawo gyara, su sami tasiri. Haqiqa qira ta haqiqa itace qirar Allah),

( صِبْغَةَ اللَّهِ وَمَنْ أَحْسَنُ مِنَ اللَّهِ صِبْغَةً وَنَحْنُ لَهُ عَابِدُونَ 138 ) [البقرة: 138]

(Wanene ya fi Allah iya qira, kyautata qirara, kuma mu masu bauta ne gare shi). Allah yana cewa,

( وَالَّذِينَ آَمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ لَا نُكَلِّفُ نَفْسًا إِلَّا وُسْعَهَا أُولَئِكَ أَصْحَابُ الْجَنَّةِ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ 42 وَنَزَعْنَا مَا فِي صُدُورِهِمْ مِنْ غِلٍّ تَجْرِي مِنْ تَحْتِهِمُ الْأَنْهَارُ وَقَالُوا الْحَمْدُ لِلَّهِ الَّذِي هَدَانَا لِهَذَا وَمَا كُنَّا لِنَهْتَدِيَ لَوْلَا أَنْ هَدَانَا اللَّهُ لَقَدْ جَاءَتْ رُسُلُ رَبِّنَا بِالْحَقِّ وَنُودُوا أَنْ تِلْكُمُ الْجَنَّةُ أُورِثْتُمُوهَا بِمَا كُنْتُمْ تَعْمَلُونَ 43 ) [الأعراف:42 - 43]

.

(Kuma waxanda suka yi imani suka ba da gaskiya ba ma xora wa rai sai abin da za ta iya, waxannan su ne ma’abota aljanna. Su masu dauwamane a cikinta, kuma muka cire musu abin da yake zukatansu na qullata, suka ce, godiya ta tabbata ga Allah wanda ya shiryar da mu ga wannan, kuma mu ba mu kasance za mu shiriya ba ba don Allah ya shiryar da mu ba. Haqiqa manzannin Ubangijinmu sun zo da gaskiya. Kuma aka kiraye su da cewa, waccan aljanna an gadar muku da ita ne saboda abin da kuka kasance kuna aikatawa).





Tags:




Mahmoud Ali El-Banna