Manufofin huxubar
Bayanin falalar koyon karatun Alqur’ani
Gargaxin mutane daga shagalta ga barin Alqur’ani
Bayanin ladubban karanta Alqur’ani
Huxuba Ta Farko
Yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma muna neman tsarinsa dag sharrin kawukanmu da munanan ayyukanmu, wanda Allah ya shiryar babu mai vatar da shi, wanda ya vatar babu mai shiryar da shi, kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kaxai ne bashi da abokin taraiya. Kum aina shaidawa cewa, Annabi Muhammadu bawansa ne manzonsa ne. (Ya ku waxanda sukayi imani kuji tsoron Allah yadda ya cancani aji tsoronsa, kada ku mutu face kuna musulmi). (Ya ku mutane kuji tsoron Ubangijinku wanda ya halicceku daga rai guda xaya, kuma ya halicci matarasa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga gare su (su biyu). Ku ji tsoron allah wanda kuke yi wa juna magiya da shi, (kuma ku kiyaye zumunci, lalle Allah mai kula ne da ku). (Ya ku waxanda suka yi imani kuji tsoron allah kuma ku faxi magana ta daidai, sai allah ya gyara muk uaiyukanku, kum aya gafarta muku zunubanku, wanda yabi Allah da Manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lale mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawun shiriya shiriyar Annabi Muhammadu (ﷺ) kuma mafi sharrin al’amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wani qagaggen abu (a addini) bidi’a ce, duk wata bidi’a vata ce, duk wani vata kuma yana wuta.
Bayan haka;
Ya ku bayin Allah: Zancen mu game da littafin Allah, rabautarku na tare mafita daga fitinu. A cikinsa akwai labarin abin da ke gabanin ku, da qissar abin da ke bayanku, da hukuncin abin da ke tsakaninku. Shi ne tantancewa, ba wargi ba. Wanda ya bar shi don tsaurin kai sai Allah ya karya shi. Wanda ya nemi shiriya ba a cikin sa ba sai Allah ya vatar da shi. Shi ne igiyar Allah mai qwari. Ambato mai hikima. Tafarki madaidaici, shi ne wanda soye-soyen zukata ba sa karkacewa da shi, harasa ba su rikicewa da shi, malamai ba sa qoshi da shi. Ba ya tsufa saboda yawan karantawa, abubuwan mamakinsa basa qarewa. Wanda ya yi magana da shi ya yi gaskiya. Wanda ya yi aiki da shi zai sami lada, wanda ya yi hukunci da shi ya yi adalci, wanda ya yi kira zuwa gare shi ya yi kira zuwa tafarki madaidaici. Wannan shi ne littafin Allah; ku mai da hankali wajen koyansa da karanta shi da tunani a cikinsa, ku sanar da ‘ya’yanku shi, ku raine su a kan karanta shi da sonsa, har su saba da shi, sai halayensu su tsarkaka, zukatansu su tsarkaka, su kasance daga mahaddatansa, domin yaro idan ya koyi Alqur’ani zai balaga yana mai sanin abin da yake karantawa a sallarsa, kuma haddace Alqur’ani a yarinta ya fi haddace shi bayan an girma, kuma yafi zama a qwaqwalwa, yafi kafuwa da tabbatuwa, domin koyo a yarinta kamar zane ne a kan dutse.
Ya ku bayin Allah, ku ji tsoron Allah, ku himmatu da wannan littafi Allah mai buwaya da xaukaka ya ce:
(إِنَّ الَّذِينَ يَتْلُونَ كِتَابَ اللَّهِ وَأَقَامُوا الصَّلَاةَ وَأَنْفَقُوا مِمَّا رَزَقْنَاهُمْ سِرًّا وَعَلَانِيَةً يَرْجُونَ تِجَارَةً لَنْ تَبُور29 لِيُوَفِّيَهُمْ أُجُورَهُمْ وَيَزِيدَهُمْ مِنْ فَضْلِهِ إِنَّهُ غَفُورٌ شَكُورٌ30) [فاطر: ٢٩ - ٣٠].
(Haqiqa waxanda suke karanta littafi kuma suka tsaida sallah, kuma suka ciyar daga abin da muka azurta su a voye da sarari, suna fatan wani kasuwanci da ba zai tave ba. Domin ya cika musu ladansu kuma ya qara musu daga falalarsa, lalle shi mai yawan gafara ne mai yawan godiya).
Kuma Allah ta’ala ya ce:
(وَرَتِّلِ الْقُرْآَنَ تَرْتِيلًا4) [المزمل: ٤].
(Kuma ka kyautata karuntun alqur’ni iya kyautatawa).
Bukhari ya ruwaito cikin sahihinsa daga Usman xan Affan ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, "Mafi alherinku shi ne wanda ya koyi Alqur’ani kuma ya koyar da shi".
Kuma daga Aisha (R.A) ta ce: Manzon Allah ya ce, “Wanda yake karanta Alqur’ani alhali yana qwararre a karatunsa yana tare da mala’iku jakadun Allah, masu girma, masu biyayiya. Wanda kuwa yake karanta shi yana in’ina cikinsa, yana masa wahala to yana da lada biyu). Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.
Kuma Muslim ya rawaito daga Abu Umamata Al-Bahili ya ce, Na ji Manzon Allah (ﷺ) yana cewa, "Ku karanta Alqur’ani, domin shi zai zo ranar Alqiyama yana mai ceto ga ma’abotansa".
Kuma an karvo daga Abu Hurairah, daga Annabi (ﷺ) ya ce, "Wasu mutane ba za su taru ba a wani xaki daga xakunan Allah ta’ala suna karanta littafin Allah, suna bitarsa a tsakaninsu, face nutsuwa ta sauko musu, rahama ta lulluvesu, mala’iku sun kewayesu, Allah ya ambace su cikin waxanda ke wajansa". Muslim ne ya rawaito shi. Kuma an karvo daga Abu Hurairata, Annabi (ﷺ) ya ce, (Za a zo da mahaddacin Alqur’ani ranar Alqkiyama sai Alqur'anin ya ce, "Ya Ubangiji ka yi masa ado". Sai a sanya masa kambin girma. sannan ya sake cewa, "Ya Ubangiji ka qara masa". Sai a sanya masa rigar girma. Sannan ya sake cewa: "Ya Ubangiji ka yarda da shi". Sai ya yarda da shi. sai a ce masa: Yi karatu ka qara xaukaka, sai ya qara samun kyakkyawan aiki da kowace aya da ya karanta". Tirmizi ne ya rawaito. Kuma hadisi ne kyakkyawa.
Wannan wani abu ke nan daga falalar karanta Alqur’ani da abin da mai karatun Alqur’ani yake da shi na lada. Kuma shi ne wasiyyar Annabi (ﷺ) wadda ya yi mana wasiyya da ita, kamar yadda Imamu Ahmad ya rawaito daga Abu Sa’id cewa, Annabi (ﷺ) ya ce, (Ina maka wasiyya da tsoron,Allah, domin shi ne kan kowane abu, kuma na hore ka da jihadi domin shi ne rahbaniyancin Musulunci. Kuma ka lazimci ambaton Allah da karanta Alqur’ani, domin shi ne ruhinka a sama da matsayinka a qasa). Albani ya inganta shi.
Ya ku bayin Allah, haqiqa karatun Alqur’ani yana da ladubba daga cikinsu akwai:
Ikhlasi ga Allah (S.W.T) domin Annabi (ﷺ) ya bamu labari game da waxanda za a rura wuta da su ranar Alqiyama su mutum uku ne: a cikinsu akwai mai karanta Alqur’ani, Annabi (ﷺ) ya ce game da da su, "Lallai Allah idan ranar Alqiyama ta yi zai sauko zuwa bayi, domin yin hukunci tsakanin su, kowace al’umma tana durqushe, farkon wanda za a kira shi ne mutumin da ya haddace Alqur’ani, da mutumin da aka kashe a tafarkin Allah, da mutum mai yawan dukiya. Sai Allah ya ce da makaranci, Shin ban sanar da kai abin da na saukarwa Manzona ba? Sai ya ce, haka ne ya Ubangiji ka sanar dai. Sai ya ce, to me ka aikata? Sai ya ce, na kasance ina tsayuwa da karatunsa lokutan dare da rana. Sai Allah ya ce masa, ka yi qarya, Mala’iku ma su ce masa, qarya kake. Allah ya ce da shi, kawai ka yi nufin a ce, ai wane makaranci ne, kuma an faxi haka. Sannan sai a ja shi zuwa wuta wa’iyazu billahi.
Ya karanta shi bisa tsarki. babu shakka kuwa karatunsa bisa tsarki shi ya fi daga karanta shi ba tsarki.
Daga ciki akwai: Yin asuwaki; domin Sayyidina Ali yana cewa, "Haqiqa bakunan ku hanyoyi ne na Alqur’ani, don haka ku daxaxa su da yin aswaki" Ibn Majah ne ya ruwaito. Kuma annabi (ﷺ) ya ce, (Haqiqa bawa idan ya tashi yana sallah sai Mala’ika ya zo masa ya tsaya bayansa, don ya ji Alqur’ani, ya kusanto, ba zai gushe ba yana saurare har ya sanya bakinsa a kan bakinsa, don haka ba zai karanta Alqur’anin ba sai ayar ta shige cikin Mala’ikan). Baihaqi ne ya rawaito shi daga Aliyu (R.A). kuma Albani ya inganta shi.
Yana daga fa’idojin aswaki ga mai karatun Alqur’ani cewa ba zai fitar da wata qazanta daga bakinsa ba da zata cuci Mala’ika da ya zo sauraronsa.
Daga ciki akwai, neman tsarin Allah daga shaixan la'ananne, domin Allah ta’ala ya ce:
(فَإِذَا قَرَأْتَ الْقُرْآَنَ فَاسْتَعِذْ بِاللَّهِ مِنَ الشَّيْطَانِ الرَّجِيمِ98) [النحل: 98]
(Kuma idan za ka karanta Alqur’ani to ka nemi tsari da Allah daga shaixani tsinanne).
Wasu malamai suka ce: wajibi ne karanta isiti’aza yayin karatun Alqur’ani, saboda zahirin umarni. Sauran malamai kuwa suka ce, Mustahabi ne.
Sigar da aka fi so ita ce:
(أعوذ بالله السميع العليم من الشيطان الرجيم من همزه ونفخه ونفثه).
Ma’ana: (Ina neman tsari da Allah mai ji masani, daga shaixan la’ananne, daga zungurinsa da busarsa da tofinsa).
Kamar yadda hakan ya tabbata daga Annabi (ﷺ).
Daga ciki: akwai yin bisimillah. Ya wajaba mai karatu ya kiyaye karanta bisimillah a farkonkon kowace sura ban da (Bara’a). Domin ya tabbata cewa Annabi (ﷺ) ana sanin qarwewar sura (a karatunsa) da fara sura ta gaba da bisimillah, sai a guri xaya shi ne tsakanin Anfal da Bara’a.
Daga ciki akwai karanta Alqur’ani dalla-dalla. Domin Allah ta’ala ya وَرَتِّلِ الْقُرْآَنَ تَرْتِيلًا [المزمل: 4]
( kuma ka kyautata karatun Alqur’ani iyakar kyautatawa).
Ummu salama ta siffanta karatun Manzon Allah (ﷺ) da cewa, karatu ne da ake rarrabe shi harafi bayan harafi.
Bukhari ya ruwaito daga Anas cewa, an tambaye shi game da karatun Annabi (ﷺ)? Sai ya ce, "Ya kasance yana jan karatunsa". Sannan ya karanta “Bismillahir Rahmanir Rahim), yana mai jan “Allaah” - Ma’ana ja na xabi’a wato harka biyu - yana jan “Arrahman”, yana jan (Arrahim). Bukhari da Muslim sun ruwaito daga Ibn Mas’ud cewa, wani mutum ya ce masa, Ni nakan karanta Almufassal (wato daga Hujurat zuwa Nass) cikin raka’a xaya. Sai Abdullahi ya ce, “Gaggatsa karatu kamar kana gaggatsa waqa”? Yana masa inkarin saurin karatun. Haqiqa wasu mutane suna karanta Alqur’ani amma ba ya wuce qashin haqarqarinsu. Idan Alqur’ani ya shiga zuciya ya kafu a cikinta sai to zai yi amfani.
Daga cikin akwai kyautata murya da Alqur’ani; An karvo daga Barra’u (R.A) ya ce, “Na ji Annabi (ﷺ) yana karanta wattini wazzzaitun a cikin sallar isha’i, ban tava jin wanda ya fishi kyan sauti ko qira’a ba”. Bukhari ne ya ruwaito.
Domin faxinsa (ﷺ) "Ku kyautata Alqur’ani da sautukanku, domin kyakkyawan sauti yana qarawa Alqur’ani kyawu". Hakim ne ya ruwaito shi daga Bara'u bn Azib. A wata ruwayar, (Kyan murya ado ne ga Alqur’ani) Albani ya inganta shi daga hadisin Ibn Mas'ud.
Yana daga cikin ladubban karatun Alqur'ani rera shi: Wannan yana bin abin da aka ambata na kyautata sauti. Domin Annabi (ﷺ) ya ce, "Ba ya daga cikinmu wanda ba ya rera karatun Alqura’ni ba". Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi daga Sa'ad bn Abi waqqas. Hakanan hadisin da Annabi yake cewa, "Allah bai yi sauraro ga wani abubu ba kamar yadda yake sauraro ga wani Annabi mai kyan sauti da ya ke rera karatun Alqur’ani). Bukhari ne ya ruwaito shi daga Abu Hurairata.
Ya ku bayin Allah,
Yana daga ladubban tilawa tsayawa a kan ayoyi. Koda tana da alaqa da ta gabonta wajan ma’ana. Domin ya zo a hadisi sahih daga Annabi (ﷺ) cewa ya kasance yana yayyanka karatunsa aya aya. Alhamdulillahi Rabbil Alamin, sai ya tsaya. Arrahmain rahim, sai ya tsaya. Imam Ahmad ya ruwaito shi daga Ummu Salamah.
Yana daga cikin su, kada wani mutum ya xaga muryarsa da karatunsa a kan na xan’uwansa, domin xaga murya a cikin wannan hali cutarwa ne ga maqocinsa. Ya zo a cikin hadisin Annabi (ﷺ) ya ce, (Kowane daga cikinku mai ganawa ne da Ubangijinsa, don haka kada sashinku ya cuci shashi. Kada sashinku ya xaga (murya) bisa sashi wajen karatu).
Sannan idan ya ji gyangyaxi to sai dakata da karatun. Domin Ahmad da Muslim sun rawaito, daga Abu Hurairah daga Annabi (ﷺ) ya ce: (Idan xayanku ya tashi da dare, sai karatun Alqur’ani ya rikice masa a harshansa, bai san mai yake cewa ba, to ya kwanta). yana nufin: Ya je ya yi barci, don kada ya cakuxa Alqur’ani da wani abu, ko ayoyi su cakuxe masa, ya gabatar da wasu ya jinkintar da wasu, ko ya yi shirme ya faxi wasu haruffan da ba su ciki, da makamancin wannan. To zararar ya ji barci zai kama shi, to ya wajaba ya je ya kwanta.
Sannan kada ya karanta Alqur’ani a ruku’i ko sujjada. Saboda faxinsa (ﷺ): (Haqiqa ni an hana ni karanta alqur’ani a ruku’i, ko sujjada. Shi ruku’i ku girmama Ubangiji a cikinsa. Ita kuwa sujjada ku yi qoqarin yin addu’a (a cikin ta), tabbas a amsa muku). Dalilin wannan, shi ne abin da Shaihul Islam-Allah ya ji qansa- yake cew, "Shi ruku’i da sujjada suna daga guraren qasqan da kai, don haka bai kamata a karanta Alqur’ani a wajan qasqantar da kai ba, tasbihi ne kawai, da tsarkake Allah (S.W.T) a cikinsu".
In afaxar abin da kuke ji, ina neman gafarar Allah gare ni da ku da sauran Musulmi daga dukkan zunubi, lallai shi mai gafara ne mai jin qai.
Godiya ta tabbata ga Allah, tsira da aminci su tabbata ga mafi xayantakar manzanni Annabinmu Muhammadu da alayensa, da sahabbansa gaba xaya.
Yaku bayin Allah, haqiqa yana daga abin da ya kamata ga mai karatun Alqur’ani yayi kuka yayin karatu domin Allah ta’ala ya ce yana yaban muminai da haka: (kuma suna kifuwa bisa havovinsu suna kuka, kuma yana qara musu tsoron Allah).
Kuma an karvo daga Ibn Mas’ud ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce min: "Ka karanta min Alqur’ani". Na ce, Yanzu na karanta maka bayan kai aka saukarwa? Ya ce: "Ni ina son na ji shi daga wani na". Sai na karantam masa suratun Nisa’i har na zo in da Allah ya ke cewa,
(فَكَيْفَ إِذَا جِئْنَا مِنْ كُلِّ أُمَّةٍ بِشَهِيدٍ وَجِئْنَا بِكَ عَلَى هَؤُلَاءِ شَهِيدًا41) [النساء: 41]
Ma’ana: (To yaya lamarinsu zai kasance yayin da muka zo da mai shaida daga kowa ce al’umam kuma muka zo da kai mai shaida a kansu) Sai ya ce: «Ya ishe ka hakanan). Sai ga idanunsa suna zubar da hawaye. Bukhari ya rawaito.
Wani sahabi ya ce, (Na zo wa Annabi (ﷺ) ya na sallah, cikinsa na da qugi kamar qugin tukunyar tasa a kan wuta). Yana nufin saboda kuka. Nasa’i ne ya rawaito.
Daga cikin ladubban karatun Alqur'ani akwai buqatar tuttuntuni a kan ma’anoninsa yayin karatunsa. Wannan kusan shi ne mafi muhimmancin ladaban karatun Alqur’ani gaba xaya, kuma shi ne amfanin karatun na haqiqa. Ga shi Allah ta’ala ya ce:
كِتَابٌ أَنْزَلْنَاهُ إِلَيْكَ مُبَارَكٌ لِيَدَّبَّرُوا آَيَاتِهِ وَلِيَتَذَكَّرَ أُولُو الْأَلْبَابِ29) [ص: 29]) (Litatafi ne da muka saukar da shi mai albarka domin su yi tuntuntuni game da ayoyinsa, kuma domin ma’abota hankali su wa’azantu).
Shi kuwa ba ya samuwa sai ga wanda ya yi tunani cikin zancen Allah mai girma da xaukaka, ya halarto da girmansa (S.W.T) ya yi la’akari cikin zantuttukan Alqur’ani, ya halarto cewa, yana karatu ne da niyyar fhaimta da aiki da abin da yake karantawa. Amma mai karanta Alqur’ani da harshe, yayin da zuciyarsa ta ke wani gurin ba zai sami amfanin da ake samu daga karatun Alqur’anin ba. Allah ya ce,
(أَفَلَا يَتَدَبَّرُونَ الْقُرْآَنَ أَمْ عَلَى قُلُوبٍ أَقْفَالُهَا24) [محمد: 24]
(Yanzu ba za su yi tuntuntuni cikin Alqur’ani ba, koko a kan zukatan su akwai kwaxuna ne).
An karvo daga Huzaifah, ya ce, Na yi sallah tare da Annabi (ﷺ) wani dare sai ya fara karatun Baqara, sai na ce, Zai yi ruku’u wajan aya ta xari, sai ya zarce; na ce zai yi ruku’u wajan aya ta xari biyu, sai ya zarce, na ce, zai yi raka’a guda ne da ita, sai ya wuce ya fara Nisa’i ya karance ta, ya fara Ali Imrana ya karantata, yana karatu a hankali, idan ya zo ayar tasbihi, sai yayi tasbihi, idan ya zo ayar roqo sai ya roqa, idan ya zo ayar neman tsari, sai ya nemi tsari, sannan ya yi ruku’u...). Nasa’i ne ya rawaito shi.
Haqiqa Annabi (ﷺ) ya ba mu labarin Khawarijawa, da cewa su mutane ne da suke karanta Alqur’ani, amma ba ya wuce maqogwaransu. Hakanan Manzon Allah (ﷺ) ya ce, (Wanda ya karanta Alqur’ani a qasa da kwana uku ba zai fahimce shi ba).
Ana tuntuntuni ne don aiki: An karvo daga Abu Abdurrahman as-Sulami ya ce: wanda yake karanta mana Alqur’ani daga sahabban Annabi (ﷺ) ya ba mu labari cewa su sun kasance suna karantar ayoyi goma daga Manzon Allah (ﷺ), ba sa ci gaba da wasu goman har sai sun ko yi abin da ke cikin waxannan na ilimi da aiki, suka ce, Sai mu ka koyi Ilimi da aiki tare.
Ya ku bayin Allah; Idan mai karatun Alqur’ani ya zo wajan sujjadar tilawa zai yi sujjada. Abu Hanifa ya ce, wajibi ce. Amma magana mafi rinjaye maganar Umar (R.A) cewa sujjadar tilawa mustahabbi ce ba wajibi ba. Kuma wannan ita ce maganar jamhurun malamai, siffar sujjadar shi ne ya yi kabbara ya yi sujjada.
Ya halatta mai karatu ya karanta Alqur’ani a zaune, ko a tsaye, ko a tafe, ko kwance, duk wannan ya halatta, domin Allah ta’ala ya ce,
(الَّذِينَ يَذْكُرُونَ اللَّهَ قِيَامًا وَقُعُودًا وَعَلَى جُنُوبِهِمْ وَيَتَفَكَّرُونَ فِي خَلْقِ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ رَبَّنَا مَا خَلَقْتَ هَذَا بَاطِلًا سُبْحَانَكَ فَقِنَا عَذَابَ النَّار191)ِ [آل عمران: 191]
(Waxannan da suke ambaton Allah a tsaye, da zaune, da kuma kishingxe, suke tunani cikin halittar sammai da qasa).
Sai dai da zai zauna yana mai qasqantar da kai, da ya,fi da ya zauna yana mai kishingixa kan gefensa. Annabi (ﷺ) ya kasance yana zaman harxe bayan sallar Alfijir ya fuskanci alqibla yana ambaton Allah har rana ta fito.
Kuma yana daga ladaban karanta Alqur’ani, kada ya saukw Alqur’ani a qasa da kwana uku; saboda faxinsa (ﷺ) "Wanda ya karanta Alqur’ani cikin qasa da kwana uku ba zai fahimce shi ba". Abu Dawud da Tirmizi da Ibn Majah suka rawaito shi daga Ibn Umar (R.A).
Ya ku bayin Allah! A yau Haqiqa mafiya yawan mutane a yau sun shagala daga koyon Alqur’ani. Manya sun shagala da duniya, yara sun shagala da karatun boko a makarantun da ba sa bawa koyar da Alqur’ani isasshan lokaci, ko kulawa da ta kamata, kuma babu malamai da za su xauki alhakin kula da karatunsa. Ragowar lokutan yaran kuwa ana asarar sa ne a wasa, abin da ya haifar da jahiltarsu ga Alqur’ani, da nesantar su daga gare shi. Har ka ga mutum yana xauke da wata babbar shaidar karatu, amma ba zai iya karanta aya xaya ta littafin Allah daidai ba. Har lamarin ya kai ga masallatar dadama sun rasa limamai saboda qarancin makaranta alqur'ani. Dalilin haka, na farko watsi da iyaye suka yi da ‘ya’yansu, da rashin damuwarsu da wannan vangare. Xayansu bai san menene halin xansa yake ciki ba dangane da Alqur’ani ba. Har musulmi dadama suka qauracewa Alqur'ani. Wannan shi ne abin da Manzo (ﷺ) ya kai kokensa, da faxinsa:
(وَقَالَ الرَّسُولُ يَا رَبِّ إِنَّ قَوْمِي اتَّخَذُوا هَذَا الْقُرْآَنَ مَهْجُورًا30) [الفرقان: 30]
(Ya Ubangiji haqiqa mutane na sun riqi wannan Alqur’ani a matsayin abin qauracewa).
Ibn Kasir – Allah ya jiqansa – ya ce, barin bibiyar ma’anarsa da fahimtarsa yana daga qaurace masa. Barin aiki da shi, da kamanta umarce-umarcensa, da nisantar hane-hanensa yana daga nisantar sa, karkata daga gare shi zuwa waninsa na daga waqa ko magana ko wasa ko wani zance ko wata xariqa wacce ba ta Alqur’ani ba, yana daga cikin qaurace masa.
Ya ku bayin Allah! Haqiqa dole ne a koyi Alqur’ani daga Malamai da suka iya karanta shi. Mutum ba zai wadatu da tashin baqinsa daga cikin Mushafi ba, domin koyar Alqur’ani daga bakin mai koyarwa qwararre shi ya fi kyau, ya fi tabbatar da kiyayewa; domin ba za a iya koyansa ta hanyar karatun rubutunsa ba, sabonda kamar yadda kowa kan iya gani, mutane dadama daga waxanda suka koyi alqur’ani ta hanyar karanta shi ba tare da malami ba, sukan yi ta tabka kurakurai wajen karanta shi. Saboda haka dole ne ya sami malami da ya qware da zai nuna masa lafazan Alqur’ani. Haqiqa tsangayoyi da makarnatun allo sun yi yawa na koyar da Alqur’ani. Sai dai abin takaici babu mai gudanar da su, face mutanen da suka haddace Alqur’ani babu tantancewa ko tajwidi, ba sa kyautata karatun koda aya xaya karatu ingantacce abin kyautatawa, tare da rashin kulawarsu da tarbiyyar Almajirai da ke hannunsu, da barinsu sasakai kamar tumaki suna yawo a titina, da gidajen mutane, babu isasshan abinci, ba kiwon lafiya, ba makwanci mai kyau, duk wannan da sunan Alqur’ani. Wannan wallahi aiki ne da yake munanawa Alqur’ani, yake munanawa musulunci, ya sanya maqiya Musulunci suna kallan wannan mummunan aiki da ake aikatawa waxannan qananan yara a matsayin vangare na wajban Musulunci, kuma xaya daga abubuwan da ake buqata domin haddace Alqur’ani, alhali musulunci ba ruwansa da duk wannan. Ya wajaba ga Gwamnonin jihohin musulmi su kula da nauyin da ya rataya a wuyansu game da wannan lamari, su kawo mafita ta karshe, su tserar da musulunci da Alqur’ani daga laifin mutane jahilai. Qoqarin da ake yi game da wannan kaxanne idan anyi la’akari da girman matsalar da havakarta. Mafificiyar hanya ita ce wayar da kan Musulmi da iyayan yara, musamman a karkara da qauyuka, da samar da makarantun haddace Alqur’ani isassu waxanda za su ginu a kan tushen shari’ah nagarta.
Ya ku bayin Allah; Wanda ya koyi littafin Allah to ya kiyaye shi, ya yawaita karanta shi da tuntuni a cikins, da fhaimtarsa cikin qasqantar da kai da halarto da zuciya. Manzon Allah (ﷺ) ya ce: (Wanda ya karanta harafi daga littafin Allah yana da ladan kyakkyawan aiki xaya, shi kuwa kyakkywan aiki yana da ladan goma kwatankwacinsa, ba zance Alif-Lam-Mim, harafi xaya ne. Sai dai Alif harafi ne – Lam harafi ne, Mim harafi ne). Tirmizi ne yarawaito kuma ya ce hadisi ne ingantacce.
Ibnul Qaiyim – Allah ya ji qansa – ya ce, “Ka lura da zancan Alqur’ani kaga wani sarki wanda mulki duk nasa ne, ya bo duka nasa ne, ragamomin lamurra a hannunsa suke duka, yana yiwa bayinsa nasiha, ya shiryar da su a bisa abin da farin cikinsu da rabautar su ke ciki, yake qwaxaitar da su cikinsa, yana gargaxinsu daga abin da hallakarsu ke ciki. Yana sanar musu da kansa da sunayansa da siffofinsa. Ya soyu zuwa gare su da ni’imominsa da falalolinsu. Ya tuna musu da ni’imominsa akansu, ya umarce su da yin abin da za su cancanci cikamakinta da su. Ya tuna musu da abin da ya tanadar musu na karama in sun bi shi, da abin da ya tanadar musu na uquba in sun save shi. Ya ba su labarin yadda yake yi da masoyansa da maqiyansa, da ya ya qarshan waxannan da waxancan. Ya buga misalai, ya nau’anta dalilai da hujjoji. Yana kira zuwa gidan aminci. Ya ambaci siffofinsa da kyawunsa. Yana gargaxi game da gidan hallaka, yana tunatarwa da azabarsa da muninta. Ya tunatar da bayinsa buqatuwarsu zuwa gare shi, kuma cewa su ba za su iya wadatuwa daga barinsa dai dai da qiftawar ido. To idan zukata suka ga sarki mai girma, mai rahama, mai kyauta, mai kyawu, a cikin Alqur’ani don me ba za su so shi ba?
Shi Alqur’ani mai tunatawa mutane Allah ne, mai kusantarwa zuwa gare shi ne, don haka ya wajaba musulmi ya kula da koyansa da yawaita karanta shi, domin shi haske ne da waraka da rahama, da ni’ima, da shiriya, da banbancewa tsakanin gaskiya da qarya, da ambato mai hikima da dalili.