Maanar ibada a musulunci


11210
Surantawa
Haqiqa maanar ibada a addinin musulunci maana ce da ta game dukkan abubuwan alherin duniya da lahira, domin haqiqanin ibada, suna ne da ya hada dukkan wasu maganganu ko ayyuka wadanda Allah ke sonsu kuma ya yarda dasu. Shi musulmi yana da yaqini a wannan gida na duniya cewa shi bawa ne na Allah haqiqanin bauta, don haka ne ma yake tashi tsaye domin ya tabbatar da samuwar wannan bauta domin ya kasance cikakken bawa na ubangijin sa; domin girman bawa da falalar sa ,suna tabbata ne idan ya kasance bawa na gari,yana me misalta umarnin Allah, me nisantar haninsa a dukkan alamuran sa na addini da rayuwa.

Manufofin huxubar

Bayanin manufar samar da halittu.

Bayanin gamammiyar ma’anar ibada a musulmi.

Bayanin cewa, ibada kala-kala ce a musulunci.

Bayyanin cewe, kyautata niyya game da abubuwan da suke halal ne yana mayar da su ibada.

Huxuba Ta Farko

Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma mua neman tsarinsa daga sharrin kawukanmu da munanan aiyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar dashi, wanda kuma ya atar babu mai shiryar da shi, kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai allah, shi kaxai ne bashi da abokin taraiya, kuma ina shaidawa cewa Annabi Muhammad bawansane manzonsane, (Yaku waxanda kuka bada gaskiya kuji tsoron Allah yadda ya cancanta aji tsoronsa, kada ku mutu face kuna Musulmi). (Yaku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicce ku daga rai guda xaya kuma ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga gare su (su biyu) kuji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya dashi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Ya ku waxanda suka yi imani kuji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku aiyukanku, kuma ya gafarta muku zunubanku. Wanda ya bi Allah da manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawun shiriya shiriyar Annabi Muhammadu (ﷺ) kuma mafi sharrin al’amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wata bidi’a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta.

Ya ku bayin Allah! Haqiqa Allah mai girma da buwaya bai halicci halittu dan wasa ba, kuma bai bar su sasakai ba. Allah ya halicce su ne don wata hikima mai girma. Allah mabuwayi da xaukaka, yana cewa:

(وَمَا خَلَقْنَا السَّمَاءَ وَالْأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا بَاطِلًا ذَلِكَ ظَنُّ الَّذِينَ كَفَرُوا فَوَيْلٌ لِلَّذِينَ كَفَرُوا مِنَ النَّار27)ِ [ص: 27]

(Kuma ba mu halicci sama da qasa da abin da ke cikinsu a banza ba, wannan shi ne zaton waxanda suka kafirce, to bone ya tabbata ga waxanda suka kafice na azabar wuta).

Allah mabuwayi ya ce:

(وَمَا خَلَقْنَا السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا لَاعِبِينَ38مَا خَلَقْنَاهُمَا إِلَّا بِالْحَقِّ وَلَكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لَا يَعْلَمُونَ39) [الدخان: ٣٨ – ٣٩].

(Kuma ba mu halicci sammai da qasa da abin da yake cikinsu muna masu wasa ba, ba mu halicce ba sai da gaskiya, sai dai yawancinsu ba su sani ba).

Allah Ta’ala ya bayyana wannan haqqin wanda don shi ne ya halicci halitta sai ya ce:

(وَمَا خَلَقْتُ الْجِنَّ وَالْإِنْسَ إِلَّا لِيَعْبُدُونِ56 مَا أُرِيدُ مِنْهُمْ مِنْ رِزْقٍ وَمَا أُرِيدُ أَنْ يُطْعِمُونِ 57)[الذاريات: ٥٦ – ٥٧].

(Kuma ban halicci aljanu da mutane ba, sai don su bauta min. Ba na neman wani arzuqi a wajensu, kuma ba neman su ciyar da ni).

Don haka hikimar da ta sa ya halicci halittarsa, shi ne, ya umarce su da bauta masa, kuma su tsaya a kan aiki da abin da ya wajabta musu. Ya aiko manzanni masu bshara da gargaxi don su sanar da halittu Ubangijinsu, su bayyana musu manufar da aka halicce su don ita, daga cikinsu akwai wanda ya karvi shiriya, da kuma wanda ya mayar, hujjar Allah mai tsayuwa ce a kan bayi.

Ya kai musulmi, ka lura da faxin Allah Ta’ala;

(وَمَا خَلَقْتُ الْجِنَّ وَالْإِنْسَ إِلَّا لِيَعْبُدُونِ) [الذاريات: 56]

(Kuma ban halicci aljanu da mutane ba sai don su bauta min).

Da faxinSa:

(وَاعْبُدُوا اللَّهَ وَلَا تُشْرِكُوا بِهِ شَيْئًا36) [النساء: ٣٦].

(Ku bautawa Allah, kuma kada ku tara bautarsa da wani abu).

Ya ku bayin Allah! Ibada tana da ma’ana gamammiya, asalin wannan ibadar shi ne tsarkake addni ga Allah. Ka kaxaita Allah da dukkan nau’in bauta, ka fuskanta zuwa ga Allah da zuciyarka da so da tsoro da fata. Hakan nan kowace ibada ka yi ta ga Allah. Sallarka ga Allah, addu’arka ga Allah, matsuwarka ga Allah, tsoronka na gaskiya ga Allah, cikar fata da amincewa ga Allah, babu girmama wanin Allah a zuciyarka. Girmamawa ta gaskiya ga Allah shi kaxai take.

(Wannan saboda cewa Allah shi ne gaskiya, kuma abin da suke kira ba shi ba qarya ne).

Ya kai musulmi, haqiqa ma’anar ibada a shar’ar musulunci ma’ana ce ta gabaxaya, gamammiya ga duk wani alheri daga lamarin addini a duniya da lahira. Haqiqa ibada, suna ne da ya tattare dukkanin maganganu da ayyukan da Allah yake so, kuma ya yarda da su. Musulmi a wannan duniyar ya san cewa shi bawa ne na Allah da bauta ta haqiqa, don haka shi yana aiki ne tuquru don tabbatar da wannan bautar, ba don komai ba sai don ya zama bawan Ubangijinsa na gaskiya. Domin duk wata darajarsa da falalarsa shi ne kasancewarsa bawan Allah na gaskiya. Yana aiwatar da umarce-umarcensa, yana nisantar hane-hanensa, yana tsaye wajen iyakokinsa, yana zartar da farillansa.

Ya kai musulmi, yana daga rahamar Allah da falalarsa a gare mu cewa, ya sanya ibadu nau’i-nau’i. Akwai ibadu na zuciya, su ne, wanda bawa yake yin su da zuciya, kamar ikhlasi da nufatar Allah da dukkan nau’in ibada. Akwai kuma ibada ta jiki, kamar waxannan salloli guda biyar da musulmi yake yinsu a kowace rana da yini. Haka kuma akwai ibadar da ta shafi kuxi, kamar zakka da musulmi yake fitarwa don imani da neman yardar Allah, yana kuma mai qara neman kusanci ga Ubangijinsa. Akwai ibadar da bawa yake hana zuciyar bin sonye-soyenta, don biyayya ga Allah kamar yadda yake a a zumi. Akwai ibada da jiki da dukiya gabaxaya kamar Hajji, domin shi ya haxa da dukiya da jiki da jihadi a tafarkin Allah shi ne mafi falala da girma.

Sannan Allah Ta’ala ya yi mana falala ya shar’anta mana nafiloli a cikin sallah da nafiloli a sadaka da nifiloli a azumin da nafiloli a hajji da umara, duk wannan don qarfafa imaninmu da xaukaka darajarmu da qarin kyawawan ayyukanmu. Don haka yana da falala da baiwa a gare mu ba ma qididdige yabo a gare shi kamar yadda shi ya yabi kansa.

Ya ‘yan’uwana a musulunci! Haqiqa shari’ar musulunci ta zo cikakkiya, gamammiya, ba ta xaukar qari ko ragi, Allah Ta’ala ya ce:

(الْيَوْمَ أَكْمَلْتُ لَكُمْ دِينَكُمْ3) [المائدة: ٣].

(A yau ne na cika muku addininku...)

Allah ya sanya sharuxa guda biyu, masu girma don karvar aiki, idan an rasa xaya daga cikinsu to aiki ya vaci, ya zama rusasshe, abin watsarwa.

Na farko: Shi ne aikin ya zamo tsarkakakke don zatin Allah shi kaxai, babu riya ba yi don a ji.

Na biyu: Shi ne ya zama daidai ne, ya dace da shari’ar Allah, da sunnar manzon Allah (ﷺ), ba qari ko bidi’a, domin Annabinmu Muhammad (ﷺ), ya isar da bayyanannen saqo, bai bar wani abu na addin ba face sai da ya bayyana su, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Gaskiya ita ce abin da ya zo da shi.

Ya kai musulmi, ba ya ga haka, ka sani cewa; gaskiya ne duk kai-kawonka a cikin rayuwarka idan ka nufi zatin Allah da shi, duk maganganunka da ayyukanka idan nufi kusantar Allah da su, za su zama ibada ce ga Allah.

Musulmi yana bautawa Allah ta hanyar biyayya ga iyayensa da kyautata musu, domin an karvo daga Abdullahi xan Amru xan Ass (R.A), ya ce, wani mutum ya zo wajen Annabi (ﷺ), sai ya nemi izininsa don yin jihadi, sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: "Shin mahaifanka suna da rai?" Sai mutumin ya ce, E. Sai ya ce, "Je ka ka yi jihadi ta hanyar yin biyayya a gare su". Bukhari da Muslim da Nasa’i da Abu Dawud da Tirmizi ne suka rawaito.

Ya kai musulmi, sada zumuncinka, ibada ce ga Allah, domin kana sauke wani wajibi ne da Allah ya wajabta maka, domin yana cewa:

(وَاتَّقُوا اللَّهَ الَّذِي تَسَاءَلُونَ بِهِ وَالْأَرْحَامَ1) [النساء: ١].

(Kuma ku ji tsoron Allah wanda kuke magiya da shi kuma ku ji tsoron (yanke) zumunta).

Ya kai musulmi! Ciyarwarka ga ‘ya’yanka ibada ce ga Allah. Annabi (ﷺ) yana cewa Sa’ad xan Abu Waqqas: “Haqiqa ba za ka ciyar da wata ciyarwa ba kana nufin zatin Allah da ita, face an ba ka lada a kanta, har abin da kake sanyawa a bakin matarka”. Bukhari da Muslim ne suka rawaito.

‘Ya’yanka maza da mata tarbiyyarsu da saita su bisa kan tafarki madaidaici da tsayuwa da haka bauta ne ga Allah. Domin Allah yana cewa,

(يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا قُوا أَنْفُسَكُمْ وَأَهْلِيكُمْ نَارًا6) [التحريم: 6]

(Ya ku waxanda suka yi imani, ku kare kanku da iyalanku daga shiga wuta).

Ya kai musulmi! Cinikinka, da kai-kawonka wajen saye da sayarwa, da gwagwarmayarka wajen kasuwanci, idan ka nufi bauta ga Allah da amfanar da al’umma da shi, za a ba ka ladan kyakkyawar niyyarka.

Aurenka kana mai nufin kame kanka, da katange farjinka, da runtse ganinka, ibada ce ga Allah, kuma xa’ar da kake neman kusancin Allah da ita.

Bautarmu ga Allah ba ta taqaita a kan rukunai kaxai ba. A’a ta qunshi xaukacin aikata wajibai da nisantar abubuwan da aka haramta.

Ya xan’uwana musulmi, yayin da ka kaucewa qasqantattun halaye da ayyukan haram, domin biyayya ga Allah, ka sani cewa wannan ibada ce ga Allah kake yi. Don haka Xalq bn Habib ya fassara haqiqanin tsoron Allah da cewa, “Ka yi aiki da biyayyar Allah, a bisa haske daga Allah, kana mai neman lada a gurin Allah, kuma ka bar savon Allah, a bisa haske daga Allah, kana tsoron uqubar Allah.

Ibn Mubarak ne ya ruwaito shi a cikin littafin az-Zuhud.

Musulmi mai gaskiya a cikin sayensa da sayarwarsa, ba ya qarya ba ya ha’inci ba ya yaudara, wannan ma ibada ce ga Allah. Sulhunta tsakanin masu husuma biyu ibada ce ga Allah. Yaye baqin cikin masu baqin ciki da damuwar masu damuwa da quncin masu qunci duka ibada ne ga Allah maxaukakin sarki.

Don haka maganganunsa da ayyukansa, idan niyyarsa ta kyautatu ta tsarkaka ga Allah a cikin duk halayensa, ya zama mai bauta da biyyaya ga Ubangijinsa.

Haka shari’ar musulunci, ke kiran musulmi zuwa alheri. Allah mai buwaya da xaukaka ya yawaita hanyoyin alheri, duk wannan domin qarin lada da xaukaka darajoji da kankare zunubai.

Ya kai xau’uwana musulmi, ka qarfafa amincewarka da Ubangijinka, ka yi aiki don lahirarka, ka tsaya qyam kan biyayya, ka halarto da niyyarka, ka tsaya kan gaskiya a cikin duk wata kyakkyawar magana, ko kyakkyawan aiki, domin ka zama mai bauta ga Ubangijika mai ba da haqqin bautar.

Ya kai musulmi! Haqiqa faxi-tashin musulmi don wata maslaha ta al’umma ibada ce ga Allah. Musulmi idan ya yi qoqari wajen amfanar da jama’a, ya zama mai bautar Allah. Bukhari da Muslim sun ruwaito hadisi daga Anas xan Malik, ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Babu wani musulmi da zai shuka wata shuka, wani mutum ko tsuntsu ya ci daga gare ta, face ya sami lada”. Wannan duk domin kwaxaitar da musulmi wajen rungumar ayyukan al’umma.

Kawar da abin da zai cutar daga kan hanya sadaka ne, kuma ibada ne. Kai duk wani ilimi da bawa zai koye shi, idan ya nufi amfanar al’umma da shi tare da maslaharsa ta duniya, kuma ya nufi zatin Allah da shi, to Allah zai ba shi ladan niyyarsa, domin kowane mutum zai sami sakamakon niyyarsa ne. Wannan kuwa yana cikin falalar Allah da karamcinsa da kyautatawarsa gare mu.

Ya kai musulmi! Don haka ka tsaya kan biyayya, ka dage a kan ibada, kuma ka kiyayi qosawa da sarewa. Allah yana cewa,

(وَاعْبُدْ رَبَّكَ حَتَّى يَأْتِيَكَ الْيَقِينُ99) [الحجر: 99]

(Kuma ka bautawa Allah Ubangiji har mutuwa ta riske ka).

Kada ya zama himmarka ka gama ibada, ko ibada ta qare, ka damu da kyautatata da tsayawa da haqqoqinta, ka aiwatar da ibada da daxin zuciya, da yalwar qirji, da farin ciki.

Ya kai musulmi! Haqiqa Annabinmu yana cewa Bilal “Ka kwantar mana da hankali da sallah”. Ahmad ne ya rawaito shi. Kuma yana cewa: “Kuma an sanya farin cikina a cikin sallah”. Nasa’i ne ya rawaito daga Anas (R.A).

Ya kai musulmi! Don haka ne Annabi ya hana musulmi, tsaurarawa da wuce iyaka a cikin addinisu, ya kuma hana su bautar da za su qosa su gaji da ita. Yayin da labari ya iske shi (ﷺ), game da Abdullahi xan Amru xan Ass (R.A), dangane da ibadarsa mai yawa, da daddare sallah, da rana tilawa, da azumi da ibada, matarsa ta kai qara wajen Manzon Allah, kan cewa mijinta ga irin abin da yake yi wanda yake damunta; ta ce shi bai tava yaye mana lulluvi ba. Idan dare ya yi, sai ya qare shi a salla da karatun Alqur’ani. Idan rana ce kuwa sai ya zarce da azumi, ya ci gaba yana azumtar kwanaki dukkansu. Yana qiyamullaili a dukkanin darare. Sai Annabi (ﷺ), ya kira shi ya ce da shi: “Ba an ba ni labarin cewar kana tsayuwar dare (dukkansa) ba, kuma kana azumtar yini ba?” Sai ya ce; Haka ne. Sai manzo (ﷺ), ya ce masa “Ya Abdullahi xan Amr, haqiqa Ubangijinka yana da haqqi a kanka, jikinka ma yana da haqqqi a kanka, iyalinka ma na da haqqi a kanka. Ya Abdullahi ka azumci kwana uku daga kowane wata”, Sai ya ce; Ni zan iya fiye da haka. Annabi bai gushe da shi ba, har sai da ya sanya azuminsa kwana xaya, shan sa kwana xaya. Ya ce; “Wannan shi ne azumin Annabi Dawud, babu fiye da azumin Annabi Dawud". Ya Abdullahi ka yi bacci rabin dare, ka yi sallah sulusinsa, asannan ka yi barci (a karo na biyu), sudusinsa”. Sannan ya ce da shi: “Ka sauke Alqur’ani a kowane wata sau xaya” Bai gushe da shi ba, har ya sanya shi yana sauke shi a kowanne kwana uku.

Abdullahi xan Amr ya bi wannan hanya, kuma ya lazimci wannan ladabi. Annabi ya ba shi labarin cewa yana kusa da ya wahala, shekaru kuwa ba su shuxe ba, har sai da Abdullahi ya kasa yin wannan aiki. Sai ya kasance yana haxa kwanaki yana azumtarsu, sannan sai ya sha azumi a kwanaki kwatankwacinsu. Yana cewa; ina ma na karvi rangwamen Annabinku (ﷺ). Bukhari ne ya fitar da shi a cikin azumi da muslim ma a babin azumi.

A’isha (R.A) tana cewa: “Annabi (ﷺ) ya kasance yana azumi har mu ce ba zai sha ba, kuma yana sha, har mu ce ba zai yi azumi ba". Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.

Wasu malamai suka ce, wannan ya yi ne don shi yana lura da maslahohi, yana gabarat da waxanda suka fi falala, a bisa koma bayansu. Idan akwai wasu al'amuran a cikin al’umma, sai ya jinkirta azumin don biyan buqatar musumi, idan kuwa ba lokacin wannan ba ne, sai ya yi.

Kuma ya ce, “Wanda ya yi azumin shekara ba shi da ladan azumi”.

Ya kai musulmi! Don haka bidi’o’i da qari a cikin lamura ba tare da umarnin shari’a ba dukkninsu babu alheri a cikinsu. A lazimci hanya miqaqqiya, wadda babu shisshigi da sakaci a cikinta.

Kuma Annbi (ﷺ) yana cewa, “Haqiqa mafi soyuwar ayyuka a wajen Allah shi ne wanda mai yinsa ya dauwama a kansa, koda kaxan ne”. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi, daga A’isha (R.A).

Don haka aiki kaxan da za ka lazimce shi, ka aiwatar da shi da kyau shi ya fi alheri fiye da aiki da yawa da za ka yi shi yau, sannan ka watsar da shi kwanaki. Kasancewar musulmi yana da ibadu kala-kala, an ba shi damar ya xauki abin da zai iya a kowanne nau’i. Wannan shi ake nema daga musulmi don ya kasance a cikin azumisa mai qaqqarfar alaqa ne da Ubangijinsa, da kuma addininsa, sannan da Annabinsa.

Ina roqon Allah dacewa da shiriya zuwa kowane alheri, ga kaina da ku, shi mai iko ne a bisa kowane abu.

Allah ya yi min albarka tare da ku, a cikin alqur’ani mai gima, kuma ya amfanar da ni da ku da abin da ke cikinsa, na ayoyi da wa'azi mai hikima. Abin da zan iya faxa ke nan, kuma ina nemman gafarar Allah mai girma ga kaina da ku, da sauran musulmi daga kowane zunubi, ku nemi gafararsa, ku tuba zuwa gare shi, lallai shi mai gafara ne mai jinqai.

Huxuba Ta Biyu

Godiya ta tabbata ga Ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su tabbata ga mafi darajar halitta wanda aka aiko shi don ya zama jinqai ga talikai, da alayensa da sahabbansa da waxanda suka tafi a bisa tafarkinsa har zuwa ranar sakamako, bayan haka:

Ya ku bayin Allah! Ibada ni’ima ce da ba mai jin (xanxanonta), sai wanda ya rasa ta. Ku tambayin ‘yan duniya, ku tambayin waxanda suka xanxani abubuwar more rayuwa ta duniya, suka hau abin da suke so, su sa tufafin da suka ga dama. Suka more da duk wani abu na rayuwa, kamar yadda Allah Ta’ala Ya ce:

(وَالَّذِينَ كَفَرُوا يَتَمَتَّعُونَ وَيَأْكُلُونَ كَمَا تَأْكُلُ الْأَنْعَامُ وَالنَّارُ مَثْوًى لَهُمْ12) [محمد: 12]

(Su kuwa waxanda suka kafirce, suna morewa, kuma suna ci kamar yadda dabbobi suke ci, kuma wuta ce makomarsu).

Sai kuma me? Idan imani bai zauna a qoqoan zuciyar su ba? Idan kuma ba su san darajar imani da bauta ga Allah sarki xaya ba? Idan ba su sami alaqa tsakaninsu da Allah mabuwayi mai xaukaka ba? Ba su sami ganawa da shi ba a kowane yini da dare sau biyar. Haqiqa abin da wannan yake nufi shi ne rushewar rayuwa ta haqiqa, rushewar rayuwar ruhi, rayuwar tunani da imani, da rayuwar aqida.

Wai shin menene mutum, idan ba tare da imani ba? Su wanene mutane ba tare da aqida ba? Su wanene mutane ba tare da bautawa Allah ba? Dabbobin daji ne a daji, ko dabbobin gida ne a garke. Amma idan suka zamo muminai masu tauhidi na gaskiya suka ado da imani, suna lazimtar koyarwa ta musulunci, suna xabbaqa mafi girman tsari da ‘yan’adam suka tava sani a tarihinsu, kuma ba za su san kamar sa ba har zuwa tashin alqiyama.

Ya ku bayin Allah! Haqiqa da yawan mutane yau sun munana fahimmta ma’anar ibada, sun taqaice ta - don jahilcinsu da vatansu - a kan wani adadi na ayukan bauta. Suka jahilci manufofinata da abubuwan da ta qunsa., Ta hanyar bayanin gamammiyar ma’anarta za mu fahimci yadda wasu suka kauce hanya wajen fahimtar haqiqanin abin da ake nufi da ibada. A nan za mu iya kasa su gida uku:

Nau’i na farko: Wanda ya yi wa ibada quntatacciyar fahimta, ya zaci cewa ita ibada ba ta wuce wasu ayyuka na ibada da aka sani ba, kamar sallah da azumi da zakka da umara da hajji. Idan yana masallaci to shi mai bauta ne ga Ubangijinsa, idan ya fita daga masallaci sai ya yi mu’amala da riba, ya rungumi zina, ya sha giya, ya savawa iyaye, ya munana zama da abokansa a wajen aiki, da xungushe a gurin aiki, za ka ga matarsa da ‘ya’yayensa mata suna shiga ta fitsara. A masallaci yana tare da Allah, da wata fuska, a wajen masallaci kuma yana tare da Allah da mutane da wata fuskar ta daban. Yana bin umarnin Allah a suratul Baqara:

(يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا كُتِبَ عَلَيْكُمُ الصِّيَامُ183) [البقرة: 183]

(Ya ku waxana suka imani, an wajabta muku azumi).

Amma ba ya bin umarnin Allah, da ya zo a cikin ita dai wannan surar, inda Allah yake cewa:

(يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا كُتِبَ عَلَيْكُمُ الْقِصَاصُ فِي الْقَتْلَى178) [البقرة: 178]

(Ya ku waxanda suka yi imani an wajabta muku qisasi game da waxanda aka kashe).

Yana bin umarnin Allah a cikin Suratul Ma’idah:

(يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا إِذَا قُمْتُمْ إِلَى الصَّلَاةِ فَاغْسِلُوا وُجُوهَكُمْ وَأَيْدِيَكُمْ إِلَى الْمَرَافِقِ وَامْسَحُوا بِرُءُوسِكُمْ وَأَرْجُلَكُمْ إِلَى الْكَعْبَيْنِ6) [المائدة: 6]

(Ya ku waxana kuka ba da gaskiya idan kun tashi zuwa sallah to ku wanke fuskokinku, da hannayenku zuwa gwiwoyin hannu, ku shafi kawunanku da (wanke) qafarku zuwa idanun sawu biyu).

Amma ya tozarta umarnin Allah na cikin Suratul Ma’idah, xin kanta:

وَمَنْ لَمْ يَحْكُمْ بِمَا أَنْزَلَ اللَّهُ فَأُولَئِكَ هُمُ الْكَافِرُونَ44) [المائدة: 44]) (Duk wanda bai yi hukunci da abin da Allah ya saukar ba, to waxannan su ne kafirai).

Wannan gurguwar fahimta ce tauyayyiya. Allah mai girma da xaukaka yana cewa:

(أَفَتُؤْمِنُونَ بِبَعْضِ الْكِتَابِ وَتَكْفُرُونَ بِبَعْضٍ فَمَا جَزَاءُ مَنْ يَفْعَلُ ذَلِكَ مِنْكُمْ إِلَّا خِزْيٌ فِي الْحَيَاةِ الدُّنْيَا وَيَوْمَ الْقِيَامَةِ يُرَدُّونَ إِلَى أَشَدِّ الْعَذَابِ وَمَا اللَّهُ بِغَافِلٍ عَمَّا تَعْمَلُونَ85) [البقرة: 85]

(Yanzu kuna imani da sashin littafi kuma ku kafirce da sashi, to ba komai ne sakamakon wanda yake aikata haka daga cikinku ba, face tozarata cikin rayuwar duniya, kuma a ranar alqiyama za a mai da su zuwa mafi tsananin azaba, kuma Allah ba mai gafala ba ne a bisa abin da kuke aikatawa).

Lallai wannan tawaye ce a cikin fahimtar ma’anar ibada.

Nau’i na biyu: Ya karkatar da ibada ga wanin Allah Mai buwaya da xaukaka. Ya miqa wuya ga wata shari’a ba ta Allah. Yana yanka ga wanin Allah, yana rantsuwa da wanin Allah, yana xawafi ba a xakin Allah, don girmama wanin Allah, yana gabatar da bakance ga wanin Allah, yana neman taimakkon wanin Allah. Yana neman agajin wanin Allah, yana fakewa ga wanin Allah, yana fawwala lamarinsa zuwa wanin Allah, yana dogara ga wanin Allah, yana amincewa da wasu qasashen duniya da al’ummar qasar fiye da amincewarsa da mahaliccin sama da qasa. Daga cikinsu akwai wanda ya ce: Idan lamurra suka wuyata a gare ku, to ku bazama zuwa mutanen cikin qabari! Daga cikinsu akwai wanda yake cewa: Shi ya qudurce cewa duniya tana da waliyyai quxubai da waliyyai watadai, da abdalu, da suke sarrafa tsarin duniya, suke tafiyar da lamurranta!! Alhali Allah mai buwaya da xaukaka yana cewa:

(قُلْ إِنَّ الْأَمْرَ كُلَّهُ لِلَّهِ154) [آل عمران: ١٥٤].

(Ka ce, lalle al’amari dukkaninsa na Allah ne).

Daga cikisu akwai wanda yake cewa: Lallai mu muna bikin tuna ranar haihuwar Sayyid Badawi abin tsoro, wanda in an kira shi zai amsa a kan tudu ne ko a cikin kogi. Allah mai buwaya da xaukaka yana cewa:

(أَمَّنْ يُجِيبُ الْمُضْطَرَّ إِذَا دَعَاهُ وَيَكْشِفُ السُّوءَ وَيَجْعَلُكُمْ خُلَفَاءَ الْأَرْضِ أَئِلَهٌ مَعَ اللَّهِ قَلِيلًا مَا تَذَكَّرُونَ62) [النمل: 62]

(Wane ne wanda yake amsawa mai tsananin buqata idan ya kira shi? Kuma yake yaye masifa, kuma yake sanya ku masu mayewa a bayan qasa? A yanzu akwai wani Ubangiji ba Allah ba? Kaxan ne qwarai kuke wa’azantuwa).

Kuma Allah mabuwayi da xaukaka yana cewa:

(وَإِنْ يَمْسَسْكَ اللَّهُ بِضُرٍّ فَلَا كَاشِفَ لَهُ إِلَّا هُوَ وَإِنْ يَمْسَسْكَ بِخَيْرٍ فَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِير17) [الأنعام: 17] (Idan Allah ya same ka da cuta babu mai yaye ta sai shi, idan ya same ka da alheri shi mai iko ne a bisa kowane abu).

Nau’i na uku: Wanda ya sarrafar da ibada ga Allah, yana neman yardarsa da ita, ba ma kokwnato a cikin ikhlasinsa. Sai dai shi ya yi ibada ba a bisa shiriyar Al-mustafa ba, kuma ba a kan sunna ba. Ibadarsa a bar mayar masa ce. Ba za ta karvu ba wajen Allah mai buwaya da xaukaka, Allah Ta’ala ya ce:

(فَمَنْ كَانَ يَرْجُوا لِقَاءَ رَبِّهِ فَلْيَعْمَلْ عَمَلًا صَالِحًا وَلَا يُشْرِكْ بِعِبَادَةِ رَبِّهِ أَحَدًا110) [الكهف١١٠].

(To wanda ya kasance yana fatan gamuwa da Ubangijinsa, to ya aikata aiki na gari, kuma kada ya tara bautar Ubangijinsa da wani).

Bukhari da Muslim sun ruwaito hadisi daga A’isha tana cewa, lallai Annabi (ﷺ) ya ce: “Wanda ya farar da wani abu a cikin lamarinmu wannan (addininmu), abin da ba ya cikinsa to shi abin mayarwa ne gare shi.”

Za a mayar da shi, Allah ba zai karve shi ba. Shin wanda ya qara wani abu a cikin addinin Allah, ya farar da wani sabon abu da Allah bai yi izini da shi ba a cikin shari'ar Allah, shin wannan ya bautawa Allah haqiqatan?

Ya ku musulmi! Matuqa a cikin bautar bawa ga Ubangijinsa shi ne har zuwa mutuwa, faxin Allah Ta’ala ya bayyana haka qarara inda ya ce,

ﭽ ﮂ ﮃ ﮄ ﮅ ﮆ ﮇ ﭼ [الحجر: ٩٩].

(Ka bautawa Ubangijinka har mutuwa ta zo maka).

Wannan yana bayyana cewa bautar mutum ga Allah da tsayawara da wajibansa, ba a iyakance shi da wata iyaka, ba ya da qarshe sai mutuwa, sai lokacin barin wannan rayuwa. Ita kuwa mutuwa ita ce, wannan abu na gaske, mai xaci mai wahala wanda ita bisa haqiqa, take da nauyi a zukatan mutane ba su sonta a bisa xabi’arsu, Allah Ta’ala Yana cewa:

(كُلُّ نَفْسٍ ذَائِقَةُ الْمَوْتِ185) [آل عمران: ١٨٥].

“Kowace rai mai xanxan mutuwa ce”

A’uzu billahi minasshaixanir-rajim:

(إِنَّ الَّذِينَ قَالُوا رَبُّنَا اللَّهُ ثُمَّ اسْتَقَامُوا تَتَنَزَّلُ عَلَيْهِمُ الْمَلَائِكَةُ أَلَّا تَخَافُوا وَلَا تَحْزَنُوا وَأَبْشِرُوا بِالْجَنَّةِ الَّتِي كُنْتُمْ تُوعَدُونَ30 نَحْنُ أَوْلِيَاؤُكُمْ فِي الْحَيَاةِ الدُّنْيَا وَفِي الْآَخِرَةِ وَلَكُمْ فِيهَا مَا تَشْتَهِي أَنْفُسُكُمْ وَلَكُمْ فِيهَا مَا تَدَّعُونَ31 نُزُلًا مِنْ غَفُورٍ رَحِيمٍ32) [فصلت: ٣٠ – ٣٢].

“Haqiqa waxanda suka ce, Ubangijinmu shi ne Allah. Sannan suka tsaya a kan tafarki, mala’iku suna sauka a gare su (yayin mutuwa suna cewa); kada ku ji tsoro, kuma kada ku yi baqin ciki kuma ku yi bushara da aljannan nan da ake muku bushara da ita. Haqiqa mu ne majivintarku a cikin rayuwar duniya da lahira, kuma ku kuna da abin da zukatanku suke sha’awa a cikinta, kuma kuna da abin da kuke kira. Saukar baqi ne daga Allah mai gafara mai jin qai.”





Tags:




Yasir Al-qurashy