Muhimmancin salla da hikimar sharanta ta


5931
Surantawa
Salla itace ginshikin addini kuma mafi girman rukuni bayan kalmar shahada,kuma itace abin da za a fara wa bawa sakamako a kanshi ranar tashin kiyama , kuma itace wasiyyar karshe da manzon Allah s.a.w yayi wa alumar sa kafin rasuwar sa, kai saboda girman ta ma sahabbai sun kasance suna kirga wanda baya halartar salla tare da jamaa cikin munafukai. Abu mafi girma dake nuna muhimmancin sallah shine yanda aka farlanta ta tun daga saman bakwai ba tare da wani shamaki ba.

Manufofin huxubar

Bayanin wajabcin kiyaye sallah da yadda ake yin hakan

Bayanin Muhimmancin Sallah da Matsayinta a Musulunci

Bayani a kan cewa Sallah alaqa ce mai maimaituwa tsakanin bawa da Ubangijinsa

Bayani kan tasirin Sallah bisa zuciya da gavvai

Huxuba Ta Farko

Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma muna neman tsarinsa daga shirrin kawukanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar da shi, wanda kuma ya vatar to babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaxai ne ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi Muhammad bawansa ne manzonsa ne. (Ya ku waxanda suka yi imani ku ji tsoron yadda ya cancaci a ji tsoronsa, kada ku mutu face kuna musulmi). (Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicceku daga rai guda xaya, kuma ya ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga garesu (su biyu). Ku ji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya da shi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Ya ku wanxanda suka yi imani ku ku ji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku ayyukanku, kuma ya gafarta muku zunubbanku. Wanda ya bi Allah da Manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawon shiriya shiriyar Annab Muhammad (ﷺ). Kuma mafi shirrin al'amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wani qagaggen abu (addini) bidi'a ce, duk wata bidi'a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta.

Bayan haka:

Ya ku 'yan uwa musulmi, haqiqa xan adam rarrauna ne ba ya da qarfi sai lokacin da yake tare da Ubangijinsa, rundunoni na sharri suna fuskantar mutum, fito-na-fito tsakanin ingije sha'awa da kuma ruxi na kwaxayi, yaqar tsaurin kai kan yi masa wahala. kuma daidaitacciyar hanya kan yi masa tsawo, kuma zango kan yi masa nisa, kuma ba shi da wata mafaka daga waxannan igiyoyin ruwa masu awon qoqarin awon gaba da shi face riqo da Allah, da fakewa da shi.

Ya ku musulmi, haqiqa dacewa da wannan lokaci mai daraja da Musulmi suke ciki a wannan kwanaki ya sanya buqatar yin bayani game da mafi muhimmancun ibada a musulunci, kuma mafi girmanta wajan kusanci da Allah mai maxaukakin sarki. wannan kuwa ita ce ibadar da Annabinmu Muhammadu kan fake zuwa gare ta yayin da wani lamari ya tsananta gare shi. Maganarmu a yau za ta kasance ne game da rukuni na biyu daga rukunan musulunci, kuma jigonsa wanda wannan addinin ya ginu a kansa, kuma ita ce farkon abin da Allah ya wajabta a ibadodi, kuma ita ce farkon abin da za a yi wa bawa hisabi a kansa ranar alqiyama, kuma ita ce qarshen wasiyar da Ma'aikin Allah (ﷺ) ya yi wa al'ummarsa wasiyya da shi yayin rabuwarsa da duniya. Inda ya ce a lokacin da zai cika: "Ina jaddada muku lamarin sallah! Ina jaddada muku lamarin sallah da kuma lamarin bayinku". Ahmad Da Abu Dawud da Ibn Majah suka ruwaito shi. Kuma ita ce qarshen abin da za a rasa daga addini; idan ta tozarta to addini gaba xayansa ya tozarta.

Sallah (ita ce ibadar) nan da falalarta ta cika kunnuwan halittu, saboda abin da aka tanadarwa masu kiyayeta. An rawaito daga Abu Umamata Allah ya qara yarda a gare shi, cewa Manzon Allah (ﷺ) ya ce: "Duk wanda ya fita daga gidansa yana mai tsarki zuwa sallar farilla, to zai sami ladan wanda ya yi harama da hajji,wanda kuma yafita zuwa nafilar walha babu abin da ya tashe shi sai ita, to zai sami ladan wanda ya yi umara, kuma salar da aka yi bayan wata sallar, alhali babu yasasshiyar magana tsakaninsu, za a rubuta ta a cikin illiyyuna". Abu Dawud ne ya rawaito shi da isnadi kyakkyawa.

Haka nan Annabi mai (ﷺ) ya ce "Sallah ita ce mafificin abu, don haka duk mai mai son yawaita ta, to sai ya yawaita". Xabarani ne ya rawaito a cikin Al-Ausat, kuma hadisi ne kyakkyawa .

Muhimmancin sallah na qara bayyana ne cikin kasancewarta an saukar da ita daga birbishin sammai bakwai, ba tare da an aiko ta hanyar saqo ba, da kuma kasancewarta mai sadarwa tsakanin bawa da Ubangijinsa. Sallah ta kasance ita ce abin faranta ran masana Allah, kuma hutun zukatansu, ga ta kuma tana hani ga barin alfasha da mummunan aiki. Allah Ta'ala Ya ce:

( إِنَّ الصَّلَاةَ تَنْهَى عَنِ الْفَحْشَاءِ وَالْمُنْكَرِ ) [العنكبوت: 45]

“Haqiqa sallah tana hana alfasha da mummunan aiki”.

Allah mai tsarki da xaukaka Ya yi kira zuwa kiyayeta ya ce:

( حَافِظُوا عَلَى الصَّلَوَاتِ وَالصَّلَاةِ الْوُسْطَى وَقُومُوا لِلَّهِ قَانِتِينَ238 ) [البقرة: 238]

(Ku kiyaye salloli, da kuma sallah ta tsakiya, kuma ku tsaya kuna masu biyayya ga Allah).

Kuma an sanya farin cikin al-Musxafa (ﷺ) a cikinta, domin Anas (R.A.) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce, "An sanya mini qaunar mata da turare, kuma an sanya farin cikina a cikin sallah". Bukhari da waninsa suka rawaito shi.

Kai nutsuwarsa ma (ﷺ) ba ta kasance ba face a cikinta, don haka ita ce matsera idan wani lamari ya tsananta a gare shi, kuma ita ce mafaka idan gajiya ta samu, sai mai tsira da amincin Allah yakan ce: "Ya Bilali tashi ka yi iqamar sallah, ka sama mana hutu da ita)) .

Sasannin mai sallah sun cika da kwarjini, kuyavunsa sun haskaka da hasken imani, annashuwar imani ta cika zuciyarsa, yana tadabburin Alqur'ani a cikin sallarsa, kuma yana xaukaka addu'arsa, kuma yana qaskantar da kai ga Ubangijinsa a cikin ganawarsa, damuwarsa ta tattara ne a kan lamarin Allah, kuma ya samu farincikinsa da (yardar) Ubangijinsa gare shi, dan haka ya kusantar da shi.

Wannan kaxan ne daga cikin girman sallah a cikin wannan addini, kuma wannan xan tsakure ne daga cikin ma'anoninta a zukantan muminai. Sai dai duk da haka za ka ga da yawa daga cikin musulmi suna sakaci cikin ba da wannan farilla ma girma. Suna sallah amma basa kyautata sallarsu; suna caccakata caccakar hankaka, ba sa nutsuwa, kuma ba sa tuna Allah a cikinta sai kaxan.

Daga cikin alamomin sakaci da sallah akwai yawan waiwaye a cikin sallah, da soshe-soshen jiki. Ko kuma xan kasuwa yana sallah amma idonsa yana a kan kayansa, to waxannan, ko da a zahiri suna sallah da jikkunansu, to amma a haqiqa ba sallah suke ba. Domin Annabi (ﷺ) ya ce wa mutumin da ba ya nutsuwa a cikin sallarsa: “Ka koma ka sake sallah domin kai ba ka yi sallah ba”.

Ya ku bayin Allah; haqiqa akwai wasu abubuwa da sukan janyo halartowar zuciya ga mai yin sallah, daga cikin su akwai: halarto da ma'anar abin da (shi mai sallar) yake faxa kuma yake aikatawa a cikin sallarsa: misali: idan ya yi kabbara ya xaga hannayansa, ya tuna cewa wannan girmamawa yake ga Allah, kuma idan ya sanya hannun dama a kan na hagu ya tuna cewa wannan qasqantar da kai yake a gabansa. Kuma idan ya yi ruku'u to yana girmama Allah ne, kuma idan ya yi sujjuda to wannan qasqantar da kai ne gaba ga xaukakar Allah.

An karvo daga Abu Hurairata (R.A.) daga Annabi )ﷺ( ya ce: "Allah Ta'ala Ya ce, "Na raba sallah tsakanina da bawana gida biyu, kuma bawana zai sami abin da ya roqa (a ( الْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ 2 ) [الفاتحة: 2]

) . Sai Allah Ta’ala ya ce, «Bawa na ya gode mini». Idan bawa ya ce, الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ 3 ) [الفاتحة: 3]

, sai Allah Ta’ala ya ce, «Bawana ya yabe ni». Idan kuma ya ce,

( مَالِكِ يَوْمِ الدِّينِ 4 ) [الفاتحة: 4]

, sai Ya ce, «Bawana ya girmama ni», wani karan kuma ya ce, «Bawana ya fawwala lamarinsa zuwa gare ni». Idan ya ce:

) إِيَّاكَ نَعْبُدُ وَإِيَّاكَ نَسْتَعِينُ 5 ) [الفاتحة: 5]

, sai ya ce: «Wannan tsakanina ne da bawana, kuma bawana zai sami abin da ya tambaya». Idan ya ce,

( اهْدِنَا الصِّرَاطَ الْمُسْتَقِيمَ 6 صِرَاطَ الَّذِينَ أَنْعَمْتَ عَلَيْهِمْ غَيْرِ الْمَغْضُوبِ عَلَيْهِمْ وَلَا الضَّالِّينَ 7 ) [الفاتحة: 7]

, sai ya ce wannan na bawana ne kuma bawana zai sami abin da ya roqa». Muslim ne ya ruwaito shi.

Yayin da ka ce: ((سبحان ربي العظيم وبحمده ko ka ce, (سبحان ربي الأعلى وبحمده), ko da kuwa ka faxe su ne da murya qasa-qasa to haqiqa Allah yana jin duk wata magana da kake faxa, kuma yana ganin duk wani aiki da kake aikata wa, komai qanqantarsa. Kuma ya san duk abin da kake tunani a cikinsa ko da kaxan ne. Kuma yayin da ka kalli gurbin sujjadarka to, Allah yana ganinka. Kuma yayin da ka yi nuni da yatsanka lokacin ambaton Allah a cikin tahiya; to Allah yana ganin nuninka, domin shi Maxaukakin Sarki, Shi ne Mai kewayewa ga bawansa, da sani da iko da gudanarwa, da ji da gani, da wanin wannan na daga ma’anonin Rububiyyarsa.

Kuma yana daga abin da zai taimaka masa wajan tsoron Allah a cikin sallah da nutsuwa a cikinsa, da ba da ita a bisa mafi cikar kama shi ne, ya roqi Allah ya taimake shi a bisa kyautata ibadar, domin Imamu Ahmad da Abu Dawud sun fitar da hadisi daga Mu’azu xan Jabal: cewa Manzon Allah (ﷺ) ya riqi hannunsa kuma ya ce, "Ya Mu'azu wallahi ni ina sonka, wallahi ni ina sonka". Sai ya ce, "Ina maka wasici kada ka bari bayan kowacce sallah ka ce, Ya Ubangiji ka taimake ni bisa ambatonka, da gode maka, da kyautata bautarka)) .

Kuma yan daga abin da yake taimakawa bisa tsoron Allah (a cikin sallah), imanin bawa cewa tsoron Allah shi ne ruhin sallah, Allah Ta'ala ya ce,

( الَّذِينَ هُمْ فِي صَلَاتِهِمْ خَاشِعُونَ 2 ) [المؤمنون: 2]

Ma’ana: (Waxanda suke masu tsoron Allah a cikin sallarsu).

Ina faxin abin da kuke ji, kuma ina neman gafarar Allah ga kaina da ku, da kuma sauran musulmi daga kowane zunubi, kuma ku nemi gafararsa lallai shi ne mai yawan gafara mai yawan rahama.

Huxuba Ta Biyu

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, majivincin nagartattu, mai gafarta zunubin masu neman gafara, mai xora karayar karyayy. Kuma Allah ya yi tsira da aminci a bisa shugaban masu tsoron Allah, kunma shugaban masu neman gafara, da kuma alayensa da sahabbansa gaba xaya, da kuma waxanda suka bi tafarkinsu har zuwa ranar sakamako, bayan haka.

Ya ku bayin Allah! Haqiqa sallah ita ce maraba tsakanin kafirci da imani, domin Jabir ya ruwaito cewa, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Haqiqa abin da ke tsakanin mutum da kafirci ba wani abu ba ne face barin sallah”. Muslim ne ya rawaito shi .

An karvo daga Buraida ya ce: Na ji Ma'aikin Allah (ﷺ) yana cewa: “Alqawarin da ke tsakaninmu (mu musulmi) da su (kafirai) shi ne sallah, duk wanda ya bar ta haqiqa ya kafirta”. Ahmad da Abu Dawud da Nasa'i da Tirmizi da Ibn Majah ne suka rawaito shi, kuma Tirmizi ya ce: Hadisi ne kyakkyawa ingantacce.

An karvo daga Abdullahi dan Shaqiq al-Uqaili (R.A.) ya ce: "Sahabban Muhammadu (ﷺ) sun kasance ba sa ganin cewa akwai wani aiki da barinsa yake zama kafirci ban da sallah". Tirmizi ne ya rawaito shi .

Ya ku bayin Allah! Haqiqa yana daga shiriyar Annabi (ﷺ) zaburarwa a kan yin sallah a cikin jama'a, da qarfafa wajabcinta, da bayanin falalarta; Muslim ya rawaito Daga Abi Huraira ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce, "Sallah a cikin jama'a ta xara sallar mutum a cikin gidansa, da sallar sa a kasuwarsa da daraja ashirin da xoriya, dalilin haka shi ne idan xayansu ya yi alwala, ya kyautata alwalar, sannan ya zo masallaci, babu wani abu da ya zaburar da shi sai sallah, kuma ba ya nufin komai face sallah, ba zai yi taku xaya ba face an xaukaka masa daraja xaya da shi, kuma an sarayar masa da laifi xaya da shi, har sai ya shiga masallaci. Kuma idan ya shiga masallaci zai zamo cikin (ladan) sallah matuqar sallah ce ta tsare shi, kuma mala'iku suna yin addu'a a bisa xayanku matuqar ya kasance a mazauninsa da ya yi sallah a cikinsa, suna cewa: “Allah ka gafarta masa, Allah ka karvi tubansa, matuqar bai cuci wani ba a cikinsa, matuqar alwalarsa ba ta karye ba”.

Kuma mai tsira da amincin Allah ya yi gargaxi a kan qin amsawa mai kiran sallah ba tare da wani uzuri ba. Domin an karvo daga Ibn Abbas (R.A.) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Wanda ya ji kiran sallah sannan bai amsa ba, to ba shi da sallah, sai dai idan yana da wani uzuri”. Ibn majah ne ya rawaito shi, da Ibn Hibban a cikin Sahihinsa, da Hakim kuma ya ingantan shi.

Duk sanda aka samu mutane uku zuwa sama, to sallar jam'i wajibi ce a kansu, a birni suke ko a qauye, in ko ba haka ba shaixan zai mallake su, ya vatar da su ga barin tafarki madaidaici, domin an karvo daga Abud Darda'i ya ce: Nia ji Ma'aiki (ﷺ) yana cewa: "Babu wasu mutum uku a cikin birni ko qauye da ba a tsaida sallah a cikinsu face shaixan ya mallake su, don haka na hore ku da lizimtar jama'a, domin ita kura tana cin dabbar da ta yi nisa ne". Ahmad da Abu Dawud da Nasa'i suka rawaito shi.

An karvo daga Abu Huraira Allah ya qara yarda a gare shi ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, "Haqiqa na yi nufin na umarci matasa na su tattaro min kawuna na itatuwa, sannan in zo wa mutanan da suke sallah a gidaddajinsu ba tare da suna da wata larlura ba, na qone musu gidajen".

Sai aka cewa Yazid wato ibn al-A'asam-: Juma'a yake nufi ko wata sallar? Ya ce: kunne na ya kurumce in ba na ji Aba Hurairah yana rawaito shi daga Manzon Allah (ﷺ) ba, bai ambaci Juma'a ko wata salla ba. Muslim da Abu Dawud suka rawaito shi, da kuma ibn majah da Tirmizi, amma shi a taqaice.

Kuma an rawaito daga xan Mas'ud ya ce: "Da za a ce ku yi sallah a cikin gidajanku kamar yadda wannan mai noqewar yake yi a gidansa, da kun bar sunnar Annabinku, da kuma za ku bar sunnar Annabinku da kun vata". Muslim da Abu Dawud suka rawaito shi.

Ya ku bayin Allah! Ku kiyaye sallah ta hanyar ba da rukunanta, da sharaxanta da wajibanta, sannan ku cika ta ta hanyar aikata mustahabbanta, domin sallah ita ce jigon addini, kuma babu addini ga wanda babu sallah a gare shi; Allah Ta'ala Ya ce

( حَافِظُوا عَلَى الصَّلَوَاتِ وَالصَّلَاةِ الْوُسْطَى ) [البقرة: 238]

Ma’ana: (Ku kiyaye salloli da kuma sallar tsakiya).

Ina neman tsari da Allah daga shaixani abin la’anta, da sunan Allah mai rahama mai jinqai:

( قَدْ أَفْلَحَ الْمُؤْمِنُونَ 1 الَّذِينَ هُمْ فِي صَلَاتِهِمْ خَاشِعُونَ 2 وَالَّذِينَ هُمْ عَنِ اللَّغْوِ مُعْرِضُونَ 3وَالَّذِينَ هُمْ لِلزَّكَاةِ فَاعِلُونَ 4 وَالَّذِينَ هُمْ لِفُرُوجِهِمْ حَافِظُونَ 5 إِلَّا عَلَى أَزْوَاجِهِمْ أوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُهُمْ فَإِنَّهُمْ غَيْرُ مَلُومِينَ 6 فَمَنِ ابْتَغَى وَرَاءَ ذَلِكَ فَأُولَئِكَ هُمُ الْعَادُونَ 7 وَالَّذِينَ هُمْ لِأَمَانَاتِهِمْ وَعَهْدِهِمْ رَاعُونَ 8 وَالَّذِينَ هُمْ عَلَى صَلَوَاتِهِمْ يُحَافِظُونَ 9 أُولَئِكَ هُمُ الْوَارِثُونَ 10 الَّذِينَ يَرِثُونَ الْفِرْدَوْسَ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ 11 ) [المؤمنون:1 - 11]

(Haqiqa muminai sun rabauta, wannan da suke tsoron Allah a cikin sallarsu) har zuwa faxinsa maxaukakin sarki: (da kuma waxanda suke kiyaye sallarsu. waxannan su ne masu gado. Waxanda suke gadar aljannar Firdausi, su masu dauwama ne a cikinta).





Tags:




Hany Al-rufa'iy