Daidaito akan koyarwar alqurani da sunnah


4279
Surantawa
Musulunci yayi fice da zama addini daidaitacce na tsaka-tsaki tsakanin alummu, shi yasa wannan aluma tayi fice akan sauran, don haka shima musulmi ya zama wajibi ya zama mai daidaituwa a dukkan alamuranshi na rayuwa.
HuxubaAllah wanda kuke yiwa junanku magiya da shi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Ya ku wanxanda suka yi imani ku ku ji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku ayyukanku, kuma ya gafarta muku zunubbanku. Wanda ya bi Allah da Manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawon shiriya shiriyar Annab Muhammad (ﷺ). Kuma mafi shirrin al'amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wani qagaggen abu (addini) bidi'a ce, duk wata bidi'a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta. Yaku Jama’a, A yau zamu tava wani maudu'i mai girma, wanda dukkan al’ummar musulmi suke buqatarsa fiye da buqatarta ga abincinta da abin shanta, saboda mahimmancinsa a rayuwar musulmi, wannan abu shi ne daidaito akan koyarwar alqurni da hadisi, da barin wuce gona da iri. ku sani – ya ku bayin Allah – daidaito shi ne tsayawa a tsakiya, ba tare da an koma gefe ba, kuma ba a wuce inda ya kamata a tsaya ba. Allah Maxaukakin Sarki yana cewa : ( وَكَذَلِكَ جَعَلْنَاكُمْ أُمَّةً وَسَطًا لِتَكُونُوا شُهَدَاءَ عَلَى النَّاسِ وَيَكُونَ الرَّسُولُ عَلَيْكُمْ شَهِيدًا ) [البقرة: 143]. Ma’ana : “Hakanan muka sanyaku tsaka – tsakin al’umma (wato zavavvu masu adalci) don ku zamo shaida a kan mutane, ku kuma Manzo ya zama shaida a kanku”. (Albaqara : 143). Ya sake cewa : ( يَا أَهْلَ الْكِتَابِ لَا تَغْلُوا فِي دِينِكُمْ وَلَا تَقُولُوا عَلَى اللَّهِ إِلَّا الْحَقَّ ) [النساء: 171] Ma’ana : “Ya ku ma’abota littafi – Yahudu da Nasara – ka da ku wuce gona da iri a cikin addininku, kada ku faxi komai akan Allah sai gaskiya”. (Annisa’i : 171). Manzon Allah (S.A.W) yana cewa, “Haqiqa wannan addini mai sauqi ne, babu wani wanda zai tsananta a cikin wannan addini face sai addinin ya rinjaye shi, don haka ku daidaita, ku kusanto, ku yi bushara, ku nemi taimako ta hanyar sammako da yammaci, da wani yanki na dare” Bukhari ne ya rawaito. An karvo daga Abdullahi xan Abbas – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah (S.A.W) ya ce min “Je ka tsinto min tsakuwowi, sai na tsinto masa ‘yan qananan tsakuwoyi, kamar irin waxanda ake iya harba wa da xan yatsa, lokacin da Manzon Allah (S.A.W) ya xora su akan hannunsa, sai ya ce, “Da kamar waxannan zaku yi jifa, ku nisanci wuce da gona da iri a addini, domin abin da ya halaka waxanda suke gabaninku shi ne wuce da gona da iri” Ahmad ne ya rawaito shi. Imam Ibnu Jarir – Allah ya yi masa rahama – ya ce, “Ina ganin cewa Allah Maxaukakin Sarki ya siffata (wannan al’umma) da cewa tana kan daidaito da tsaka – tsaki, saboda daidaitonta a cikin addini, ba su wuce gona da iri ba, irin yadda Kirista suka yi wajen bauta, da abin da suka faxa akan Annabi Isa, haka kuma wannan al’umma ba ta zama mai gazawa akan abin da aka umarce ta da shi ba, irin gazawar Yahudu waxanda suka canza littafin Allah, suka kashe Annabawa, suka yi wa Ubangijinsu Allah qarya, suka kafirce masa. Amma ita wannan al’umma ma’abociyar daidaito ce, don haka Allah ya saiffata su da hakan, domin al’amarin da Allah ya fi so shi ne tsaka – tsaki (ba gazawa ba wuce gona da iri)”. Yaku ‘yan uwana : Daidaiton wannan addini da tsaka – tsakinsa yana bayanna ne a dukkan sasannin wannan addini, a vangaren aqida, musulunci ya zama tsaka – tsaki a cikin addinai, babu karkacewa, ko maguzanci a cikinsa, kaxai bautar Allah ce tsantsa. Ta kaxaita Allah a cikin ayyukansa da wajen bauta masa, da sunayensa da siffofinsa, babu kamanta Allah da wani abin halitta, babu korewa Allah siffofinsa. Babu lalata ma’anar nassi. A vangaren qaddara ma musulunci a tsakiya yake, tsakanin waxanda suke kore qaddara, da wanda yake cewa kuma bawa tilasta shi a ke yi a cikin aikinsa. A wajen imani, nan ma musulunci tsakiya yake tsakanin waxanda suka yi jafa’i, suka cire ayyukan ibada daga abin da ake kira imani, da waxanda suka wuce gona da iri suka fitar da duk wanda ya yi savo daga da’irar imani, da waxanda suka yi hukunci da kafircinsa. Waxanda suke kan gaskiya ba sa kafirta mutum don ya yi zunubi, matuqar bai halatta yin sa ba, kamar yadda wanda yake savo ba ya zama mai cikakken imani, mumini gwargwadon imaninsa, fasiqi ne da manya – manyan zunubansa. A babin Annabta da walittaka da sahabbai akwai tsaka – tsaki a cikinsu : ba wuce gona da iri, da xaukan (Annabawa da waliyyai da sahabbai) Alloli koma bayan Allah, babu kuma jafa’I irin jafa’in Yahudawa, waxanda suka qaryata wasu Annabawan, suka kashe wasu. Hakanan Musulmai suna tsakiya wajen imani da Annabawa, sun yi imani da dukkan Annabawa, da dukkan littattafan Allah, kuma suna son waliyyan Allah, sannan suna nema wa Sahabban Manzon Allah (S.A.W) yardar Allah gaba xayansu. Ya ‘yan uwana musulmi : daidaito da tsayawa a tsakiya ba tare da wuce gona da iri ba a cikin wannan addini yana shiga vangaren ibada, saboda a musulunci ba a watsar da vangaren jiki, a kula da vangaren zuciya kaxai ba, a’a ana haxawa ne gaba xaya, a ba jiki haqqinsa, kamar yadda za a ba wa zuciya haqqinta. Allah yana cewa : ( وَابْتَغِ فِيمَا آَتَاكَ اللَّهُ الدَّارَ الْآَخِرَةَ وَلَا تَنْسَ نَصِيبَكَ مِنَ الدُّنْيَا ) [القصص: 77] . Ma’ana : “Ka nemi gidan lahira da abin da Allah ya baka, amma kada ka manta da rabonka na duniya” (Alqasas : 77). Saboda tsayawa akan daidaito Manzon Allah (S.A.W) ya hana Usman Bin Maz’un ya yi wa kansa fixiya, ya haramta wa kansa jin daxin duniya, ya ce masa, “Ni na fi ku tsoron Allah da kiyaye dokokinsa, amma duk da haka ina azumi ina hutawa, ina yin sallar (dare) kuma ina barci, ina auren mata, duk wanda ba ya son sunnata to ba ya tare da ni”. Bukhari da Muslim ne suka rawaito. A riwayar Muslim Manzon Allah (S.A.W) cewa ya yi : “Masu wuce gona da iri sun halaka” a wata riwayar dai ta Muslim cewa ya yi : “Wannan addini mai sauqi ne, ku shige shi da sauqi, kuma ku yi a hankali, babu wanda zai tsananta a wannan addini face sai addinin ya rinjaye shi”. Don haka musulunci ya nisantar da mabiyansa daga dukkan wani abun da yake tauye haqqin xan adam ne, da duk abin da yake sakaci ne wajen daidaita tsakanin rai da jiki. Yaku Musulmi : Daga cikin vangarorin da daidaiton wannan addini yake fitowa fili a cikinsu shi ne, abin da ya shafi halal da haram, shari’ar musulunci ta zama tsakiya tsakanin Yahudawa waxanda aka haramta musu da yawa daga cikin daxaxan abubuwa, da mutanen da suka halatta komai har da abin da aka haramta. amma musulmi sun tsaya inda Allah da Manzonsa suka tsayar da su. A tsarin tattalin arziki, musulunci ya daidaita tsakanin ‘yancin xaixaiku da kuma al’umma, ya girmama mallakar mutum xaya , ya tabbatar da ita, ya tsarkaketa, ta yadda ba zata cutar da al’umma ba, sai musulunci ya zama a tsakiya, savanin tsarin ‘yan jari hujja, tsarin da ya damu da mutum xaya akan sauran al’aumma (ya ba si dama ya wawure dukiyar al’umma, ya yi duk abin ya ga dama ko da al’umma zata cutu) hakanan savanin tsarin ‘yan gurguzu da yake hana mutum mallakar xaixaiku, da hujjar maslahar al’umma. A wajen ciyarwa nan ma ana samun daidaito, Allah Maxaukakin Sarki ya ce, ( وَالَّذِينَ إِذَا أَنْفَقُوا لَمْ يُسْرِفُوا وَلَمْ يَقْتُرُوا وَكَانَ بَيْنَ ذَلِكَ قَوَامًا 67 ) [الفرقان: 67] Ma’ana : “Waxanda idan za su ciyar ba sa varna, ba sa kuma yin qwafro, sun kasance a tsaka – tsakin haka”. (Alfur’qan : 67). Wannan kaxan kenan daga cikin wuraren da addinin musulunci yake a tsaka – tsaki, wanda hakan yana nuna wannan addini yana da girma, kuma addini ne na Allah. Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya shiryar da mu, ba don ya shiryar da mu ba da bamu shiryu ba. Ku ji tsoron Allah – Yaku bayin Allah – ku siffatu da abin da Allah ya umarce ku da shi, na daidaito da tsayawa a tsakiya, zaku rabauta. Allah ya yi mana Albarka cikin abinda muka ji, na Alqur ’ani da Hadisi, Shi Allah Mai iko ne akan dukkan komai.
Godiya ta tabbata ga Allah, Kyakyawan qarshe yana ga masu tsoron Allah, Tsira da Aminci su tabbata ga fiyayyen halitta, Manzon Allah (S.A.W) da iyalansa da Sahabbansa da waxanda suka bi su, har zuwa ranar sakamako gaba xaya. Bayan haka : Ya ‘yan uwana musulmi, Akwai wasu abubuwa da yin su yake kore daidaito a cikin addini, wajibi akan mutane su nisance su, daga cikin su : Akwai wuce gona da iri a bidi’a, mai wuce gona da iri shi ne mai yin qari a kan abin da shari’a ta yi umarni da shi, kodai wajen adadi ko wajen kamar da za a yi aikin, ko kuma yawansa, kamar wanda zai yi tasbihi xari bayan ya gama sallah, maimakon ya yi talatin da uku, kmar yadda Annabi (S.A.W) ya umarta a yi, ko kuma wanda zai xora wa kansa sanya waxansu tufafi na daban yayin da zai yi sallah ko zai shiga masallaci, da makamancin haka. Ita ko bidi’a tana sanya mai yin ta ya yi wa Allah gyara, ya zo da sabon abu wanda Allah da Manzonsa ba su yi umarni da shi ba. Shaikhul – Islam Ibnu Taimiyya – Allah ya yi masa rahama - ya ce, “Ya riga ya gabata cewa addinin Allah tsaka – tsaki ne, tsakanin mai wuce goda da iri da wanda yake gaza yin abin ake so. Duk abin da Allah Maxaukakin Sarki ya umarci bayinsa da shi, sai Shaixan ya fito wa (masu qoqarin yi) ta hanya biyu, don ya vatar da su, ko dai ya sanya su, su wuce gona da iri, ko kuma ya sanya su su yi sakaci da abin”. (Al-wasiyyatul Kubra) Yaku musulmi, ku sani cewa wuce gona da iri a addini yana kawo munanan al’amura, daga cikinsu, akwai halaka, kamar yadda Manzon Allah (S.A.W) ya ce : “Masu wuce gona da iri sun halaka, masu wuce gona da iri sun halaka”. A wata riwayar ya ce, “Abin da ya halaka waxanda suke gabaninku shi ne wuce gona da iri” don haka duk mai wuce gona da iri qarshensa shi ne halaka a nan duniya tun gabanin lahira. Halaka a nan ta haxa halaka ta zahiri da kuma halaka ta voye, zai iya halaka ya daina yin biyayya da ibada, ya gaza yin ta gaba xaya, zai iya kuma halaka ta hanyar karkacewarsa a aqida, da savawa umarnin Allah da shiriyar Manzon Allah (S.AW). Daga cikin munanan abubuwan da wuce gona da iri yake haifarwa akwai ta’adanci da yawan kafirta mutane ba kai ba gindi. Daga cikin irin waxannan abubuwa akwai vata surar musulunci da musulmi a idon duniya, wuce gona da iri yana vata hoton musulunci a yau a duniya, yana sanya mutane su guje wa addinin, kuma buxe qofa ne ga sukan addinin. Daga ciki akwai faxawa cikin savo, ka duba ka ga yadda khawarijawa wuce gona da iri ya kai su zuwa ga kashe musulmi, da barin masu bautawa gumaka. Daga cikin tasirin wuce gona da iri akwai barin ibada. Imamul Bukhari – Allah ya ji qansa da rahama – ya yi babi a cikin littafinsa ya ce, “Babin da yake bayanin abin da aka hana na tsanantawa wajen ibada”. Al – Hafiz Ibnu Hajar – Allah ya yi masa rahama – ya fassara wannan babi da cewa “a cikin wannan babi akwai kwaxaitarwa wajen daidaito a cikin ibada, da hana zurfafa wa a cikinta, da umarnin a fukanci ibada cikin nishaxi”. (Duba Fathul – Bari J 3 sh 36). Ku ji tsoron Allah – yaku bayin Allah – ku tsaya kan abin Allah da Manzonsa (S.A.W) suka umarta, kada ku wuce gona da iri a cikin ayyukanku, wuce gona da iri sharri ne, kada kuma ku yi sakaci, a cikin sakaci ma akwai halaka, ku sani Allah ba zai daina baku lada ba, har sai kun daina bauta masa, ku xauki ayyukan da zaku iya, ku nemi taimakon Allah, Shi ne mafi alherin masu taimako.




Tags:




Sa'ad Al-gamidy