Gargadi Akan bidia


7050
Surantawa
Haqiqa bidia tana da hatsarin gaske a cikin addini, shi yasa Allah da manzonsa suka yi hani daga ita a ayoyi da hadisai da dama , kuma suka nuna cewa ita bata ce bayyananna wadda kan halakar da mai ita.
Manufofin huxubar Bayanin haxarin bidi’a addini. Gargaxin mutane game da qirqirar bidi’a a addini. Bayanin wasu daga cikin abubuwan da suke jawo bidi’a a addini. Huxuba Ta Farko Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma mua neman tsarinsa daga sharrin kawukanmu da munanan aiyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar dashi, wanda kuma ya atar babu mai shiryar da shi, kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai allah, shi kaxai ne bashi da abokin taraiya, kuma ina shaidawa cewa Annabi Muhammad bawansane manzonsane, (Yaku waxanda kuka bada gaskiya kuji tsoron Allah yadda ya cancanta aji tsoronsa, kada ku mutu face kuna Musulmi). (Yaku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicce ku daga rai guda xaya kuma ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga gare su (su biyu) kuji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya dashi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Ya ku waxanda suka yi imani kuji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku aiyukanku, kuma ya gafarta muku zunubanku. Wanda ya bi Allah da manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawun shiriya shiriyar Annabi Muhammadu (ﷺ) kuma mafi sharrin al’amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wata bidi’a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta. Bayan haka, ku ji tsoron Allah - ya ku muminai – don ku samu rahama. Ku yi guzuri daga kyawawan ayyuka ko kwa rabauta. Ku rigayi kwanakinku da ayyukanku domin a cikin yankewar kwanaki akwai izina, kuma a cikin saurin shuxewar kwanaki akwai tunatarwa. Allah ya jiqan bawan da ya yi imani da Allah kuma ya tsaya qyam a kan atafarki, kuma duniya ba ta shagaltar da shi daga lahira ba! Ya ku musulmai, haqiqa Allah ta’ala ya aiko manzonsa Muhammadu (ﷺ) a lokacin da sawun manzanni ya xauke, yayin da vata ya kama qasa, duhu ya tsananta, halittu suka ruxe a cikin wautar jahiliyya, da hanyoyin makanta. Ba su san wani abu gaskiya ba. Sai manzancin Annabi da aikensa ya zamo su. Yana xauke da saqon fitar da mutane daga son zuciya da bin hanyar iyayensu zuwa bin sa da bin sunnarsa. Yayin da Annabi (ﷺ) ya tashi yana mai bushara da gargaxi a cikin mutane, kuma mai kira zuwa ga Allah, kuma fitila mai haske, nan da nan shaqiyyai suka shiga yaqarsa. Suka fuskanci kiransa da kafirci. Sai da Allah Ta’ala ya xaukaka kalmarsa ya bayyana addininsa. Manzon Allah (ﷺ) ya aikata abin da Allah ya wajabta masa. Allah ya shiryi al’umma da shi zuwa gaskiya, ya tseratar da halittu da yawa a sandiyyarsa. Annabin (ﷺ) bai rasu ba har sai da ya isar da manzanci, ya ba da amana, ya yi nasiha ga al’umma, ya cika addini, ya bar mu a kan tafarki tantarwai, wanda daresa kamar ranarsa ne. Ya ji tsoron kada mutane su koma zuwa ga son zuciyarsu, su bar bin sa, ko su bi wasu su bar sunnarsa, don haka ya gargaxe su, ya tsoratar da su, ya ba da labarin bayyanar fitintunu da vacewar sunnoni, da yaxuwar bidi’a. Ya yi gargaxi da a guji ma'abota soye-soyen zukata, waxanda suka farraqa addini, suka rarrabu bayan rasuwar Annabi (ﷺ) . Bayan wuce 'yan shekaru da wafatin Manzo (ﷺ) sai masu fifita hankali suka bayyana, qarqashin jagorancin Mu’utazilawa. Haka masu Sufaye suka wuce gona da iri. Kawarijawa suka fito, Murji’awa suka faso kai. Qungiyoyi suka rarrabu. Wasu mutane suka juya wa hanyar sunna baya. Suka ruxe a cikin vata. Babban musabbabin vacewar waxannan qungiyoyi duka kuwa shi ne barin sunna da rinjayar son zuciya, da miqa ragama ga hankali, da bin ra’ayin iyaye, da watsi da gaskiya saboda shaihunai da shugabanni. Waxannan su ne ‘yan huxu na bidi’a, kuma qungiyar gaba da sunna, wato son zuciya, da miqa ragama ga tsantsar hankali, da makauniyar biyayya, da jahilci. Don haka ne, dalilai suka yawaita daga Alqur’ani da sunnah da zantuttukan sahabbai da tabi’ai da shuwagabannin shiriya, suka tabbatar da hujjoji masu nuna fifikon dawwama a kan sunna sama da komai. Haka nan da bin shiriyar Annabi (ﷺ) da nisantar bidi’a da fararrun abubuwa. Haqiqa Alqur’ani mai girma ya cika da ayoyin biyayya da xa’a ga Manzo (ﷺ), da kuma cewa, bin Annabi (ﷺ) shi ne alamar soyayya ta gaskiya. Allah yana cewa: (قُلْ إِنْ كُنْتُمْ تُحِبُّونَ اللَّهَ فَاتَّبِعُونِي يُحْبِبْكُمُ اللَّهُ وَيَغْفِرْ لَكُمْ ذُنُوبَكُمْ وَاللَّهُ غَفُورٌ رَحِيمٌ31) [آل عمران: 31] (Ka ce idan kun kasance kuna son Allah, to ku bi ni Allah ya so ku, kuma ya gafarta musku zunubanku). Da faxinsa: (وَإِنْ تُطِيعُوهُ تَهْتَدُوا54) [النور: ٥٤]. )Idan kun bi shi kwa shiriya(. Haka nan yana cewa, (وَمَا آَتَاكُمُ الرَّسُولُ فَخُذُوهُ وَمَا نَهَاكُمْ عَنْهُ فَانْتَهُوا7) [الحشر: ٧]. (Abin da manzo ya zo muku da shi to ku karve shi, kuma abin da ya hane ku ga barinsa to ku hanu). Kuma babu wani abu bayan bin Annabi (ﷺ) sai bin son zuciya: فَإِنْ لَمْ يَسْتَجِيبُوا لَكَ فَاعْلَمْ أَنَّمَا يَتَّبِعُونَ أَهْوَاءَهُمْ وَمَنْ أَضَلُّ مِمَّنَ اتَّبَعَ هَوَاهُ بِغَيْرِ هُدًى مِنَ اللَّهِ إِنَّ اللَّهَ لَا يَهْدِي الْقَوْمَ الظَّالِمِينَ [القصص: 50] (To idan ba su amsa maka ba, to ka sani cewa suna bin son zuciyarsu ne, kuma wane ne mafi vata daga wanda ya bi son zuciyarsa ba tare da shirya daga Allah ba, lalle Allah ba ya shiryar da mutanen da suke azzalumai). Ma’abota son zuciya, su ne masu kawar da kai ga barin sunnoni. Allah ya ce, (وَمَنْ أَعْرَضَ عَنْ ذِكْرِي فَإِنَّ لَهُ مَعِيشَةً ضَنْكًا وَنَحْشُرُهُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ أَعْمَى124) [طه: 124] (Kuma duk wanda ya kau da kai ga barin ambatona, to yana a rayuwa mai qunci, kuma za mu tashe shi a ranar alqiyama yana makaho). Haka nan ahalin bidi’a suke cikin qunci da matsi da takura, babu yalwar qirji, ba nutsuwa. Domin shiriya ba ta kasancewa face a cikin biyayya ga Annabi (ﷺ): فَمَنِ اتَّبَعَ هُدَايَ فَلَا يَضِلُّ وَلَا يَشْقَى123) [طه: 123] ((Duk wanda ya bi shiriya ta, to ba zai vata ko ya wahala ba). Nana A’isha, ta ce manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Duk wanda ya farar da wani abu a cikin al’amarinmu wannan, abin da babu shi, to an mayar masa". Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi. A cikin riwayar Muslim, "Wanda ya aikata wani aiki ba da umarninmu ba, to an mayar masa”. An karvo daga Jabir (R.A) ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya kasance idan zai yi huxuba sai idanunsa su yi ja, sautinsa ya xaukaka, fushisa ya tsananta, kamar ka ce mai gargaxin runduna ne, yana cewa, "Barkanku da safiya! Barkanku da yamma". Kuma yana cewa: “An aiko ni alhali abin da ya rage ga tashin alqiyama kamar wxannan biyun ne". Sai ya haxa tsakanin ‘yan yatsunsa biyu, (manuniya da na tsakiya)”. Kuma yana cewa (ﷺ) “Bayan haka, haqiqa mafi alherin zance shi ne littafin Allah, kuma mafi alherin shiriya, shiriyar Muhammadu. Kuma mafin sharrin lamura qagaggunsu, kuma dukkani bidi’a vata ce”. Muslim da Ibn Majah da waninsa ne suka rawaito shi. Kuma na karvo daga Anas xan Malik (R.A) ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Haqiqa Allah ya toshe tuba daga duk wani mai yin bidi’a har sai ya bar bidi’arsa”. Xabarani ne ya rawaito shi, kuma salsalarsa kyakkyawa ce. Haka nan daga Irbadh xan Sariya ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ina yi muku kashedi da fararrun abubuwa, domin duk wani fararren abu vata ne”. Ahmad da Tirmizi da Ibn Majah da Ibn Hibban ne suka rawaito shi. Kuma Tirmizi ya ce, "Hadisi ne kyakkyawa ingantacce". Ya ku bayin Allah! Haqiqa lazimtar sunnah shi ne shaidawa Annabi Muhammad (ﷺ), manzon Allah ne. Kuma shi ne bin manzon (ﷺ) a cikin abin da ya yi umarni da shi da gaskata shi a cikin abin da ya ba da labari, da nisantar abin da ya yi hani da gargaxi a kansa. Kuma kada a bautawa Allah sai da abin da ya shar’anta. Don haka bai halatta a nemi kusanci zuwa ga Allah da wani addini ko ibada wanda ba manzon Allah (ﷺ) ne ya shar’anta ba. In ba haka ba za ta zama karvavviya a gurin Allah ba. Allah ya ce, (أَمْ لَهُمْ شُرَكَاءُ شَرَعُوا لَهُمْ مِنَ الدِّينِ مَا لَمْ يَأْذَنْ بِهِ اللَّهُ21) [الشورى: ٢١] (Ko kuma suna da wasu abokan tarayya ne da suka shar’anta musu wani abu na addini wanda Allah bai yi izini da shi ba). Don haka bai halatta a bi wasu maganganu da suka savawa sunna ba komai girman mafaxinsu. Kuma kowa a kan iya karvar maganarsa ko a mayar da ita banda Manzon Allah (ﷺ), kamar yadda Imamu Maliku ya faxa, Allah ya rahamshe shi. Kuma haqiqa Imamus Shafi’i, Allah ya jiqan sa, ya ce: “Malamai sun haxu a kan cewa duk wanda sunnar manzon Allah (ﷺ) ta bayyana a gare shi, ba shi da hurumin ya barta saboda maganar wani mutum”. Imamu Ahmad Allah ya jiqnsa ya ce: “Ina mamakin mutane da suka san Isnadi da ingancinsa, amma suke tafiya zuwa ga ra’ayin Sufyanu. Alhali Allah Ta’ala yana cewa: فَلْيَحْذَرِ الَّذِينَ يُخَالِفُونَ عَنْ أَمْرِهِ أَنْ تُصِيبَهُمْ فِتْنَةٌ أَوْ يُصِيبَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ63) [النور: 63]) (Kuma waxanda suka sava umarninsa, su ji tsoron kada wata fitina ko azaba mai raxaxi ta same su). Shin ka san ko mene ne fitinar? Fitinar ita ce, shirka, wataqila shi idan ya mayar da sashin maganarsa, wani abu daga karkata ta, ya faxawa zuciyarsa ya hallaka». Qarshen maganar Imam Ahmad ke nan. Ya ku musulmai! Kamar yadda musulunci yake, shi ne miqa wuya ga Allah, da saduda gare shi tare biyayya. To haka nan idan aka samu wani hadisi ya ingata daga wanda ba ya kuskure ya wajaba a sallama masa, a miqa wuya gare shi. Allah yana cewa, (وَمَا كَانَ لِمُؤْمِنٍ وَلَا مُؤْمِنَةٍ إِذَا قَضَى اللَّهُ وَرَسُولُهُ أَمْرًا أَنْ يَكُونَ لَهُمُ الْخِيَرَةُ مِنْ أَمْرِهِمْ وَمَنْ يَعْصِ اللَّهَ وَرَسُولَهُ فَقَدْ ضَلَّ ضَلَالًا مُبِينًا36) [الأحزاب: 36] (Kuma ba zai yiwu ga mumini ko mumina ba idan Allah da Manzonsa suka hukunta wani abu, ya zama suna da wani zavi daga lamarisu. Kuma duk wanda ya savawa Allah da manzonsa, haqiqa ya vata vata mabayyani). Ya ku musulmai! Shi kuwa savanin sunna, shi ne rarrabuwa a cikin addini, da vata mabayyani, Allah yana cewa, (وَأَنَّ هَذَا صِرَاطِي مُسْتَقِيمًا فَاتَّبِعُوهُ وَلَا تَتَّبِعُوا السُّبُلَ فَتَفَرَّقَ بِكُمْ عَنْ سَبِيلِهِ ذَلِكُمْ وَصَّاكُمْ بِهِ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ153) [الأنعام: 153] (Kuma wannan shi ne tafarkina madaidaici, to ku bi shi, kuma kada ku bi wasu hanyoyi sai su raba ku da tafarkinsa). Saboda duk wanda ya qetare abin da aka umarce shi da shi, to babu shakka ya yi shisshiga, kamar yadda Alqur’ani ya nuna, Allah yana cewa, (أُمِرْتَ وَمَنْ تَابَ مَعَكَ وَلَا تَطْغَوْا إِنَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ بَصِيرٌ112) [هود: ١١٢]. (Ka daidaita kamar yadda aka umarce ka, da wanda ya tuba tare da kai, kuma kada ku yi shisshigi, lalle shi mai gani ne ga abin da kuke aikatawa). Kuma haqiqa yin bauta da abin da mutum yake ganinsa mai kyau ne, kuma yake karkata zuwa gare shi, ba tare da wani dalili ko shiriya ba, shi ne haqiqanin bin son zuciya. Allah yana cewa, أَرَأَيْتَ مَنِ اتَّخَذَ إِلَهَهُ هَوَاهُ أَفَأَنْتَ تَكُونُ عَلَيْهِ وَكِيلًا43) [الفرقان: 43] (Yanzu ka ga wanda ya riqi son zuciyarsa shi ne abin bautarsa?!) Kuma yana cikin haxarin shiga cikin wanxanda Allah yake cewa game da su: (آَنِفًا أُولَئِكَ الَّذِينَ طَبَعَ اللَّهُ عَلَى قُلُوبِهِمْ وَاتَّبَعُوا أَهْوَاءَهُمْ16) [محمد: 16] (Waxannan su ne Allah ya yi rufi a kan zukatansu, kuma suka bi son zicuyarsu). Haqiqa Annabi (ﷺ) ya ambaci bid’a a matsayi vata. Domin haqiqa shi xan bidi’a yana vata ne a cikin bin son zuciya. Yakan xauki dalilai masu rikitarwa a mariqa ta son zuciya da sha’awa, ba mariqa ta miqa wuya zuwa hukunce-hukuncen Allah ba. Sai ya sanya son zuciya da kyautata abin, shi ne abin nemansa na farko, su kuma sauran dalilai ya nemi su goya masa baya. Sai ya aje dalilan a kan abin da ya dace da hankalinsa da son zuciyarsa. Don haka Allah mai buwaya da xaukaka ya ce, (يُضِلُّ بِهِ كَثِيرًا وَيَهْدِي بِهِ كَثِيرًا26) [البقرة: ٢٦]. (Yana vatar da mutane da yawa da shi, kuma yana shiryar da mutane da dadama da shi). Kuma Allah Ta’ala Ya yi gargaxi game da ma’abota vata wajen kafa dalili, kamar yadda Allah Ta’ala Ya ce: (هُوَ الَّذِي أَنْزَلَ عَلَيْكَ الْكِتَابَ مِنْهُ آَيَاتٌ مُحْكَمَاتٌ هُنَّ أُمُّ الْكِتَابِ وَأُخَرُ مُتَشَابِهَاتٌ فَأَمَّا الَّذِينَ فِي قُلُوبِهِمْ زَيْغٌ فَيَتَّبِعُونَ مَا تَشَابَهَ مِنْهُ ابْتِغَاءَ الْفِتْنَةِ وَابْتِغَاءَ تَأْوِيلِهِ وَمَا يَعْلَمُ تَأْوِيلَهُ إِلَّا اللَّهُ7) [آل عمران: ٧]. (Shi ne wanda ya saukar maka da littafi, a cikinsa akwai ayoyi wanda ma’anar su take a fili, wasu kuma masu rikitarwa. To amma su waxanda karkata take a cikin zukatansu sai su riqa bin abin da yake da rikitarwar, don neman fitina, da neman fassararsa, ba wanda ya san fassararsa sai Allah). Ya ku bayin Allah! Haqiqa wani ba shi da ra’ayi bayan sunnar Manzon Allah (ﷺ). An karvo daga xan Abbas (R.A), ya ce, "Wanda ya farar da wani ra’ayi da ba ya cikin littafin Allah, kuma sunnar manzon Allah ba ta zartar da shi ba, bai san abin da yake kai ba, yayin da ya gamu da Allah mai buwaya da xaukaka". Malam Shaxibi - Allah ya jiqansa - ya ce: “Haqiqa xan bidi’a ana jefa masa qasqanci a duniya, da fushin Allah. Saboda faxinsa maxaukakin sarki: (إِنَّ الَّذِينَ اتَّخَذُوا الْعِجْلَ سَيَنَالُهُمْ غَضَبٌ مِنْ رَبِّهِمْ وَذِلَّةٌ فِي الْحَيَاةِ الدُّنْيَا وَكَذَلِكَ نَجْزِي الْمُفْتَرِينَ152) [الأعراف: 152] (Lalle waxanda suka riqi xan maraqi, fushi da qasqanci a rayuwar duniya za su same su. Kuma haka muke sakawa masu qirqirar qarya). Wannan ya haxe su mutanen Annabi Musa da makamantansu, domin bidi’o’i dukkaninsu qirqirar qaya ne ga Allah”. Qarshen maganar Shaxibi. Ibnul Majishuna ya ruwaito daga Imamu Malik - Allah ya jiqansa - yana cewa, “Wanda ya qirqiri wata bidi’a a musulunci da yake ganinta kyakkyawa to haqiqa ya riya cewa Mahamma ya ha’inci manzanci. Domin Allah Ta’ala yana cewa: (الْيَوْمَ أَكْمَلْتُ لَكُمْ دِينَكُمْ3) [المائدة: ٣]. (Yau na cika muku addininku). To abin da bai zama addini ba a wancan lokaci, ba zai zama addini ba a yau”. Qarshen maganar Maliku. Kuma Annabi (ﷺ) ya ba da labari kamar yadda yake cikin sahihi Muslim cewa, duk masu musanyawa da masu canjawa za a kore su a fatattake su daga bakin tafkinsa. Haqiqa bidi’o’i suna rusa addini ingantacce. Kuma wasu mutane ba za su qirqiri wata bidi’a ba face Allah ya cire musu kwantankwacinta daga sunna. Wannan sananne ne, ana ganinsa quru-quru, domin kana ganin kwaxayin wasu mutane kan bidi’o’i fararru, da barinsu ga sunnon tabbatattu, ko ma wajibai. Kamar yadda kake ganin nishaxin tashohin rediyo da na talabijin, da na tauraron xan adam wajen nuna waxannan bidi’o’i da yaxa su, tare da irin savawa addinin da ke ciki, suna nuna ibadunsu kai tsaye, wanda gama gari ke ruxuwa da su. Suna zaton cewa addini ne, musamman idan masu dangatuwa ga ilimi da malanta suka shiga ciki. Don haka malamai su ji tsoron Allah kada su zama fitina ga muminai. Allah ya yi albarka gare ni da ku a cikin Alqur’ani da sunna, kuma ya amfane ni da ku da abin da ke cikinsu na ayoyi da hikima. Ina neman gafarar Allah ga kaina da ku!
Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin talikai, Allah ya yi tsira a bisa mafi darajar manzanni, Muhammadu (ﷺ) da alayensa da sahabbansa gabaxaya. Bayan haka: Haqiqa yana daga abin da yake jefa mutane cikin tarkon bidi’a da son zuciya, kwaikwayon iyaye da manya, ko bin kurakuran malamai. Ko kuma tsantsar ra’ayin biyayya ga shugabanni. An karvo daga Muqatil xan Hayyan Allah Ya jiqansa ya ce, “Ma’abota son zuciya su ne guba a cikin al’ummar Muhammadu (ﷺ). Suna ambaton Annabin (ﷺ) da ahalin gidansa, da wannan sai su riqa samun yabo daga jahilan mutane, daga nan sai su jefa su a cikin halaka. Sun yi kama da mutumin da yake shayar da guba a matsayin zuma. Yana daga cikin tsofaffin hujjoji da shaixan yake qawatawa mutane hanyoyinsa da su don ya don ya raba su da gaskiya da sunna, su ne makauniyar biyayya ga iyaye da shugabanni, da tsattsauran ra’ayi a wajen bin su, ko da sun kaucewa shiriya; wannan tsohuwar hanya ce da vatattu suke kafa hujja da ita, tun shekaru aru-aru. Ga shi Allah Ta’ala ya ba da labari game musayar Annabi Ibrahim da mutanensa yayin da ya ce musu: (مَا تَعْبُدُونَ مِنْ بَعْدِي قَالُوا نَعْبُدُ إِلَهَكَ وَإِلَهَ آَبَائِكَ إِبْرَاهِيمَ وَإِسْمَاعِيلَ وَإِسْحَاقَ إِلَهًا وَاحِدًا وَنَحْنُ لَهُ مُسْلِمُونَ133) [البقرة: 133] (Me kuke bautawa? Sai suka ce, muna bautawa gumaka ne, mukan dukufa wajen butarsu. Ya ce, shin suna jin ku yayin da kuke kiransu, ko suna amfanarku ko suna cutarwa? Suka ce kaxai mun sami iyayenmu ne haka suke aikatawa). A nan sai suka kauce daga ba da amsar tambayar, suka kafa hujja da biyayyar iyayensu. A cikin wata surar kuma: (أَمْ آَتَيْنَاهُمْ كِتَابًا مِنْ قَبْلِهِ فَهُمْ بِهِ مُسْتَمْسِكُونَ21 بَلْ قَالُوا إِنَّا وَجَدْنَا آَبَاءَنَا عَلَى أُمَّةٍ وَإِنَّا عَلَى آَثَارِهِمْ مُهْتَدُونَ22وَكَذَلِكَ مَا أَرْسَلْنَا مِنْ قَبْلِكَ فِي قَرْيَةٍ مِنْ نَذِيرٍ إِلَّا قَالَ مُتْرَفُوهَا إِنَّا وَجَدْنَا آَبَاءَنَا عَلَى أُمَّةٍ وَإِنَّا عَلَى آَثَارِهِمْ مُقْتَدُونَ23قَالَ أَوَلَوْ جِئْتُكُمْ بِأَهْدَى مِمَّا وَجَدْتُمْ عَلَيْهِ آَبَاءَكُمْ قَالُوا إِنَّا بِمَا أُرْسِلْتُمْ بِهِ كَافِرُونَ24) [الزخرف: ٢١ – ٢٤]. (Shin ko kuwa mun ba su wani littafi ne wanda suke riqo da shi? Kaxai cewa suka yi, mu mun sami iyayenmu a kan wani addini, kuma mu masu bin su ne sau-da-qafa. Haka yake, ba mu aiko da wani mai gargaxi a gabaninka a cikin wata alqarya ba, face masu morewa a cikinta sun ce, haqiqa mu mun tarar da iyayenmu a kan wani addini, kuma mu masu bin su ne sau-da-qafa. Ya ce, ko da na zo muku da mafi shiriya daga abin da kuka sami iyayenku a kai? Suka ce, haqiqa mu masu kafircewa ne da abin da aka aiko ku). To ku ji tsoron Allah ya ku Musulmai. Ku bi abin da aka saukar muku daga Ubangijinku, kuma kada ku bi wasu majivinta ba shi ba. Ku sani cewa savawa sunna a zahiri alama ce ta riya a baxini. Ya ku bayin Allah! Haqiqa akwai varnace-varnace masu yawa a cikin bidi’a. Bidia’ tana rusa addini ingantacce ta maye gurbin sunna. Domin Darimi ya ruwaito da ingantaccen isnadi, daga Hassan xan Axiyya Almuharibi, Allah ya jiqansa, ya ce, “Wasu mutane ba za su qirqiri wata bidi’a a cikin addinisu ba, face Allah ya cire musu sunna kwankwacinta. Sannan ba za a dawo musu da ita ba har tashin alqiyama.” Don haka ne ma za ku tarar da ‘yan bidi’a suna nacewa (bidi’arsu) fiye da yadda suke nacewa a kan sunna. Domin shaixan ya qawata musu bidi’a». Kuma za ka ga xan bidi’a yana ganin cewa, addini yana buqatar qari. Don haka shi yana nufin ya kammala addini da bidi’arsa. In ba haka ba da yana ganin cewa addinin cikakke ne, to ai da bi yi bidi’a ba. Har ila yau, ‘yan bidi’a qyamar sunna suke yi. Kuma ba su da wata himma da kazar-kazar wajen aiki da sunna. Suna kaza-kazar ne wajen aikata bidi’a. Don haka za ka tarar da su suna ciyar da dukiyoyinsu, suna wahalar da jikkunansu, suna tozartar da lokutansu a cikin raya bidi’a. Sannan bidi’a na dawo wa da mutane jahiliyya cikin rayuwarsu. Sanna sukan haifar da rarrabuwa a savani. Kowace qungiya na ganin abin da take a kai ya fi na xayar, kamar yadda Allah Ta’ala yake faxa: (كُلُّ حِزْبٍ بِمَا لَدَيْهِمْ فَرِحُونَ32) [الروم: 32] (Kowace qungiya na alfahari da abin da ke gurinsu). Kuma kamar yadda Tsarkakakken Sarki ya ce: وَلَا تَتَّبِعُوا السُّبُلَ فَتَفَرَّقَ بِكُمْ عَنْ سَبِيلِهِ153) [الأنعام: 153]) (Kuma kada ku bi wasu hanyoyi, sai su raba ku da tafarkinsa) Su kuwa sunnoni suna tattara mutane ne, su haxa tsakanin zukatansu, sai su zama ‘yan uwa masu son juna a kan turba xaya, da addini xaya. Suna masu aiki da faxinsa Maxaukakin sarki: (وَاعْتَصِمُوا بِحَبْلِ اللَّهِ جَمِيعًا وَلَا تَفَرَّقُوا103) [آل عمران: ١٠٣]. (Kuma ku yi riqo da igiyar Allah gabaxaya, kada ku rarraba). Bidi’a tana gadar da girman kai, da qin gaskiya. Shi xan bidi’a idan aka kira shi zuwa gaskiya, ba zai yadda ba. Sai dai ya riqe bidi’arsa gangam, ya kuma yi dukkanin wani yunquri domin kare ta. Bidi’a tana vata addini nagartacce. Wannan kuwa shi ne burin shaixanun mutane da aljanu daga kafirai da munafukai maqiya addini. Suna qoqarin vata shi ta dukkan hanyoyi. Mafi muhimmancin makami da suke amfani da shi, a wajen rushe addini shi ne bidi’o’i da camfe-camfe don su munana musuluncin da su. Su rufe fuskar ingantaccen addini da su, har wanda bai san haqiqar Musulunci ba, sai ya yi zaton cewa musulunci tarin camfe-camfe ne da tilin gurvatattun ibadu. Sai wanda yake nufin shiga cikinsa ya fasa. Bugu da qari, su waxanda ke yayata bidi’o’i suna girbar wasu amfanoni na abin duniya daga yaxa bidi’a, ko su sami damar biyan sha’awoyinsu na haram. Sau nawa ake kashe kuxi wajen raya waxannan bidi’o’i, nawa ne aka keta na mutunci saboda cuxanya tsakanin maza da mata ba tare da mai tsawatarwa ko mai kwava ba? Don haka ya wajaba ga malamai da masu huxuba su gargaxi mutane daga gare ta. Ya ku mutane! Haqiqa sahabban Manzon Allah (ﷺ) sun kasance suna gargaxi game da bidi’a. Labari ya zo ga Abdullahi xan Mas’ud (R.A) cewa Ibn Amru bn Utba, tare da wasu abokansa sun gina wani masallaci a bayan garin Kufa. Sai Abdullah ya ba da umarnin a je a rusa shi. Sannan labari ya sake iske shi cewa, su dai waxanna mutane suna taruwa a wata nahiya ta masallacin Kufa, suna wani irin tasbihi da tahlili da kabbara. Sai Abdullahi ya sanya rigarsa mai haxe da hula, sannan ya tafi ya zauna a wajensu. Yayin da ya fahimci abin da duk suke yi, sai ya yaye hular rigar, sannan ya ce, "Ni ne Abu Abdurrahman". Sannan ya ci gaba da cewa: “Haqiqa ku, ko dai kun fi sahabban Manzon Allah (ﷺ) ilimi, ko kuma kun zo da bidi’a ce da zalunci. Sai Amru bin Utbah ya ce, "Muna istigfari ne sau uku". Sannan wani mutum daga Bani Tamim ya ce, "Wallahi ba mu fi sahabban Muhammadu (ﷺ) ilmi ba, kuma ba mu zo da bidi’a ta zalunci ba, mun haxu ne kawai muna zikiri". Sai xan Masu'ud ya ce, "Tabbas kun yi. Na rantse da wanda ran xan Mas’udu yake hannunsa, wallahi da za ku kama hanyar sahabbai, haqiqa da kun san in riga na muku fintinkau. Idan kuwa kun ruxe kun saki hanya, dama ko hagu, to kun vata, vata mai nisa". Don haka ku ji tsoron Allah Ya bayin Allah, su sani cewa Musulmi yana da wadatuwa da alheri mai yawa a cikin abin da ya tabbata daga Annabi (ﷺ). Saboda haka kada ku waiwaya zuwa abin da yake savanin haka na bidi’o’i da abin da bai tabbata daga ruwayoyi ba. Abin da Annabinku (ﷺ) yake kai, da magabatan al’umma, ya ishe ku.




Tags:




Sahl Yaseen