Wuta Da Aljanna


6732
Surantawa
Aljannah itace mafi tsadar haja, wadda masu yin aiki suke yi saboda ita . Cikinta akwai fuskoki masu haske masu murmushi, cikinta akwai kyawawan abubuwa ,kuma akwai matan hurul-iyni. Ita ko wuta, azaba ce dawwamamma, cikinta akwai ruwan sha mai tsananin zafi, da azaba mai tsauri. Babu wanda ze ji labarin aljanna face ya tashi tsaye wajen nemanta, hakanan babu wanda ze ji labarin wuta face ya dage wajen nesanta da ita.

Yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah. Tsira da amincin Allah su tabbata ga annabin rahama, annabinmu Muhammadu da alayensa da sahabbansa da waxanda suka bi tafarkinsa har zuwa tashin qiyama. Bayan haka:

Ya ku bayin Allah. Ubangiji mai girma da buwaya ya horewa bayin hanyoyi daban daban don samin gidan aljannah domin tsananin tausayinsa ga bayinsa.

Allah yana faxa a cikin littafin mai tsarki cewa:

 

{إِنَّ اللَّهَ اشْتَرَى مِنَ الْمُؤْمِنِينَ أَنْفُسَهُمْ وَأَمْوَالَهُمْ بِأَنَّ لَهُمُ الْجَنَّةَ يُقَاتِلُونَ فِي سَبِيلِ اللَّهِ فَيَقْتُلُونَ وَيُقْتَلُونَ وَعْدًا عَلَيْهِ حَقًّا فِي التَّوْرَاةِ وَالْإِنْجِيلِ وَالْقُرْآَنِ وَمَنْ أَوْفَى بِعَهْدِهِ مِنَ اللَّهِ فَاسْتَبْشِرُوا بِبَيْعِكُمُ الَّذِي بَايَعْتُمْ بِهِ وَذَلِكَ هُوَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ} [التوبة: 111]

 (Lalle Allah ya sayi rayukan muminai da farashin aljanna. Su yi yaqi don xaukaka kalmar Allah, sai su kashe kuma a kashe su. Wannan alkawari ne na gaskiya da ya xaukarwa kansa a cikin Attaurah da Linjila da Alqur'ani. Wanene wanda ya fi Allah cika alkawarinsa?! Don hka ku yi murna da wannan ciniki da kuka yi da Allah. Wannan kuma shi ne babban rabo

An karvo daga Jarir xan Abdullahi ya ce: Mun kasance a wani lokaci a wajen Manzon Allah da daddare, wata yana tsakiyar haskensa, sai Manzon Allah ya ce: “Haqiqa za ku ga Ubangijinku, a fili kamar yadda kuke ganin wannan watan a wannan lokaci, ta bare da turereniya  ba. Saboda haka duk kada xayanku ya yarda a fi qarfinsa akan sallar Asuba da ta Magariba". [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

Manzon Allah ya ce: “Duk wanda ya yi sallar nafila raka’a goma sha biyu a yini da dare, Allah zai gina masa gida a aljanna. Raka’a biyu kafin asubahi. Raka’a huxu kafin azahar da raka’a biyu a bayanta, da raka’a biyu bayan sallar magariba da raka’a biyu bayan sallar isha’i". Muslim ne ya ruwaito shi.

A game da qiyamullaili, Allah yana cewa;

 

{تَتَجَافَى جُنُوبُهُمْ عَنِ الْمَضَاجِعِ يَدْعُونَ رَبَّهُمْ خَوْفًا وَطَمَعًا وَمِمَّا رَزَقْنَاهُمْ يُنْفِقُونَ} [السجدة: 16]

(Jukkunansu suna nisa da shimfixinsu. Suna bautawa Ubangijinsu suna masu tsoron azabarsa, masu kwaxayin ladansa. Kuma suna ciyarwa daga abin da muka azurta su). Shi ya sa Manzon Allah yake cewa: “Ku yaxa sallama a tsakaninku. ku ciyar da abinci,  ku sada zumunci, ku yi sallah da daddare lokacin da mutane suke barci, sai ku shiga aljanna da aminci". [Tirmizi ne ya ruwaito].

Sannan ka lizimci ambaton Allah. Kamar yadda Annabi (r) yake cewa: (Wanda duk ya ce, Subhanallahi, wal-Hamdu lillahi, to za a dasa masa dabino a aljannah). (Tirmizi ne ya ruwaito).

Hakanan Manzon Allah yana cewa: “Na ga Annabi Ibrahim a daren da aka yi Isra’i da ni. Ya ce ya Muhammad ka isar wa da al’ummarka gaisuwata. Ka ba su labari da cewa, aljanna turvayarta mai qanshi ce. Ruwanta mai daxi ne. qasarta qequwa ce. Dashenta kuwa shi ne, Subhanallahi, wal-Hamdu lillahi Walaa-ilaaha Illal-Lahu. Wal-Lahu Akbar". [Tirmizi ne ya ruwaito].

Yana daga cikin hanyoyin samin gidan aljannah, bawa ya kyautata halayensa. Manzon Allah (r) yana cewa: "Ba na ba ku labari ‘yan aljanna daga cikin mazajenku ba? Annabi yana aljanna, Siddiqi yana aljanna, Shahidi yana aljanna, da wanda yake ziyarar xan’uwansa a can wani gari don Allah. Matanku 'yan aljannah su ne: Da dukkanin mace mai yawan nuna qauna ga mijinta, mai yawan haihuwa, wacce take xora hannunta a kan hannun mijinta in ta vata masa rai, ta riqa cewa, "Ba zan iya barci ba idan ba ka huce ba". Nisa'i ne ya ruwaito shi.

Allah maxaukakin sarki yana cewa:

 

{إِنَّ الَّذِينَ آَمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ أُولَئِكَ هُمْ خَيْرُ الْبَرِيَّةِ">جَزَاؤُهُمْ عِنْدَ رَبِّهِمْ جَنَّاتُ عَدْنٍ تَجْرِي مِنْ تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا أَبَدًا رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمْ وَرَضُوا عَنْهُ ذَلِكَ لِمَنْ خَشِيَ رَبَّهُ} [البينة: 7-8]

(Haqiqa waxanda suka yi imani, kuma suka yi ayyuka na gari, to waxannan su ne mafi alkhairin halitta. Sakamakonsu a wajen Ubangijinsu aljannatai ne waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu. Suna dawwama a cikinsu har abada. Allah ya yarda da su. Suma sun yarda da shi. Wannan sakamakon ne na wanda duk ya ji tsoron Ubangijinsa).

Ya Allah ka ba mu da cewa da gidan Aljannarka ta Firdausi. Ka sanya mu cikin masu aiki tuquru don gina lahirarsu da sa mun yardarka, da ganin fuskarka ranar gobe qiyama. Allah ka nisatar da fuskokinmu daga wuta. Ka nesatar da ayyukanmu daga ayyukan 'yan wuta. Ka sa aljannarka madawwamarmu. Amin.






Tags:




Taufeeq Al-sa'ig