Yin Aiki Don Allah Da Bayanin Muhimmancin sa


5344
Surantawa
Yin aiki don Allah abin nema ne babba, kuma yin ko-in-kula dashi hadari ne wawakeke, domin Allah baya karbar aiki sai ya zama aiki ne kyakkyawa, kuma aka yisa domin shi. Don haka dukkan wanda yayi wani aiki yayi tarayyar Allah da wani ciki, to fa lallai Allah baze amsa wannan aiki ba duk yawanshi kuwa, amma dukkan wanda yayi aiki don Allah, ta lallai Allah zai amshi wannan aiki duk qarancinsa.

Manufofin huxubar

Wajabcin tsarkake ayyuka domin Allah.

Yana daga cikin sharuxxan karvar aikin mumini.

Muhimmancinsa da haxarinsa.

Tsoratarwa dangane da abubuwan da suke rushe ikhlasi.

Amfanin yin (Ikhlasi), tsarkake aiki da fa’idojinsa.

Huxuba Ta Farko

Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma muna neman tsarinsa daga sharrin kawukanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar da shi, wanda kuma ya vatar to babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaxai ne ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi Muhammadu bawansa ne manzonsa ne. (Yaku waxanda suka yi imani ku ji tsoron Allah yadda ya cancaci a ji tsoronsa, kada ku mutu face kuna musulmi). (Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicceku daga rai guda xaya, kuma ya ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga garesu (su biyu). Ku ji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya da shi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Yaku wanxanda suka yi imani ku ku ji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku ayyukanku, kuma ya gafarta muku zunubbanku. Wanda ya bi Allah da Manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawon shiriya shiriyar Annab Muhammadu (ﷺ). Kuma mafi shirrin al'amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wani qagaggen abu (a addini) bidi'a ce, duk wata bidi'a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta".

Bayan haka: Ya ku musulmi!

Wanene a cikinmu nan ba ya fatan ya zama karvavve a gurin Allah?!

Wanene daga cikinmu a nan yake fatan ayyukansa su zama qura abar xaixaitawa?! ranar tsayuwarsa gaban Ubangijinsa?!

Wanene cikinmu a yau ba ya son ya gan shi cikin 'yan aljannah ranar gobe qiyama?!

Babban abin maganarmu a wannan haxuwa tamu ta yau shi ne magana a kan tsarkake aiki domin Allah, wanda Allah ba ya karvar ibada sai da shi. Kuma adalinlinshi ne Allah yake xaukaka darajar bawa. Ko ya qasqantar da shi.

Allah ba ya karvar aikin bayi sai idan an yi aikin dominsa. Duk wanda ya aikata aiki ya yi tarayya da Allah a cikin wannan aiki, to Allah ya wadatu ga barin karvar wannan aikin, duk kuwa yadda wannan aiki yake da yawa. Allah yana cewa:

( إِنَّا أَنْزَلْنَا إِلَيْكَ الْكِتَابَ بِالْحَقِّ فَاعْبُدِ اللَّهَ مُخْلِصًا لَهُ الدِّينَ 2أَلَا لِلَّهِ الدِّينُ الْخَالِصُ3) [الزمر: ٢ – ٣].

“ Haqiqa mun saukar maka da littafi da gaskiya, ka bautawa Allah Shi kaxai kana mai tsarkake aiki dominsa. Ku saurara tsarkakakken addini na Allah ne”.

Hakanan yake cewa:

(قُلْ أَمَرَ رَبِّي بِالْقِسْطِ وَأَقِيمُوا وُجُوهَكُمْ عِنْدَ كُلِّ مَسْجِدٍ وَادْعُوهُ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ29) [الأعراف: 29]

(Ka ce da su, Ubangijina ya yi umarni da tsayar da adalci. Kuma tsayar da fiskokinku a kowane masallaci. Kuma ku bautawa masa kuna masu tsarkake bauta dominsa).

Ya kuma cewa a wani wurin:

(فَادْعُوا اللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ وَلَوْ كَرِهَ الْكَافِرُونَ14) [غافر: 14]

(Ku bautawa Allah kuna masu tsarkake addini gare shi, Shi kaxai, koda kafirai sun qi).

Hakanan ya sake cewa:

(هُوَ الْحَيُّ لَا إِلَهَ إِلَّا هُوَ فَادْعُوهُ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ الْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ65) [غافر: 65]

(Shi ne rayayye babu abin bauta da gaskiya sai shi. To ku bauta masa kuna masu tsarkake addini gare shi. Gudiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai).

Ya sake cewa,

(وَمَا أُمِرُوا إِلَّا لِيَعْبُدُوا اللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ حُنَفَاءَ وَيُقِيمُوا الصَّلَاةَ وَيُؤْتُوا الزَّكَاةَ وَذَلِكَ دِينُ الْقَيِّمَةِ5) [البينة: 5]

(Ba a umarce su da komai ba sai su bauta wa Allah suna masu tsarkake addini agare shi. Kuma su tsaida sallah, su ba da zakka, wannan shi ne addinin miqaqqiyar hanaya).

Yin aiki domin Allah shi ne, ka yi aiki domin neman yardar Allah ba ta tare da haxa shi da wani ba. Ba riya, ba yi don a ji. Idan aiki ya zama haka, to ya lalace, mai yin aikin ma ya halaka.

ImamTirmizi ya fitar da hadisi daga Shufayyu al-asbahi, wata rana ya shigo Madina sai ya ga taron mutane sun kewaye wani mutum. Sai ya ce, «Wanene wanna kuma?». Sai aka ce masa Abu Huraira ne. Sai na matsa kusa da shi na zauna a gabansa yana ba mutane hadisi. Bayan mutane sun watse, sai na ce da Abu Huraira na haxa ka da Allah ka faxa mini wani hadisi wanda ka ji shi daga manzon Allah, kuma ka kiyaye shi, kuma ka fahimce shi. Sai Abu Huraira ya ce, «Zan faxa maka hadisin da na ji daga manzon Allah, kuma na kiyaye shi, na fahimce shi. Sai nan da nan Abu Huraira ya shixe. Sannan daga baya ya dawo hayyacinsa. Sai ya sake cewa, «Lallai zan faxa maka hadisin da na ji daga manzon Allah a wannan gida, ba wani tare damu, daga ni sai shi. Sai ya sake shixewa. Sannan ya farfaxo. Ya shafa ruwa a fuskarsa. Sai ya sake cewa, «Lallai zan faxa maka hadisin da na ji daga manzon Allah a wannan gida, ba wani tare damu, daga ni sai shi. Sai ya sake shixewa. Sannan ya farfaxo. Ya shafa ruwa a fuskarsa. Sannan ya yi wata shexewa mai qarfi, har ya kifa da fuskarsa. Na kama shi na riqe shi a jikina na daxe. Sai ya farfaxo. Sai ya ce, «Manzon Allah (ﷺ) ya ba ni labari cewa, ranar alqiyama Allah Zai sauko domin hukunci a tsakanin bayi. Kowace al'umma an gurfanar da ita a gaban Allah. Farkon wanda Allah zai kira domin yi masa hisabi mutumin da Allah ya ba shi Alqur’ani, da mutumin wanda ya mutu a wajen jihadi, da wanda Allah ya ba shi dukiya mai yawa. Sai Allah ya ce da makaranci, "Ban sanar da kai abin da na saukarwa Manzona ba?" Sai ya ce, "Allah Ka sanar da ni". Sai Allah ya ce, "To me ka yi da shi?" Sai ya ce, "Na kasance ina karanta shi dare da rana". Sai Allah ya ce, "Qarya kake". Mala’iku ma su ce masa, "qarya kake". Allah ya ce,"Ka karanta shi ne don a ce maka makaranci, kuma an faxa".

Sai a zo da mai dukiya, sai Allah ya ce, "Ban yalwata maka dukiya ba, har ka zamana ba kada buqata a gurin wani?". Sai ya ce: E, ka yi ya Ubangiji". Sai Allah ya ce, "To me kai da dukiyar da na ba ka"? Sai ya ce, "Na kasance ina sada zumiunci, ina sadaka". Sai Allah ya ce, "Qarya kake". Sai mala’iku ma su ce masa, "Qarya kake. Sai Allah ya ce, "Ka yi ne don a ce maka mai kyauta, kuma an faxa". Sai a zo da wanda aka kashe wajen xaukaka kalmar Allah. Sai Allah Ya ce da shi, "A kan me aka kashe ka?". Sai ya ce, An umarce ni da yin jihadi don xaukaka kalmarka, na yi yaqi har aka kashe ni". Sai Allah ya ce, "Qarya kake". Sai mala’iku su ma su ce masa, "Qarya kake". Allah ya ce, "Kwai ka yi ne don a ce maka jarimi, kuma an faxa.

Abu Huraira, ya ce, "Sai manzon Allah ya buge ni a gwiwoyina ya ce, "ya Aba hurairah, waxannan su ne mutane uku da za ta fara qonawa a ranar alqiyama".

Ya kamata mu kula da kyau, me ya sa makarancin al’qur’ani, alqur’anin bai cece shi ba? Tun da qur’ani yana ceton masu karanta shi. Ba komai ya sa ba, saboda yana karanta al’qur’nin ne ba don Allah ba. Haka nan mai dukiya, alherin da yake yiwa mutane bai cece shi ba. Saboda ba don Allah ya yi ba. Haka shi ma wanda ya mutu a wajen jihadi. Wannan wa’azi ne da gargaxi ga dukkanin mai hankali da lura.

Babbar shirka, ita ce ka sanya wa Allah abokin tarayya ana bauta masa. Mai yin wannan ya fita daga musulunci. Kuma duk aikinsa ya rushe.

Qaramar shirka kuwa ita ce, yin aiki ko magana wanda shari'a ta kira shi shirka, duk da cewa ba ya fitar da mutum daga musulunci, kamar riya, ko aiki don aji a faxa. To wannan yana tauye tauhidin mutum, kuma yana kure ikhlasi. Yana kuma vata aiki.

Imam Ahmad ya fitar da hadisi a cikin Musnad xinsa, daga Mahmud bn Labid, cewa manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Babban abin da na fi muku tsoro shi ne qaramar shirka". Sai sahabbai suka tambaye manzon Allah (ﷺ), Mene ne qaramar shirka? Sai ya ce, "Riya. Allah zai ce da su a ranar alqiyama idan ya sakakwa bayi a kan ayyukansu, "Ku je wajen waxanda kuke yi domin su, a duniya, ko ka samu sakamakonku a wajensu?".

Ibn Abbas ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, "Duk wanda ya yi abu don a ji ya zai jiyar game da shi. Hakanan duk wanda ya yi dan a gani, Allah zai nuna shi a gan shi". Bukhari da Muslim ne suka rawaito.

Sau da yawa mutum zai yi aikin lahira don neman duniya da jin daxinta. Kamar wanda zai je jihadi don neman ganima, ko neman ilimi don ya samu takardar shaida (Certificate) da samun aiki.

To irin wannan yana da yana biyu:

Na farko: Mutum ya nemi duniya tsantsarta da aikin lahira, ko ya daidaita neman duniyar da neman lahirar. Ko ya rinjayar da neman duniyar akan neman lahirar. To wannan yana rushe ikhlasi da aiki baki xaya.

An karvo daga Ubayyu xan Ka’ab, ya ce, "Manzon Allah (ﷺ) ya ce, ka yi wa wannan al’umma bushara da xaukaka da kafuwa, da nasara a doron qasa. Duk wanda ya yi aikin lahira don neman duniya, to ba shi da rabo a wajen Allah". Ahmad ne ya rawaito.

Na biyu: Ya zamana ya yi akin qwarai ya kuma nufi wani abu da shi wanda yana daga cikin manufar shari'a a wannan ibadar, ko ma yana qarfa shi mai ibadar. To wannan ya halatta, kuma ba ya rushe ikhlashi. Duk da cewa, ladan mutum a nan ba zai kai kamar ladan wanda ya yi ikhlasi tsantsa ba.

Bin son-ciya kuwa, shi ne mutum ya riqa bautar Allah saboda wata biyan buqata ta shi ta karankansa, ba don Allah ba. To hakan yana rushe ikhlasin bawa.

Shi kuma jiji-da-kai, shi ne, mutum ya riga shi wani ne, saboda wani aiki da ya yi, ya ruxu da wannan aikin. Ya daina tuna ni'imar Allah da ya yi masa kwata-kwata. To wannan ya ma fi riya tsanani da muni. Yana daga cikin shirka ta zuciya wanda yake lizimtar bawa. Domin bala'in da yake tattare da mai jiji-da-kai shi ne, shi yana aikin ibada ne ba don neman kusancin Allah mahalicci ba, a'a yana yin ta ne kawai don biyan buqatar kansa. Saboda hakane Imamun Nawawi yake cewa: "Ikhlasi yana gamuwa wani lokaci da jiji-da-kai. Duk wanda ya yi jiji-da-kai a aikinsa to aikinsa ya rushe".

Girman kai, shi ne qin gaskiya da ganin ka fifiko akan jama'a, saboda jiji-da-kai. Shi ma yana daga cikin shirka ta zuci mai rushe ikhlasi mai vata aiki. Domin ba neman kusancin da Allah ya sa shi aikin ba. A'a yana aikin ibadar ne domin biyan wata buqata ta karankansa. Da kuma qoqarin nuna ya fi kowa, da wulaqanta mutane.

Wanda duk zai aikata aikin ibada don Allah ya ba shi aljannah, ya tsirar da shi daga wuta wannan ba ya kure ikhlasi.

Bayyana aikin ibada na fili, da voye savon Allah, wannan ba ya yiwa ikhlasi tangarxa. Shari'a ma haka ta fi so. Don haka ba a hana aikata wani aki wanda shari'a ta amince a aikata shi, wai don tsoron riya. A'a za a yi umarni ne da aikata shi tare da yin ikhlasi a cikinsa.

Godewa mutum a kan wani aiki da ya yi domin Allah, ba ya lalata masa aikinsa. Wannan yana daga cikin ribar qafa. An karvo daga Abu Zarr, ya ce, "An ce da manzon Allah, menene matsayin wanda ya yi aikin alheri, sai mutane suka yi ta yabonsa? Sai manzon Allah ya ce, "Wannan yana daga cikin bushara ta gaggawa ga mumini. Muslim ne ya rawaito.

Abubuwan da suke biyo bayan aiki na ibada, kuma waxanda Allah ya halatta, tare da samuwar ikhlasi da kasancewar bawa ya yi aikinsa na ibada tun farko domin Allah, to waxannan abubuwa da za su samu ba sa rushe ikhlasi. Kamar mutum ya je hajji ya haxa da kasuwanci, ko ya sa da zumunci don Allah ya yalwata masa arzikinsa. Ko ba shi da lafiya ya yi sadaka don Allah ya ba sauqi. Duk waxannan abubuwa ba sa cin karo da ikhlasi.

Haxa wata ibada da wata, wannan baya kore ikhlasi. Kamar mutumin da zai yi azumi da niyar neman lada da kuma karya sha'awarsa. Wannan abu ne ma mai kyau a shari'a.

Yin kwalliya don zuwa wajen ibada da haxuwa da jama'a, wannan shi ma ba ya kore ikhlasi.

Amma da mutum zai riqa yin abin da bai kamata ba a bainar jama'a da hujjar wai don kada a zarge shi da riya. Wannan kwata-kwata ba daidai ba ne.

Yin xa’a ko qarawa a kan abin da aka saba lokacin da aka ga masu ibada don koyi da su, wannan bai zama laifi ba, kuma ma ba shi alaqa da riya ko kaxan. Yana daga cikin albarkar zama da mutanen kirki. Matuqar dai bawa ya yi aikinsa don Allah.

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Na shai da babu abin bauta da gaskiya sai Allah shi kaxai. Kuma na shaida lalle Annabi Muhammadu bawan Allah ne kuma manzonsa. Allah ya qara tsira a gare shi da sahabbansada alayensa bikixaya. Da duk waxanda suka bi su da kyautatawa har zuwa ranar qiyama.

Bayan haka:

Yaku musulmai! Kamar yadda muka yi bayani a baya cewa, ikhlasi yakan cutu da wasu abubuwa, kamar jiji-da-kai, da neman sakamako na duniya akai aikin ibada. To duk wani abu da zai zama cikas ga ikhlasi to shari’a ta tanadin maganinsa.

Maganin jiji-da-kai shi ne mutum ya riqa ganin baiwar da Allah ya yi masa da falalar da ya yi gare shi. Kuma duk wani abu da zai aikat to daga falalar Allah ne. Allah yana cewa:

(وَلَوْلَا فَضْلُ اللَّهِ عَلَيْكُمْ وَرَحْمَتُهُ مَا زَكَا مِنْكُمْ مِنْ أَحَدٍ أَبَدًا) [النور: ٢١].

(Ba domin falalar Allah gare ku ba da rahamarsa, to babu wani daga cikinku da zai tsarkaka har abada. Sai dai Allah shi ne yake tsarkake wanda ya so).

Hakanan maganin neman abin duniya akan aikin xa’a, wanda yin haka yana cutar da ikhlasi, shi ne, bawa ya san fa cewa shi tsantsar bawa ne ga Allah. Don haka don ya yi wa Ubangijinsa hidima ba zai ce, haqqi ne akan Ubangijinsa sai lalle ya biya shi. Duk abin da Ubangiji zai ba shi na sakamako falala ce ta Allah gare shi.

Kamar yadda yana daga cikin abubuwa da suke cutar da ikhlasin bawa, idan ya yi wani aiki ya riqa jin ya gama gamsuwa da aikin da ya yi. Magnanin irin wannan lamari abu biyu ne:

Na farko: Ya riqa hango gajiyawarsa, da kasawarsa, ya kuma gane cewa akwai nasibin shaixan da son zuciya a tattare da shi. Duk qarancin aiki da wuya ne ka samu shaixan ba shi da wani nasibi a cikinsa. An tambayi Manzon Allah game da waiwaye a sallah, sai ya ce, «Wani abu ne da shaixan yake sata daga sallar bawa». Ka ga fa wannan waiwaye ni kaxan ya yi da idonsa, amma ga abin da ya kasance. To ina ga wanda zuciyarsa ce zai ta waiwayi wanin Allah?!

Hanyar magani ta biyu: Ita ce, bawa ya san cewa Allah yana da haqqoqi diyawa akansa saboda kasancewar bawan Allah ne. Kuma bawa bai isa ya ce, zai biya Allah duk haqqoqinsa da suke kansa. To don me ba zai ji kunyar zuwa ga Allah da xan aikinsa ba. Don haka wajibi ne ya riqa tuhumar kansa akai-akai. Duk bawan da ba ya tuhumar kansa akai-akai to wannan jahili ne, mai ruxar kansa.

Bayin Allah!

Akwai wasu abubuwa da za su taimaka bawa wajen ikhlasinsa bayan taimakon Allah. Waxannan abubuwa kuwa su ne:

Bawa ya sa Allah a zuciyarsa koda yaushe. Ya yi aikinsa domin shi. Ya riqa neman agajinsa yana cewa: «Ya Hayyu Ya qayyum, bi rahmatika Astagith”.

Abu na biyu mutum ya san cewa, mutane ba sa amfanarwa kuma ba sa cutarwa. Don haka mu ma daina kawo su a tunaninmu yayin da muka wata ibada.

Bawa ya guji zuciyarsa mai umartar sa da mummunan aiki. Wacce take neman girma da fariya, da girma da yabo, da wulaqanta mutane, da nuna musu girman kai, da yi musu izgili.

Mu guji shaixan la’ananne. Ka mu sake ya biy mana ta inda ba ma tsammani. Kamar wajen hira, ko alfahari, ko nuna kishi ga addini. Ko lokacin da mutane za su riqa yabonsa suna nu sha’awarsu da abin da yake yi.

Yaku bayin Allah!

Ku riqa halarto da Allah yayin ayyukanku. Ku sanya sirrinku ya zama ma fi tsarkaka daga zahirinku. Ku sani Allah ya san asiran bayinsa, babu wani abu da yake vuye masa a sama ko a qasa. Mu Karnta faxar Allah da yake cewa:

(وَمَا تَكُونُ فِي شَأْنٍ وَمَا تَتْلُو مِنْهُ مِنْ قُرْآَنٍ وَلَا تَعْمَلُونَ مِنْ عَمَلٍ إِلَّا كُنَّا عَلَيْكُمْ شُهُودًا إِذْ تُفِيضُونَ فِيهِ وَمَا يَعْزُبُ عَنْ رَبِّكَ مِنْ مِثْقَالِ ذَرَّةٍ فِي الْأَرْضِ وَلَا فِي السَّمَاءِ وَلَا أَصْغَرَ مِنْ ذَلِكَ وَلَا أَكْبَرَ إِلَّا فِي كِتَابٍ مُبِينٍ) [يونس: 61]

(Babu wani sha’ani da za ka kasance a cikinsa. Kuma babu wani abu da kake karantawa na al’qur’ani, ko wani aiki da kuke yi face mun zamo muna halarce lokacin da kuke aikata shi. Kum babu wani da yake vuya ga Ubangijinka a qasa yake ko a sama, ko mafi qanqanta daga haka, ko mafi girma face yana cikin littafi mabayyani).





Tags:




Mahir Al-mu'ayqaly