Bikin idin karamar sallah


5635
Surantawa
idi a musulunci yana da manufa mai girma, da karamci da cikakken amfani, da maslaha ta duniya da lahira. Musulunci yana da idi guda biyu. Idin qaramar sallah da idin babbar sallah. Kuma dukkansu suna zuwa ne bayan wata ibada mai girma, kuma a bayan wani rukuni daga cikin rukunan musulunci, kuma akan yi shi a mafificin lokaci.

Manufofin huxubar

Bayanin cewa kowace al’umma tana da idi, da banbance idin musulmi.

Amfanunnukan idi.

Bayanin dacewar fitar mata zuwa idi a shari’ance.

Zaburarwa ga ayyukan kirki, da tsoratarwa game da zunubai.

Bayanin sunnoni da ladubban idi.

Falalar azumtar shida ga watan Shawwal.

Huxuba Ta Farko

Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma muna neman tsarinsa daga shirrin kawukanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar da shi, wanda kuma ya vatar to babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaxai ne ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi Muhammad bawansa ne manzonsa ne. (Ya ku waxanda suka yi imani ku ji tsoron yadda ya cancaci a ji tsoronsa, kada ku mutu face kuna musulmi). (Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicceku daga rai guda xaya, kuma ya ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga garesu (su biyu). Ku ji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya da shi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Ya ku wanxanda suka yi imani ku ku ji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku ayyukanku, kuma ya gafarta muku zunubbanku. Wanda ya bi Allah da Manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawon shiriya shiriyar Annab Muhammad (ﷺ). Kuma mafi shirrin al'amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wani qagaggen abu (addini) bidi'a ce, duk wata bidi'a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta.

Bayan haka:

Ku ji tsoron Allah ya ku musulmai haqiqanin jin tsoron Allah, ku yi riqo da igiya qaqqarfa ta musulunci, ku nemi yardar Ubangijinku ta hanyar yi masa xa’a, haka nan ku guji fushinsa ta hanyar barin sava masa.

Ya ku musulmai! Lallai ne kowace al’umma tana da biki (idi), wanda yake maimaituwa a gare su a wasu lokuta kevantattu. Idin yakan qunshi aqidojinsu da al’adunsu da abubuwan da suka gada da abubuwan da suke so, da burace-buracensu. Kowace al’umma tana da matuqar farin ciki a idinta, takan kuma yi farin ciki da haxuwar da ake yi, haka nan sukan girmama lokacin, kuma su zavi guri mai tsari, sannan su sanya kaya sababbi, sukan yi kwalliya da kaya iri-iri. Haka nan Allah Ya qaddarawa kowace al’umma, har al’ummomin jahiliyya, bukukuwa daban-daban, domin zama fitina a gare su da kuma qari a kan vatansu, kamar yadda Allah maxaukaki yake cewa:

وَلَا يَحْسَبَنَّ الَّذِينَ كَفَرُوا أَنَّمَا نُمْلِي لَهُمْ خَيْرٌ لِأَنْفُسِهِمْ إِنَّمَا نُمْلِي لَهُمْ لِيَزْدَادُوا إِثْمًا وَلَهُمْ عَذَابٌ مُهِينٌ [آل عمران: 178]

(Kuma kada waxanda suka kafirta su yi zaton cewa lallai ne jinkirin da Muke yi musu alheri ne ga rayukansu. Muna yi musu jinkirin ne domin su qara laifi kawai, kuma suna da azaba mai wulaqantarwa).

Hakanan Allah yana faxa:

( لِكُلِّ أُمَّةٍ جَعَلْنَا مَنْسَكًا هُمْ نَاسِكُوهُ ) [الحج: 67] .

(Ga kowace al’umma Mun sanya wurin yanka, su ne masu yin baiko gare shi…..).

Xan Abbas Allah Ya yarda da su ya ce, (Almansak- wurin baiko - yana nufin idi). An karvo hadisi daga Anas, Allah ya yarda da shi, ya ce: manzon Allah ya iso Madina kuma muna da ranaku biyu da muke wasa a cikinsu sai ya ce: “lallai Allah ya musanya muku da abin da ya fi su alkhairi (su ne) idin qaramar sallah da idin babbar sallah».

Bukukuwan sauran al’ummomi waxanda ba na musulunci ba, bukukuwa ne na jahiliyya da suke cike da vata, ba su da wata manufa managarciya da maslaha ta duniya da lahira, babu maganar tausayi ko jin qai a ciki, kamar yadda Allah Maxaukaki yake cewa,

( وَمَنْ يَبْتَغِ غَيْرَ الْإِسْلَامِ دِينًا فَلَنْ يُقْبَلَ مِنْهُ وَهُوَ فِي الْآَخِرَةِ مِنَ الْخَاسِرِينَ 85 ) [آل عمران: 85]

(Kuma wanda ya nemi wanin Musulunci ya zama addini, to, ba za a karva daga gare shi ba. Kuma shi a lahira yana daga cikin masu hasara).

Amma idi a musulunci yana da manufa mai girma, da karamci da cikakken amfani, da maslaha ta duniya da lahira. Musulunci yana da idi guda biyu. Idin qaramar sallah da idin babbar sallah. Kuma dukkansu suna zuwa ne bayan wata ibada mai girma, kuma a bayan wani rukuni daga cikin rukunan musulunci, kuma akan yi shi a mafificin lokaci. Idin babbar sallah yakan kasance a qarshen tsayuwar Arfa, kuma yakan kasance a ranar Alhajjul Akbar (wato goma ga zulhijja). Idin qaramar sallah kuwa yakan kasance bayan an gama azumin watan Ramadan. Haka kuma sukan kasance bayan qoqari da dagewa a ayyukan ibada da yawaita xa’a, a cikin ranaku da darare masu xaukaka da falala, da kuma wasu sa’o’i masu albarka da ake ninninka lada, kuma musulmi yake tsoron uquba a cikinsu. Musulmi sukan yi rigegeniya a wannan lokaci, sukan ribaci waxannan sa’o’i da ayyuka na gari. Sukan yi iya bakin qoqarinsu wajen bautar Ubangijinsu da yi masa biyayya, har sai yayin da ruhin xan adam ya sami abin da take so, ta qoshi da abincinta, sanna kuma gajiya ta fara rufe ta; qarfi ya fara qarewa, sai Allah Ta’ala ya buxewa bawansa wata qofa ta samin hutu, da shaqatawa, domin a samu kalamar tarbiyyar jiki da ta ruhi, duk domin mutum ya iya shirin tinkarar sauran ibadu.

Ya tabbata a cikin hadisi daga manzon Allah (ﷺ): “Lallai Ubangijinka yana da haqqi a kanka, kuma jikinka yana da haqqi a kanka, lallai matarka tana da haqqi a kanka, kuma masu ziyararka suna da haqqi a kanka, don haka ka ba wa kowane mai haqqi haqqinsa”

Wani daga cikin magabata yana cewa: “Ku dinga hutar da qwaqwalenku a wasu lokuta domin su ma suna gajiya kamar yadda jiki yake gajiya”

Addinin musulunci yakan bi mutum musulmi a hankali kuma mataki-mataki, daga nan zuwa can, daga wannan yanayi zuwa wani yanayin, daga abu kyakkyawa zuwa wanda ya fi shi kyau, domin ya jadda masa rayuwarssa da karsashinsa, don ya iya cimma abin da zai amfane shi, ya dace da kowane irin alheri.

Haka nan, idi yana daga cikin alamomin musulunci na zahiri, kuma ina cike da hikimomi da amfani iri-iri, ta fuskar aqida, da ibada da amfaninsa a shari’a, kuma amfaninsa a wurin zamantakewar al’umma, da kuma amfaninsa a duniya da lahira.

Ya bayin Allah!

Dangane da amfanin idi ta fuskar aqida: lallai hukunce-hukuncen idi suna nanata kaxaitar Allah ga bayinSa da wajabcin bauta masa shi kaxai ba tare da abokin tarayya ba. Da abin da ya qunsa na addu’o’i da girmamawa da miqa wuya da sallamawa da soyayya, da makamantan haka na abubuwan da suke kasance haqqin Allah ne shi kaxai. Allah yana cewa:

Ma'ana: (Kuma lallai ne wuraren sujuda na Allah ne, saboda haka kada ku kira kowa tare da Allah ( a cikinsu) ).

Amfanin Idi kuwa ta vangaren ibada: Haqiqa koyarwar idi, tana tabbatar da bauta ga Allah ubangijin talikai, ta yadda qanqan da kai da saduda suke tabbata ga Allah gami da soyayya. Haka nan jigon ibada yana komawa ne zuwa ga soyayya don Allah saduda domin Allah da tsoro don Allah. Wani daga cikin magabata yana cewa: (wanda ya bauta wa Allah da tsoro kawai to wannan xan Khawarij ne, wanda kuma ya bauta wa Allah da soyayya kawai, wannan zindiqi ne, wanda kuma ya bauta wa Allah da saduda da tsoro da soyayya, to wannan shi ne cikakken mai bauta), Allah maxaukakin sarki yana cewa,

( إِنَّهُمْ كَانُوا يُسَارِعُونَ فِي الْخَيْرَاتِ وَيَدْعُونَنَا رَغَبًا وَرَهَبًا وَكَانُوا لَنَا خَاشِعِينَ 90 ) [الأنبياء: 90]

(Lallai ne su sun kasance suna tserereniya zuwa ga ayyukan alheri. Kuma suna kiranmu a kan kwaxayi da fargaba. Kuma sun kasance masu qin aikata savo gare mu).

Dangane da amfanin idi kuwa ta fuskar shari’a, Idi yana qunshe da bayyana farillan addinin musulunci da alamomin addini da yayata koyarwar addini, da sanar da shari’o’in imani, domin addinin musulunci ya ci gaba da zama a tsare kuma mai qarfi mai kariya ta yadda ba zai rusu ba. Sannan ta yadda masu qoqarin jirkita shi da lalata shi ba za su iya ci nasara ba, domin addinin musulunci qaqqarfa ne ta hanyar shari’o’insa. Ya dace da halittar xan Adam. Haka nan koyarwar hukunce-hukuncen addinin musulunci takan kasance mai sauqi ga babba da qarami da namiji da mace da na kusa da na nesa.

Rukunan addinin musulunci a fili suke, sannan iyakokinsa sanannu ne a fili suke, haka nan koyarwarsa da hukunce-hukuncensa sun watsu ko’ina, kuma addini ne na duniya baki xaya. Allah maxaukakin sarki yana cewa,

( فَأَقِمْ وَجْهَكَ لِلدِّينِ حَنِيفًا فِطْرَةَ اللَّهِ الَّتِي فَطَرَ النَّاسَ عَلَيْهَا لَا تَبْدِيلَ لِخَلْقِ اللَّهِ ذَلِكَ الدِّينُ الْقَيِّمُ وَلَكِنَّ أَكْثَرَ النَّاسِ لَا يَعْلَمُونَ 30 ) [الروم: 30]

(Saboda haka ka tsayar da fuskarka ga addini, kana mai karkata zuwa ga gaskiya, halittar Allah da Ya halitta mutane a kanta. Babu musanyawa ga halittar Allah. Wannan shi ne addini maidaidaici, kuma amma mafi yawan mutane ba su sani ba).

Kuma saboda wannan qarfin da yake da shi, wannan yakan qara wa addinin kyau, kuma yakan qara faxaxa, yakan tabbata ba tare da raurawa ba. Ya , kuma kamar haskenta yake a wajen kusantowarsa. Ya zama kamar rana wajen xaukakarsa, wanda ya mame kowa da haskensa Godiya ta tabbata ga Allah da ya sanya mu muka zama musulmai. Shi ne addinin adalci da aminci da nutsuwa da sa’ada, shi ne addinin ‘yan uwantaka, addinin alkhairi. Addinin da ke kwaxaitarwa ga dukkanin wani alheri, yake hani ga barin kowane sharri.

Amma amfanin idi a rayuwar al’umma gava xaya, shi ne yakan tabbar da haxin kai da haxuwar zuciya tsakanin musulmai, da kawar da duk wani barin gutsuri tsoma da fushi da qullata. Akan sami cikar jin qai da rahama da ziyarce-ziyarce, yanke zumunci yakan qare. Akan yi musayar abubuwa masu amfani. Ya zo a cikin hadisi: (kwatankwacin musulmai a cikin soyayyarsu da jin qansu da tausayinsu kamar jiki ne guda, idan wani sashe ya kamu da rashin lafiya, dukkanin sauran jiki ma sai ya karva da rashin barci da zazzavi). Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.

Daga cikin amfanin idi da hikimominsa da manufofinsa shi ne yaddyyana buqatarsu wajen ubangijinsu, ba kuma za su iya wadatuwa daga taimakonsa ba daidai da qiftawar ido. Sukan yi tawasulli zuwa ga Allah domin ya biya musu buqatunsu da gyara musu al’amuransu ta hanyar sallar idi a cikin jam’i, da jin ambaton Allah da ni’imomin Allah da falalolinsa. Haka nan da sanin hukunce-hukuncen addinin musulunci a huxuba. Wannan ya sa su sami alheri mai girma da gamammiyar falala wadda al’ummomin da suka gabace su ba su samu irin wannan ba. Don haka godiya ta tabbata ga Allah a bisa gamewar ni’imarsa da xaukakar karamcinsa.

Ya ku bayin Allah, saboda garavasar wannan idi, da kuma abin da ya tattara na rahama da albarka, sai Manzon tsira (ﷺ) ya yi umar da a fita zuwa gare shi, hatta mata masu haila da 'yan mata, amma ba tare da sun yi fitar nuna tsiraici da sanya turare da nuna kwalliya ba, duk domin su sami wannan alherin. Daga Umm Axiyyah, Allah ya yarda da ita tana cewa: “Manzon Allah (ﷺ) ya umarce mu da mu fito da 'yammata, da masu haila a yayin idin qaramar salla da babba, amma su masu haila sai su nisanci wurin sallah, su ma su sami alheri, su kuma saurari addu’o’in musulmai. Sai na ce, "Ya manzon Allah, xayarmu ba ta da abin da za ta rufe jikinta". Sai ya ce, "‘Yar uwarta ta ara mata nata abin rufe jikin". Bukhari da Muslim ne suka rawaito.

A wata ruwayar ta Bukhari ta ce: “Mun kasance ana umartarmu da fita a ranakun idi har akan umarci ‘yan mata su fita daga wuraren da suke zaune, har mai haila, sai su dinga yin kabbara idan musulmai sun yi kabbara, kuma su dinga yin addu’a idan sun yi addu’a, suna fatan albarkar wannan rana da tsarkinta.

Allah Akbar Allah Akbar Allah Akbar, La’ilaha illallah, wallahu akbar Allah Akbar, walillahil hamdu.

Ya ku bayin Allah, ku yi riqo da sallah domin ita ce jigon addini, kuma mai hani ce daga alfasha da zunubai, ku tsayar da ita a cikin gidajen Allah kuma a cikin jam’i, domin ita ce abu na farko da za a tambayi bawa a kansa ranar alqiyama, idan aka karve ta, to sai a karve ta da sauran ayyukan, idan kuma aka mayar da ita, to sai a mayar da ita da sauran ayyukan.

Ku fitar da zakkar dukiyoyinku wadda za ta tsarkake zukatanku, dukkan wanda ya fitar da ita yana tare da albarka, kuma akwai busharar lada a gare shi. Haka nan duk wanda ya yi rowa game da zakkarsa to an toshe albarkar dukiyarsa kuma azaba mai raxaxi da uquba za su tabbata a gare shi.

Ku azumci watan azumi, ku yi aikin hajii ga xakin Allah mai tsarki, za ku shiga aljanna tare da aminci. Hakanan ku riqi yin biyayya ga iyaye da kuma sadar da zumunci. Domin haqiqa duk wanda ya yi riqo da wannan ya tsira. Ku kyautata kula da matanku na aure da ‘ya’yanku da masu yi muku hidima da duk wanda Allah ya damqa al’amarinsa a hannunku. Ku kula da haqqoqinsu, kuma ku tafi da su a kan abin da zai amfane su, ku guji abin da zai cutar da su. Ubangiji maxaukakin sarki yana cewa,

( يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا قُوا أَنْفُسَكُمْ وَأَهْلِيكُمْ نَارًا وَقُودُهَا النَّاسُ وَالْحِجَارَةُ عَلَيْهَا مَلَائِكَةٌ غِلَاظٌ شِدَادٌ لَا يَعْصُونَ اللَّهَ مَا أَمَرَهُمْ وَيَفْعَلُونَ مَا يُؤْمَرُونَ 6 ) [التحريم: 6]

(Ya ku waxanda suka yi imani, ku kare kawunanku da iyalinku daga shiga wuta, makamashinta mutane da duwatsu ne. Masu gadinta waxansu mala’iku ne kaushi, masu qarfi. Ba su savawa Allah ga abin da Ya umarce su, kuma suna aikata abinda aka umarninsu).

Hakanan ya zo a cikin hadisi: “Kowannenku mai kiwo ne, kuma kowannenku abin tambaya ne game da abin da aka ba shi kiyo». Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi, daga Ibn Umar.

Allah Akbar Allah! Akbar Allah Akbar! La’ilaha illallah, wallahu akbar Allah Akbar, walillahil hamd.

Ya ku musulmai, ku kiyayi yin tarayya da Allah maxaukakin sarki a wajen addu’a ko neman taimako ko neman agaji, ko yanka ko bakance ko tawakkali, ko wani abu makamancin wannan daga cikin nau’ikan ibadu waxanda ake yin su domin Ubangijin talikai kawai. Duk wanda ya yi shirka da Allah a cikin bautarsa, haqiqa Allah ya haramta masa aljanna. Ubangiji maxaukakin sarki yana cewa:

( إِنَّهُ مَنْ يُشْرِكْ بِاللَّهِ فَقَدْ حَرَّمَ اللَّهُ عَلَيْهِ الْجَنَّةَ وَمَأْوَاهُ النَّارُ وَمَا لِلظَّالِمِينَ مِنْ أَنْصَار 72 ) [المائدة: 72]

(Lalle duk wanda ya yi tarayya da Allah, to haqiqa Allah ya haramta masa aljanna, kuma makomarsa wuta ce, kuma azzalumai ba su da wasu mataimaka.)

Ku guji kashe rai wadda Allah ya haramta, domin ya zo a cikin Sahihil Bukhari daga hadisin Xan Umar, Allah ya yarda da su ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Bawa ba zai gushe ba yana zaman lafiya da addininsa matuqar dai bai zubar da jinin da aka haramta ba”.

Haka nan ku guji riba, domin riba tana gadar da fushin Ubangiji, kuma tana cinye albarkar dukiya da kwanaki, ku guji zina, domin zina bala’i ce mai kai mutum wuta. Ubangiji maxaukakin sarki yana cewa:

( وَلَا تَقْرَبُوا الزِّنَا إِنَّهُ كَانَ فَاحِشَةً وَسَاءَ سَبِيلًا 32 ) [الإسراء: 32]

(Kuma kada ku kusanci zina. Lallai ne ita ta kasance alfasha ce, Kuma hanyarta ta yi muni qwarai).

Kuma ku guji irin aikin Mutanen Annabi Lux, domin Allah ya la’anci wanda yake aikata wannan, kuma manzon Allah ya la’anci mai aikata hakan. An karvo daga Xan Abbas, Allah ya qara musu yarda ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce “Allah ya la’anci wanda yake aikata aikin mutanen Annabi Lux, Allah ya la’anci wanda yake aikata aikin mutanen annabi Lux, Allah ya la’anci wanda yake aikata aikin mutanen annabin Lux”. Imam Ahmad da Hakim ne suka ruwaito shi.

Haka nan ina gargaxinku ku guji kayan maye masu gusar da hankali, domin su fitina ce mai halakarwa, kuma suna gadar da fushin Ubangiji, kuma sukan nuna mutum a wata irin sifa, wadda zai dinga ganin abu mai kyau a matsayin mummuna, mummuna a matsayin mai kyau.

An karvo daga Jabir, daga manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Duk wani abu mai sa maye haramun ne, kuma lallai akwai Allah ya yi alqawari ga duk mai shan abin maye cewa zai shayar da shi daga ruwan gulandon ‘yan wuta”. Imam Muslim da Nasa’i ne suka rawaito shi.

Ku guji dukiyar musulmai da kuma zaluntarsu. Duk wanda ya yanki taqi xaya na qasa ba tare da haqqi ba, Allah zai yi misa 'yar wuya da qassai bakwai.

Ku guji dukiyar marayu da miskinai. Domin wannan yana jawo talauci da lalacewa, da uquba ta gaggawa.

Ku guji yin qazafi ga mata masu kamun kai, domin wannan yana daga abubuwa masu halakarwa.

Ku guji yin giba da annamimanci, domin wannan zalunci ne ga musulmi, kuma savo ne mai tafiyar da ayyukan qwarai ga mai yi, kuma Allah ya haramta hakan a cikin Alqur’ani.

Ku guji jan kaya a qasa da alfahari da taqama, domin Abu Huraira Allah ya qara yarda a gare shi ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Duk abin da ya wuce idon sawu na daga izari to yana cikin wuta”. Bukhari ne ya ruwaito shi.

Ya ku taron mata ku ji tsoron Allah, ku yi xa’a ga Allah da manzonSa. Ku kiyaye sallolinku, kuma ku yi xa’a ga mazajen aurenku, ku kula da haqqoqinsu, ku kyautata zama da maqota, kuma ku lura da tarbiyyar ‘ya’yanku ta hanyar tarbiyyar musulunci da riqo da amana.

Don haka ku guji nuna tsaraici da rashin kamun kai da cakuxexeniya da maza, ku yi riqo da sutura da kamewa, za ku kasance daga cikin masu rabauta, kuma za ku shiga aljanna tare da mata na qwari, kuma Ubangijin sammai da qassai zai yarda da ku.

Daga Abdurrahman xan Auf, Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Idan mace ta sallaci sallolinta guda biyar, kuma ta azumci watanta, kuma ta kiyaye farjinta, kuma ta yi biyayya ga mijinta, za a ce mata: ki shiga aljanna daga kowace qofa da kike so”. Imam Ahmad da Xabarani ne suka rawaito.

Haka nan, an karvo daga xan Abbas Allah ya yarda da su ya ce: “na halarci sallar idin qaramar sallah tare da manzon Allah (ﷺ) sai ya je wajen mata tare da Bilal, sai ya karanta masu faxar Allah:

( يَا أَيُّهَا النَّبِيُّ إِذَا جَاءَكَ الْمُؤْمِنَاتُ يُبَايِعْنَكَ عَلَى أَنْ لَا يُشْرِكْنَ بِاللَّهِ شَيْئًا وَلَا يَسْرِقْنَ وَلَا يَزْنِينَ وَلَا يَقْتُلْنَ أَوْلَادَهُنَّ وَلَا يَأْتِينَ بِبُهْتَانٍ يَفْتَرِينَهُ بَيْنَ أَيْدِيهِنَّ وَأَرْجُلِهِنَّ وَلَا يَعْصِينَكَ فِي مَعْرُوفٍ فَبَايِعْهُنَّ وَاسْتَغْفِرْ لَهُنَّ اللَّهَ إِنَّ اللَّهَ غَفُورٌ رَحِيمٌ 12 ) [الممتحنة: 12]

.

(Ya kai wannan Annabi! Idan mata muminai suka zo maka suna yi maka mubaya’a a kan ba za su yi shirka da Allah ba ga komai, kuma ba za su yi sata ba, kuma ba za su yi zina ba, kuma ba za su kashe ‘ya’yansu ba, kuma ba za su zo da qarya da suke qiqirarta daga tsakanin hannuwansu da qafafunsu, kuma ba za su sava maka ga wani abu da aka sani na shari’a ba, to, ka karvi mubaya’arsu, kuma ka nemi Allah ya gafarta musu. Lallai Allah Mai gafara ne Mai jinqai). Sai ya ce: (kun yarda da wannan), wata mata ta ce: Na’am ya manzon Allah.

Imam Ahmad ya rawaito cewa, Umamata Bint Ruqayya ta yi wa manzon Allah mubaya’a a kan wannan ayar. A cikinsa kuma akwai faxar cewa “Kada ku riqa rusa kuka don mutuwa, kuma kada ku yi fitar qyale-qyale, irin fitar qyale-qyalen jahiliyya”.

Ma’anar: “ kuma ba za su zo da qarya da suke qiqirarta daga tsakanin hannuwansu da qafafunsu” shi ne ka da su zo da wasu ‘ya’ya da ba na mazajensu ba su ce na su ne.

Allah Akbar Allah Akbar Allah Akbar, La’ilaha illallah, wallahu akbar Allah Akbar, walillahil hamdu.

Bismillahi Rahmanir Rahim. Allah yana cewa:

( وَإِذَا قُرِئَ الْقُرْآَنُ فَاسْتَمِعُوا لَهُ وَأَنْصِتُوا لَعَلَّكُمْ تُرْحَمُونَ 204 ) [الأعراف: 204]

(Kuma idan an karanta Alqur’ani sai ku saurare shi, kuma ku yi shiru, La’alla ko kwa samu rahama).

Allah ya yi albarka gare ni da ku a cikin Alqur’ani mai girma, ya amfane ni da ku daga abin da yake cikinsa na ayoyi da tuntuntuni na hikima, kuma ya amfane mu da koyarwar shugaban mursalai, da maganarsa daidaitacciya. Abin da zan faxa ke nan. Ina neman gafarar Allah mai girma gare ne da ku da sauran musulmai daga kowane zunubi, ku nemi gafararsa domin Shi Mai yawan gafara ne Mai yawan rahama.

Huxuba Ta Biyu

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, kyakkyawan qarshe yana ga masu tsoron Allah, babu tavewa sai ga azzalumai, da tsira da aminci bisa cikamakin annabawa, Annabi Muhammad sallallahu alaihi wasallam. Bayana haka:

Allah Akbar! Allah Akbar!! Allah Akbar!!! La’ilaha illallah, wallahu akbar, Allah Akbar, walillahil hamdu.

Allahu Akbar kwatankwacin adadin abin da ya halitta a sama. Allahu Akbar kwatankwacin adadin abin da ya halitta a qasa. Allahu Akbar kwatankwacin adadin abin da ke tsakanin waxannan. Allahu Akbar kwatankwacin adadin komai, Allahu Akbar kwatankwacin cikar komai, Allahu Akbar kwatankwacin abin da littafi ya qididdige.

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin sammai da qassai, mai jivintar al’amarin komai, mai amsa addu’o’i, yakan karvi tuba daga bayinsa kuma yakan yi afuwa daga munanan ayyuka. Ba wani abu da ya fi qarfin Allah ya yi kauta da shi. afuwarsa ba ta tawaya domin ya yi yafiya ga manyan zunubai. Ina godewa Ubangijina a bisa kyawawan ni’imominsa da ba sa yankewa a wani lokaci daga cikin lokuta. Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya bisa cancanta sai Allah, Shi kaxai ba shi da abokin tarayya, yana da sunaye mafiya kyau, da siffofi masu girma. Haka nan ina shaidawa cewa manzonmu, kuma shugabanmu Annabi Muhammad, bawanSa ne kuma manzonSa ne, wanda aka aiko shi da bayyanannun hujjoji. Ya Allah Ka qara daxin tsira da aminci da albarka a kan bawanka kuma manzonka, Annabi Muhammad, da iyalansa da sahabbansa, kyawawan shuwagabanni.

Ku ji tsoron Allah ya ku musulmai, ku yi masa xa’a, ku nemi yardarsa kuma kar ku sava masa. Ya ku musulmai, lallai wannan idin naku idi ne mai karamci, kuma taro ne mai girma. Allah yakan sanya alheri da dama a cikinsa ga al’ummar muslmai. Haka kuma Ubangijinmu ya shar’anta wasu hukunce-hukunce a wannan Idi. Hakanan Annabi (ﷺ) ya sunnanta sunnoni a cikinsa:

Allah ya shar’anta yin wanka kafin a fita sallar Idi. Kuma babu laifi idan mutum ya yi wanka tun kafin alfijir ya keto Idan har yin hakan ya fi masa sauqi. Haka nan an sunnanta yin kwalliya da kaya masu kyau. Ya zo a cikin hadisi; “lallai Allah yayin da ya yi wata ni’ima ga bawa, Yana son ya ga vurvushin wannan ni’imar tare da shi”. Ibn Sa'ad da Xahawi ne suka ruwaito shi.

Kuma sunna ce yin asuwaki da sanya turare, da aske gashin baki da kuma yanke farce. Amma kar mutum ya kuskura ya aske gemunsa, domin yin hakan haramun ne.

Har ila yau, an sunnanta mutum ya fara cin dabino kafin cin komai. Sannan kuma mutum ya sauya hanyar da yi bi a yayin zuwa yayin komawa. Sannan bayan haka, an sunnanta bayyana kabarbari a daren idi, kuma musulmi su bayyana kabarbarinsu a yayin fita zuwa wajen yin salla har sai liman ya fara huxuba, sai ya ce:

Allah Akbar Allah Akbar Allah Akbar, La’ilaha illallah, wallahu akbar Allah Akbar, walillahil hamdu.

Yana daga cikin hikimar yin kabarbari shi ne girmama Ubangiji da kuma turbuxe hancin shaixan da qasqantar da shi, da wulaqanta shi. Da kuma bayyana cewa musulmi ya fi qarfin zuciyarsa da wani kwaxayi na duniya, da bayanin cewa lallai Allah shi ne ya fi komai girma da xaukaka a zuciyar musulmi.! Allah maxaukakin sarki yana cewa:

( وَلِتُكْمِلُوا الْعِدَّةَ وَلِتُكَبِّرُوا اللَّهَ عَلَى مَا هَدَاكُمْ وَلَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ 185 ) [البقرة: 185]

(… Kuma domin ku cika adadin, kuma domin ku girmama Allah a kan ya shiryar da ku, kuma tsammaninku, za ku gode).

Ya ku musulmai! Abu Dawud da Ibn Majah sun rawaito daga Xan Abbas Allah ya qara yarda a gare su cewa: “Manzon Allah ya farlanta zakkar fid-da-kai domin tsarkake mai azumi daga yasasshen zance da maganganun batsa, sannan kuma ciyarwa ce ga miskinai».

An karvo daga Abu Sa’id Alkhudri ya ce: “Mun kasance muna fitar da zakkar fid-da-kai, sa’i xaya na alkama ko na sha’iri kuma sa’i na dabino ko zabib, ko kuma sa’i na cukwi. Idan ya fitar daga irin abincin da mutancen garinsu suke amfani da shi ya yi daidai.

Wannan zakka ta fid-da-kai, wajibi ce a kan kowane musulmi, namiji ne ko mace, babba ne ko qarami. Kuma an fi son a fitar da ita kafin a tafi sallar idi. Kuma za a yin hakan kafin kwana xaya ko biyu ga idi.

Allah Akbar! Allah Akbar!! Allah Akbar!!! La’ilaha illallah, wallahu akbar, Allah Akbar, walillahil hamd.

Ku ji tsoron Allah ya ku musulmai. Kuma ku sani cewa Shi Mai Shar’antawa Mai Hikima, ya sunnanta muku azumi guda shida na Shawwal, kuma ya sanya hakan ya zama tamkar bibiyar ayyukan kirki ne da wasu ayyukan kirki. Domin manzon Allah (ﷺ) yana cewa: “Duk wanda ya azumci Ramadan, sannan ya bi shi da shida ga Shawwal, ya kasance kamar ya yi azumin shekarar ce gaba xaya.” Muslim ne ya rawaito shi.

Yadda aka yi azumin Ramadan tare da shida na watan shawwal ya zama kamar azumin shekara , shi ne Allah mai girma da xaukaka, yakan ninka dukkanin wani kyakkyawan aiki zuwa ninki goma kwatankwacinsa. Kamar yadda yake a faxar Allah maxaukaki:

( مَنْ جَاءَ بِالْحَسَنَةِ فَلَهُ عَشْرُ أَمْثَالِهَا ( [الأنعام: 160]

“Wanda ya zo da kyakkyawa aiki guda, to, yana da goma xin misalinsa”

Don haka azumin Ramadan akan qirga shi a matsayin an ninka shi kwatankwacin wata goma, shi kuwa azumin shida ga Shawwal akan qirga shi a matsayin kwatankwacin kwana sittin. Da wannan sai a sami kwatankwacin ladan shekara cikakkiya.

Abin da ya fi falala dangane da azumtar waxannan kwana shida na Shawwal shi ne, a yi su da gaggawa bayan ranar idi, kuma yana da kyau a yi su a jere. Amma babu laifi ga wanda ya yi su a rarrabe. Hakan nan ba laif idan mutum ya jinkirta yin su har zuwa tsakiyar watan ko qarshensa. Kuma a sani yin wannan azumi ba wajibi ba ne. Kuma abin da wasu suke zato na cewa duk wanda ya riga ya yi a wata shekara, to wai ya wajaba a kansa duk sauran shekarun, wannan ba haka ba ne, domin yin azumin sunna ne ba wajibi ba. Duk wanda ya yi zai sami lada, wanda kuma ya bari bai yi ba, ba wani abu a kansa. Haka nan duk wanda ya zama yana yin wannan azumin a kowace shekara, sannan sai wata shekarar ya yi rashin lafiya ko kuma tafiya ta kama shi a daidai lokacin yin azumin, to za a rubuta masa ladan azumin, ko da kuwa bai yi ba. Hakan kuma na qarfafa ne da faxin manzon Allah a hadisi ingantacce cewa: “Idan bawa ya yi rashin lafiya ko kuma ya yi tafiya, Allah maxaukakin sarki zai rubuta masa lada misalin abin da ya kasance yana yi a yayin zaman gida”. Bukhari ne ya fitar da shi, da Ahmad, daga Abu Musal Ash’ari, Allah ya yarda da shi.

Haka kuma ba ya halatta a gabatar da azumin shida ga Shawwal alhalin kuma akwai ramuwa a kan mutum, domin yana daga cikin sharaxin samun ladan azumin shidan shi ne ya kasance mutum ya azumci Ramadan gabaxayansa. Da haka ne mutum zai kasance kamar ya azumci shekara gabaxayanta.

Ya bayin Allah, ku godewa Ubangijinku a bisa abin da ya yi muku tagomashi da shi a wannan na zaman lafiya da imani, da kuma lafiyar jiki da yassara arziqi da yalwar rayuwa, da kuma kashe wutar fitintinu. Kuma ni’imar Allah tana dawwama ne ta hanyar godiya gare shi maxaukakin sarki da kuma yi masa xa’a.

Ya bayin Allah, “Lallai Allah da manzonsa suna yin salati ga manzon Allah, ya ku waxanda suka imani ku yi salati a gare shi tare da cikakkiya sallama. Haqiqa, ya ce (sallal lahu alaihi wasallam) “duk wanda ya yi salati a gare ni guda xaya, Allah zai yi masa da guda goma da wannan salatin.” Don haka ku nemi daxin tsira da aminci a bisa ga shugaban na farko da na qarshe. Ya Allah ka yi salati ga annabin Muhammad da iyalan Muhammad kamar yadda ka yi salati ga Ibrahim da iyalan Ibrahim, ka yi daxin albarka ga Muhammad da iyalan Muhammad kamar yadda ka yi albarka ga Ibrahim da iyalan Ibrahim lallai kai ne abin godiya mai yabawa, ka yi daxin tsira da aminci mai yawa.





Tags:




Sunnonin Fixira