Hudubar sabuwar shekara


4612
Surantawa
Ya kai masoyi, ka yi duba zuwa ga shafukan rayuwarka da ta shuxe, mai ka aje a cikinsu domin lahirarka? Ka yi tunani a ranka,:me wannan harshe naka ya faxa? Me kuma idanunka suka kalla? Kunnen nan naka me ya ji? Kuma waxannan qafafuwan naka ina suka je? Ya hannu! Me kika tava? Abin da ake buqata a gurinka shi ne ka riqe linzamin rayuwarka da kanka. Ka yi wa kanka hisabi.

Manufofin huxubar

Bayanin saurin shexuwar shekaru da lokaci.

Bayanin abin da yake wajaba a kan bawa game da hakan.

Wajabcin yi wa kai hisabi, da kuma gaggauta tuba.

Kwaxaitarwa a kan ga amfani dd lokaci ta hanyar ayyukan xa’a

Huxuba Ta Farko

Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma muna neman tsarinsa daga shirrin kawukanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar da shi, wanda kuma ya vatar to babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaxai ne ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi Muhammad bawansa ne manzonsa ne. (Ya ku waxanda suka yi imani ku ji tsoron yadda ya cancaci a ji tsoronsa, kada ku mutu face kuna musulmi). (Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicceku daga rai guda xaya, kuma ya ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga garesu (su biyu). Ku ji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya da shi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Ya ku wanxanda suka yi imani ku ku ji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku ayyukanku, kuma ya gafarta muku zunubbanku. Wanda ya bi Allah da Manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawon shiriya shiriyar Annab Muhammad (ﷺ). Kuma mafi shirrin al'amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wani qagaggen abu (addini) bidi'a ce, duk wata bidi'a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta.

Bayan haka:

Ya ku bayin Allah! A wannan rana muna bankwana da wata shekara, wadda ta riga ta tattara komatsenta. Ba wani abu ne ya rage ba, sai ‘yan awanni kaxan ne suka rage mana mu shiga sabuwar shekara, wadda za ta buxe sabon shafinta. To, me muka shuka wa kanmu kwanakin shekarar da ta wuce, kuma da wane abu ne muka cika shekarar, kuma da me za mu tunkari ita wannan sabuwar shekarar? Wadda ga ta nan dai, ba mu sani ba, shin za mu cikashe, ko kuma za mu kasance daga waxanda suke tafiya zuwa lahira. Dole mu yi wa kawunanmu hisabi. Idan har mun yi ayyuka na qwarai a kwanakin shekararmu da ta wuce, to sai mu godewa Allah. Idan kuma wasa da shirme muka yi, da rashin biyayya ga Allah, to sai mu sauya tunaninmu kuma mu tuba zuwa ga Allah, tuba wadda take ta gaskiya. Domin mafi alherin abin da za mu dinga cika shekarunmu da shi, shi ne mu dinga tuba zuwa ga Allah Ta’ala, a kan abubuwan da muka yi sakaci a kansu na rashin xa'a ga Allah, ko kuma zunuban da muka aikata. Kuma mu godewa Allah da Ya ba mu damar gyara kurakuranmu.

Daga Abi Huraira (R.A), lallai Manzon Allah (ﷺ), ya ce: “Kada xayanku ya yi burin mutuwa, ko dai mai ayyukan kyautatawa ne, wataqila zai qara, ko kuma mai ayyukan munanawa ne, wataqila zai tuba. Bukhari ne ya rawaito shi, kuma wannan lafizin nasa ne, da Muslim.

Ya ku musulmai! Lallai darare da ranaku wasu taskoki ne na adana ayyuka. Sukan tsufar da sabon abu, kuma su matso da na nesa kusa. Kwanaki suna shuxewa, kuma shekaru suna maimaituwa, kuma mutane suna ta qara komawa zuwa ga Allah. Wani ya yi gaba wani ya yi baya. Wancan mara lafiya. Kuma kowanne yana komawa ne zuwa ga Allah. Haqiqa, Maxaukakin Sarki, ya ratse da wannan zamanin, wanda ya ara mana da cewa, lallai mutum yana cikin asara, sai fa wanda ya siffatu da abubuwa huxu: waxanda suka yi imani, suka yi ayyukan qwarai, suka yi wasiyya da gaskiya, kuma suka yi wasiyya da haquri. Ubangiji Mai xaukaka Yana cewa:

( وَالْعَصْرِ 1 إِنَّ الْإِنْسَانَ لَفِي خُسْرٍ 2 إِلَّا الَّذِينَ آَمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ وَتَوَاصَوْا بِالْحَقِّ وَتَوَاصَوْا بِالصَّبْرِ3 ) [العصر:1 - 3]

Ma’ana: (Ina rantsuwa da zamani! Lallai xan’adam yana cikin asara. Sai dai waxanda suka yi imani, suka aikata ayyukan qwarai, suka yi (wa juna) wasiyya da gaskiya, suka yi wasiyya da haquri).

Wannan sura mai girma, Imam Shafi’i yana faxa dangane da ita cewa, “Da ba a saukar da wata sura ba sai wannan, da ta ishi mutane.”

Ya kai masoyi, ka yi duba zuwa ga shafukan rayuwarka da ta shuxe, mai ka aje a cikinsu domin lahirarka? Ka yi tunani a ranka,: me wannan harshe naka ya faxa? Me kuma idanunka suka kalla? Kunnen nan nak me ya ji? Kuma waxannan qafafuwan naka ina suka je? Ya hannu! Me kika tava? Abin da ake buqata a gurinka shi ne ka riqe linzamin rayuwarka da kanka. Ka yi wa kanka hisabi. Maimun xan Mihran yana cewa: “Bawa ba zai zama haqiqanin mai tsoron Allah ba, har sai ya zama mai bibiyar kansa qeqe-da-qeqe sama da yadda xan kasuwa yake bin qwaqqwafin abokin kasuwancinsa”

Don haka dole mu yi wa kanmu hisabi a kan farillai. Kuma mu yi wa kanmu hisabi a kan abubuwan da aka hana. Gamu a kan dokin dare-da-rana yana famar tiqar gudu damu zuwa lahira. Abud Darda’i ya ji wani mutum yana tambaya game da wata jana’iza da ta wuce: mutumin ya ce wanene wannan? Sai Abud Darda, ya ce, «Ai kai ne».

A yayin da aka tambayi Abu Hazim: Yaya zuwa wajen Allah yake? Sai ya ce, «Amma shi mai xa’a, kamar matafiyi ne ya dawo ga iyalansa. Shi kuwa mai savo, kamar a dawo da gujajjen bawa ne ga ubangidansa».

Ku dage da qoqari ya ku masoya, tun daga yanzu. Domin su ayyuka qwarai, suna amfani ne idan mutum ya cika da su. Kada ya zo yana cewa:

( قَالَ رَبِّ ارْجِعُونِ 99 لَعَلِّي أَعْمَلُ صَالِحًا فِيمَا تَرَكْتُ كَلَّا إِنَّهَا كَلِمَةٌ هُوَ قَائِلُهَا وَمِنْ وَرَائِهِمْ بَرْزَخٌ إِلَى يَوْمِ يُبْعَثُونَ 100 ) [المؤمنون:99 - 100]

“Ya ce, “Ya Ubangijina ka mayar da ni (duniya). Ko na aikata aiki na qwarai a cikin abin da na bari. Kayya! Lallai ne ita kalma ce, shi ne mai faxinta, alhali kuwa a baya gare su akwai wani shamaki har ranar da za a tayar da su.”

Ya ku masoya! Ku ribaci shekarunku, kar ku vata su da aikata abubuwan da ba su da amfani, da gafala. Ku ribaci kwanaki qarfi, ku qara qaimi wajen ayyuka na qwarai. Domin dare da rana suna aiki a kanku, to kuma ku yi aiki akansu kamar yadda suke yi. Haka Umar xan Abdul’aziz ya faxa.

Haka nan, ku nutsu ku duba kimar lokaci, kar ku vata lokacinku akan abin da ba xa’ar Allah ba. Domin faufau, ba gami tsakanin wanda ya zauna a wani guri yana ambaton Allah, da wanda ya zauna a wani wuri yana vata lokacinsa da zantukan shirme waxanda ba za su amfanar da shi ba. Ko kuma mai savon da zai dulmiyar da shi a cikin Jahannama. Malam Ibn Kasir yana cewa a wajen faxin Allah Ta’ala:

( وَهُوَ الَّذِي جَعَلَ اللَّيْلَ وَالنَّهَارَ خِلْفَةً لِمَنْ أَرَادَ أَنْ يَذَّكَّرَ أَوْ أَرَادَ شُكُورًا 62 ) [الفرقان: 62]

Ma’ana: (Kuma shi ne wanda ya sanya dare da yini masu maye gurbin juna, ga wanda yake son ya yi tunani, ko kuwa ya yi nufin ya gode).

Malam Ibn Kasir ya ce,: “Kowane xaya daga cikinsu yana maye gurbin abokinsa, suna tare ba sa gajiya, idan wannan ya tafi, sai wancan ya zo. An sanya su suna bibiyar juna domin su zama lokacin bautar bayi ga Ubangiji. Duk wanda wani aiki ya kuvuce masa da daddare, sai ya yi shi da rana. Wanda kuma ya kuvuce masa da rana, sai ya yi shi da daddare” .

Ya ku bayin Allah ku sani cewa, dare da yini wasu ababan hawa ne, da suke nisanta ka da duniya kuma suke kusantar da kai zuwa lahira. Farin ciki ya tabbata ga bawan da ya amfani shekarunsa.

يُقَلِّبُ اللَّهُ اللَّيْلَ وَالنَّهَارَ إِنَّ فِي ذَلِكَ لَعِبْرَةً لِأُولِي الْأَبْصَارِ [النور: 44]

(Allah yana juyar da dare da yini. Lallai a cikin wannan akwai abin kula ga ma’abota gannai).

Kullum muna ganin shekaru suna zuwa su shuxe. Idan wannan shekara ta zo ta wuce, sannan muka shiga sabuwa, sai mu riqa ganinta da tsawo, nan da nan sai ta zo ita ma ta wuce. Abdullahi xan Umar ya ce: “Manzon Allah (ﷺ) ya riqe kafaxata, sai ya ce: “Ka zama a duniya kamar kai baqo ne, ko matafiyi.”

Don haka kada mumini ya saki jiki da duniya, kuma kada ya nutsu da ita, domin shi mutum a kan hanya yake, dole ne ya shirya kansa domin wannan tafiyar.

Ya kai xan’uwana Musulmi! Farkon shekara nan dole kowa ya tsaya tsayin daka ya bin ciki kansa ya kuma gyara hanyar gudanar da rayuwarsa, da kuma gusar da kurakurai, da komawa zuwa ga hanyar daidai. Domin komawa kan gaskiya ya fi dagewa akan qarya. Kada ka riqa kallon yawon laifuffukanka ka xauka Allah ba zai gafarta maka ba. Kada tsofaffin kurakuranka su hana ka tuba ta gaskiya ga Allah. Ubangijin Ta'ala yana cewa, a lokacin da yake magana da masu manyan laifuka da kurakurai, waxanda suka cuci kansu. Yana cewa:

( قُلْ يَا عِبَادِيَ الَّذِينَ أَسْرَفُوا عَلَى أَنْفُسِهِمْ لَا تَقْنَطُوا مِنْ رَحْمَةِ اللَّهِ إِنَّ اللَّهَ يَغْفِرُ الذُّنُوبَ جَمِيعًا إِنَّهُ هُوَ الْغَفُورُ الرَّحِيمُ 53 ) [الزمر: 53]

(Ka ce (Allah ya ce) “Ya ku bayina waxanda suka cutar da kansu da sovo, kada ku yanke qauna daga rahamar Allah. Lallai Allah yana gafarta zunubai gabaxaya. Lallai shi, shi ne mai gafara, mai jin qai). To me za mu yi? Sai Ya ce:

( وَأَنِيبُوا إِلَى رَبِّكُمْ وَأَسْلِمُوا لَهُ مِنْ قَبْلِ أَنْ يَأْتِيَكُمُ الْعَذَابُ ثُمَّ لَا تُنْصَرُونَ 54 وَاتَّبِعُوا أَحْسَنَ مَا أُنْزِلَ إِلَيْكُمْ مِنْ رَبِّكُمْ مِنْ قَبْلِ أَنْ يَأْتِيَكُمُ الْعَذَابُ بَغْتَةً وَأَنْتُمْ لَا تَشْعُرُونَ 55 ) [الزمر:54 - 55]

(Kuma ku mayar da al’amari zuwa ga Ubangijinku, kuma sallama masa, tun kafin azaba ta zo muku, sannan kuwa ba za a taimake ku ba. Kuma ku bi mafi kyawun abin da aka saukar muku daga Ubangijinku, tun kafin azaba ta zo muku bagatatan, kuma ku ba ku sani ba).

Wace irin azaba ce za ta zo maka kwatsam, ba tare da ka shirya ba, idan har kana savawa Allah? Ita ce mutuwa! Shin mutuwa tana turo da saqon sanarwa ne kafin zuwanta? A’a! Yanzu mutun zai hau motarsa da qafafuns, Amma bayan jima kaxan sai ka gan shi ana saukar da gawarsa! Kuma mutum zai sa kayansa da kansa, amma ba zai cire su da kansa ba, wataqil sai an sa almakashi an yanke masa su. Wannan shi ne ma’anar faxin Allah:

أَنْ تَقُولَ نَفْسٌ يَا حَسْرَتَا عَلَى مَا فَرَّطْتُ فِي جَنْبِ اللَّهِ وَإِنْ كُنْتُ لَمِنَ السَّاخِرِينَ 56 أَوْ تَقُولَ لَوْ أَنَّ اللَّهَ هَدَانِي لَكُنْتُ مِنَ الْمُتَّقِينَ 57 أَوْ تَقُولَ حِينَ تَرَى الْعَذَابَ لَوْ أَنَّ لِي كَرَّةً فَأَكُونَ مِنَ الْمُحْسِنِينَ58 ) [الزمر: 56 - 58]

(Kada wani rai ya ce: “Ya nadamata a kan abin a na yi sakaci akan sha’anin Allah kuma lallai na kasance haqiqa daga masu izgili. Ko kuma (kada) ya ce “Da Allah Ya shiryar da ni, da na kasance daga masu taqawa. Ko kuma (kada) ya ce a lokacin da yake ganin azaba, “Da lallai a ce ina da wata komawa (zuwa duniya) domin in kasance daga masu kyautatawa).

Allah ya nuna qarya yake, don haka ya ce,

( بَلَى قَدْ جَاءَتْكَ آَيَاتِي فَكَذَّبْتَ بِهَا وَاسْتَكْبَرْتَ وَكُنْتَ مِنَ الْكَافِرِينَ 59 ) [الزمر: 59]

(Na’am! Lallai ayoyina sun je maka, sai ka qaryata su, kuma ka yi girman kai, kuma ka kasance daga kafirai).

Kada savon Allah ya hana ka tuba, ka riqa cewa, wallahi ni mai zunubi ne da yawa! To idan kamai yai mai yawon savo ne, to shi kuma Allah Mai yawan gafara ne.

Kana cewa zunubaina manya-manya ne. To gafarar Allah ta fi zunubanka girma. Da a ce zunubanka za su yi tsiri har su tavo samaniya, sannan ka haxu da Allah kana mai neman gafararSa, Zai gafarta ma. Da zunubanka za su kasance kamar kumfar kogi, ko kamar yawan yashi, ko kuma kamar yawan ruwan sama, to rahamar Allah ta fi haka faxi. Allah yana cewa:

( وَرَحْمَتِي وَسِعَتْ كُلَّ شَيْء ) [الأعراف: 156].

“Kuma rahamata ta yalwaci dukkan komai...”

Kawai ka sauya! Wannan shi ne abin da ake son ka yi. Duk abin da ya wuce, Allah Zai gafarta maka shi, duk yawansa da nauyinsa da girman laifin da ke cikinsa. Duk wannan sai Allah Ya sauya maka shi zuwa kyawawan aiki. Shin ana samun abin da ya fi wannan ya xan’uwana? Wace falala ce ta fi wannan girma?

Har ila yau, bayan Allah Ya yafe maka, sai kuma Ya yi farin ciki da kai. Ya zo a cikin hadisi a Sahihil Bukhari, Manzon Allah (ﷺ) yana cewa: “Lallai Allah ya fi tsananin farin ciki ga tuban bawansa, sama da mutumin da ya kasance a wata dokar daji – yana cikin halin tafiya, yana tare da abin hawansa, kuma guzurinsa da ruwansa yana kanta, sai ta vace masa. Ya neme ta ya rasa. A yayin da ya yanke qauna ba zai ganta ba, sai ya sallamawa mutuwa. Sai ya zo qarqashin wata bishiya, ya zauna yana jiran mutuwa a yayin da yake cikin barci yana jiran mutuwa, sai ga taguwarsa nan, tana dawowa, kuma ta tsaya a gabansa. A yayin da ya buxe idanunsa sai ya same ta, sai farin cikin ya rufe shi, saboda tsabar farin ciki sai ya ce: ya Allah kai ne bawana, ni ne Ubangijinka.” Bai ma san me yake faxa ba, don haka sai ya yi kuskure saboda tsabar farin ciki.

Huxuba Ta Biyu

Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyen halitta Annabinmu Muhammad da alayensa da sahabbansa da waxanda suka bi tafarkinsu har zuwa tashin qiyama. Bayan haka:

Ya kai xan’uwana, Lallai gyara duk wata kantara daga gare ka, bayan yi wa kai hisabi, gyara ne ga rayuwarka. Kuma wata babbar dama ce mai inganci wajen gyara kanka da kanka. Kuma wannan ba yana nufin mutum ya haxa ayyukan kirki a tsakiyar ayyukan varna ba, wannan abu ne wanda yake bai dace ba.

Lallai komawa zuwa ga Allah, tana buqatarka da ka qara tsarin rayuwarka gabaxayanta. Kuma ka sake qulla alaqa tsakaninka da Ubangijinka alaqa cikakkiya mai nagarta, kuma da aiki cikakke. Kuma Maxaukakin Sarki yana kiranka zuwa ga samun wannan ta hanyar shugaban Istigfari. Ya zo a cikin Sahihil Bukhari da Muslim daga hadisin Bara’u xan Azib, Allah ya yarda da shi, ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Bana nuna maka shugaban Istigfari ba? Sai na ce, E, ina so, ya Manzon Allah. Sai ya ce: "Shugaban Istigfari shi ne bawa ya ce “Ya Allah Kai ne Ubangijina babu abin bautawa bisa cancanta sai Kai. Kai ka halicce ni kuma ni bawanKa ne, kuma ina kan alqawarinKa da wa’adinKa, gwargwadon iyawata. Ina neman tsarinKa daga sharrin abin da na aikata, ina bijiro da ni’imarKa a kaina, kuma ina bijiro da zunubina, Ka gafarta min domin haqiqa babu Mai gafarta zunubi sai Kai".

Ya ku ‘yan’uwana na addini! Lallai shi wannan wata na Muharram, yana daga cikin mafi xaukakar watannin Allah Maxaukakin Sarki. Matsayinsa mai girma ne, kuma alfarmarsa daxaxxiya ce, shi ne farkon wata a shekara. Kuma yana daga cikin watannin Allah masu alfarma. A cikinsa ne Allah Ya tseratar da Annabi Musa da mutanensa daga Fir’auna da ‘yan kanzaginsa. Ayyukan kirki a wannan watan suna da falala mai girma, tun ba ma azumi ba. Imam Muslim ya rawaito a cikin Sahihinsa daga Abu Huraira, Allah Ya yarda da shi, ya ce: “Manzon Allah (ﷺ), ya ce: “Mafificin azumi bayan Ramadan (shi ne azumin) watan Allah mai alfarma. Kuma mafi falalar sallah, bayan sallar farilla, ita ce sallar dare”.

Kuma mafi falalar kwanakin wannan watan, ya ku bayin Allah, ita ce ranar Ashura.

Hadisi ya zo a cikin littafin Bukhari da Muslim, daga xan Abbas, Allah ya yarda da su, ya ce: “Manzon Allah (ﷺ), ya zo Madinah, sai ya sami Yahudawa suna azumtar ranar Ashura, sai ya ce musu (ﷺ), wace rana ce wannan kuke azumtarta? Sai suka ce: wannan rana ce mai girma. A cikinta ne Allah ya kuvutar da annabi Musa da mutanensa, kuma ya dulmiyar da Fir’auna da ‘yan kanzaginsa. Sai Annabi Musa ya azumce ta, domin godiya, don haka mu ma muke azumtarta. Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Mu muka fi ku cancanta Annabi Musa. Sai Manzon Allah ya azumci wannan rana, kuma ya yi umarni da azumtar wannan rana.

Haka nan ya zo a cikin ingantaccen littafin Muslim, daga Abu Qatada Allah Ya yarda da shi: An tambayi Manzon Allah (ﷺ) game da azumin ranar Ashura? Sai ya ce: "Ina tsammanin Allah zai kankare (zunuban) shekarar da take gabaninsa". Allahu Akbar! Me ya fi wannan falala, wanda ba wanda zai yadda ta kuvuce masa sai asararre.

Kuma lallai Manzon Allah ya yi azamar azumtar ranar da take kafin wannan rana, domin ya savawa yahudawa, sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Idan har na kai zuwa baxi, zan azumci rana ta tara” . Muslim ne ya ruwaito shi daga xan Abbas, Allah Ya yarda da su.

Don haka ya kamata a kan musulmi ya azumci wannan ranar, domin koyi da annabawan Allah, da kuma neman ladan Allah. Kuma sannan ya kamata mutum ya azumci ranar da take kafin ranar Ashura, domin savawa Yahudawa, da kuma aikata abin da sunnar Musxafa (ﷺ) ta tabbatar. Lallai haqiqa, aiki ne xan kaxan da lada mai yawa, daga Allah.

Haqiqa wannan - Ya ku masoyana - yana daga cikin godiyar Allah game da ni’imominsa, kuma buxe farkon shekara ne da aikin mafi falala, wanda ake neman ladan Allah Maxaukakin Sarki da shi. Cikakken mai hankali shi ne wanda yake gane irin tagomashin da wannan irin aiki ya qunsa. Don haka mutanen kirki sai ku zage dantse.

Kuma ku sani – Allah Ya yi muku rahama – lallai Allah ya umarce ku da yawaita salati da sallama ga wanda aka aiko shi rahama ga talikai, Manzo mai shiryarwa, zavavve, amintacce, ma’abocin mu’ujizozi, da ayoyi bayyanannu. Allah Maxaukakin Sarki Yana cewa:

( إِنَّ اللَّهَ وَمَلَائِكَتَهُ يُصَلُّونَ عَلَى النَّبِيِّ يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا صَلُّوا عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا تَسْلِيمًا 56 ) [الأحزاب: 56]

(Lallai Allah da mala’ikunsa suna yin salati ga Annabi, ya ku waxanda suka yi imani ku yi salati a gare shi, kuma ku yi sallama matuqar sallama).

Kuma Manzo tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “Duk wanda ya yi salati a gare ni, Allah Zai yi masa da wannan salati goma.” Allah ka yi salati ga Annabinka kuma bawanka Muhammad da iyalan xakinsa kamar yadda ka yi tsira da amincinka ga Annabi Ibrahim da alayensa lalle kai wanda ake godewa ne, kuma mai girma.





Tags:




Ali Hajjaj Souissi