Manufofin huxubar
Umarni da tuba da neman gafarar Allah.
Bayanin a kan cewa yaye bala’i da musibu yana haxe da yawan istigfari .
Tunatar da mutane yi wa Allah xa’a da kuma tsoratar da su game da sava masa.
Yawaita addu’a da qanqan da kai da komawa zuwa ga Allah maxaukakin sarki.s
Huxuba Ta Farko
Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma muna neman tsarinsa daga shirrin kawukanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar da shi, wanda kuma ya vatar to babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaxai ne ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi Muhammad bawansa ne manzonsa ne. (Ya ku waxanda suka yi imani ku ji tsoron yadda ya cancaci a ji tsoronsa, kada ku mutu face kuna musulmi). (Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicceku daga rai guda xaya, kuma ya ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga garesu (su biyu). Ku ji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya da shi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Ya ku wanxanda suka yi imani ku ku ji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku ayyukanku, kuma ya gafarta muku zunubbanku. Wanda ya bi Allah da Manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawon shiriya shiriyar Annab Muhammad (ﷺ). Kuma mafi shirrin al'amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wani qagaggen abu (addini) bidi'a ce, duk wata bidi'a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta.
Bayan haka:
Ina yi muku wasiyya ya ku mutane, da ni kaina, da mu ji tsoron Allah maxaukakin sarki. Ku tsoraci Allah. Domin tsoron Allah, hanya ce ta tsira da aminta, kuma hanya ce ta rabauta da karamci. Waxanda suka kuvuta daga azabar Allah su ne masu tsira. Allah yana cewa:
Ma'ana: (Sannan kuma, mu tserar da waxanda suka yi aiki da taqawa, kuma mu bar azzalumai a cikinta a gurfane).
Kuma su ne masu gadon gidan aljannah. Allah yana cewa:
تِلْكَ الْجَنَّةُ الَّتِي نُورِثُ مِنْ عِبَادِنَا مَنْ كَانَ تَقِيًّا 63 ) [مريم: 63] ) Ma’ana: (Wancan aljanna ce wadda muke gadar da ita ga wanda ya kasance mai aiki da taqawa daga bayina).
kuma za a karvi ayyuka ne kawai daga waxanda suke masu taqawa. Allah yana cewa:
( إِنَّمَا يَتَقَبَّلُ اللَّهُ مِنَ الْمُتَّقِينَ 27 ) [المائدة: 27]
(Lalle, Allah yana karva ne kawai daga masu taqawa ne).
Ya ku musulmai, Allah Ta’ala albarkatunsa sun yawaita, kuma ambatonsa ya xaukaka, Shi ne mai yafe zunubai, mai suturce aibi, yana kiran bayinsa:
( وَتُوبُوا إِلَى اللَّهِ جَمِيعًا أَيُّهَا الْمُؤْمِنُونَ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ 31 ) [النور: 31]
“Kuma ku tuba zuwa ga Allah gabaxaya ya ku muminai. Ko wala’alla kwa sami babban rabo.”
Haka kuma yana kiransu yana cewa: “Ya ku bayina, lallai ku kuna kuskure da rana da dare, ni kuma Ina yafe zunubai gabaxaya, ku nemi yafewata, Zan yafe muku.” Muslim ne ya rawaito shi, daga Abu Zarril Gifari, Allah ya yarda da shi.
Tsarki ya tabbata a gare shi, kuma ya xaukaka, shi ya fi kowa sani game da halittarsa. Ya san kasawarsa da rauninsu da gajiyawarsa. Don haka sai ya buxe musu qofar fatan samun afuwarsa da kwaxayin rahamarsa, samun yardarsa. Allah yana cewa:
وَاللَّهُ يَدْعُو إِلَى الْجَنَّةِ وَالْمَغْفِرَةِ بِإِذْنِهِ ) [البقرة: 221] )
(Kuma Allah yana kira zuwa ga aljanna da gafara da izininsa).
Rahamar Ubangiji mai kwarara ce babu mai sama ta wegi. Haka nan ni’imominsa ba su da iyaka, wane ne yake rantsuwa cewar Allah ba zai gafarta zunuban bayinsa ba?!
( وَمَنْ يَغْفِرُ الذُّنُوبَ إِلَّا اللَّهُ ) [آل عمران: 135] .
“Kuma wanene ke gafara zunubai in ba Allah ba?”
Ya ku ‘yan’uwa, idan neman gafara ya yi yawa a cikin al’umma, kuma ya fito daga zukata nitsatssu, sai Allah ya gusar daga gare su gungun cutarwa, sai Allah ya kawar daga gare su nau’i-nau’i na bala’o’i da masifu.
( وَمَا كَانَ اللَّهُ لِيُعَذِّبَهُمْ وَأَنْتَ فِيهِمْ وَمَا كَانَ اللَّهُ مُعَذِّبَهُمْ وَهُمْ يَسْتَغْفِرُونَ 33 ) [الأنفال: 33]
“Kuma Allah ba zai musu azaba ba alhali kuwa kai kana cikinsu, kuma Allah ba zai musu azaba ba alhali kuwa suna yin istigfari.”
Da istigfari ne rahamomi suke sauka.
لَوْلَا تَسْتَغْفِرُونَ اللَّهَ لَعَلَّكُمْ تُرْحَمُونَ 46 ) [النمل: 46] )
(Don me ba ku neman Allah gafara ba , ko wala’alla za a yi muku rahama?)
Ya ku masoya, lallai gyaruwar xaixaikun mutane da al’umma, da barin zunubai da laifuffuka, yana alaqa mai qarfi tsakanin hakan da samun biyan buqatu, da yalwatar alheri. Akwai qaqqarfar alaqa tsakanin samun wadata ta dukiya da kuma qarfi da dauwama akan yin istigfari. Ku saurari kiran da Annabi Nuhu ya yi wa mutanensa ind yake cewa:
( فَقُلْتُ اسْتَغْفِرُوا رَبَّكُمْ إِنَّهُ كَانَ غَفَّارًا 10 يُرْسِلِ السَّمَاءَ عَلَيْكُمْ مِدْرَارًا 11 وَيُمْدِدْكُمْ بِأَمْوَالٍ وَبَنِينَ وَيَجْعَلْ لَكُمْ جَنَّاتٍ وَيَجْعَلْ لَكُمْ أَنْهَارًا 12 ) [نوح: 12]
(Sai na ce, ‘Ku nemi gafarar Ubangijinku, lallai ne shi ya kasance Mai yawan gafara ne. Ya sako (girgijen) sama a kanku da ruwa mai kwarara. Kuma ya yalwata ku da dukiyar da ‘ya’ya, Ya sanya muku (albarka) ga gonaki, kuma Ya sanya muku koguna).
Kuma mafificin istigfari, ya ‘yan’uwa musulmai shi ne, bawa ya fara da yabo ga Ubangijinsa, sannan ya yi iqrari da ni’imar Allah, sannan ya yarda shi mai laifi ne , sannan daga nan sai ya nemi gafarar Ubangijinsa. Kamar yadda ya zo a hadisin Shaddad xan Auws, Allah ya yarda da shi, daga manzon Allah (ﷺ) ya ce, (Shugaban Istigfari shi ne bawa ya ce” ya Allah kai ne Ubangijina babu abin bautawa bisa cancanta sai kai, kai ka halicce ni kuma ni bawanka ne, kuma ina kan alqawarinka da wa’adinka, gwargwadon iyawata. Ina neman tsarinka daga sharrin abin da na aikata, ina komowa da ni’imarka a kaina, kuma ina dawowa gare ka da zunubina, ka gafarta min domin haqiqa babu mai gafarta zunubi sai kai). Bukhari ne ya ruwaito shi.
Allah ya sanya ni da ku mu zan cikin waxanda suka farka don qoqarin cimma abin ya guje musu, kuma . Haka nan Allah ya tsare ni da ku, kada mu zama kamar wanda shekarunsa suka tafi, amma aikinsa ya yi qaranci, kuma ajalinsa ya kusanto, kuma sannan ya munana zatonsa ga Ubangijinsa.
Ku ji tsoron Allah Ubangijinku, kuma ku mayar da zukatanku gare shi, ku kyautata masa zato, ku dage wajen bibiyar ayyukanku, kuma ku yi gaskiya wajen kamun qafa da Allah. Duk wanda ya koma ga Allah da gaske, sai ya karvi tubansa idan ya tuba. Ku guji alfasha da zancen banza, da zama da waxanda suke da miyagun aiki, da harka da wawaye. Ku kiyaye wa mutane alfarmarsu, kada ku dinga vata ayyukanku. Ku sadar da zumunci. Ku taimakawa marayu da iyayensu mata. Ku yi sadaka da dinare da abin da Allah ya hore muku, ku ji tsoron wuta ko da da tsagin dabino ne. Allah yana cewa:
( فَلَا اقْتَحَمَ الْعَقَبَةَ 10 وَمَا أَدْرَاكَ مَا الْعَقَبَةُ 11 فَكُّ رَقَبَةٍ12أَوْ إِطْعَامٌ فِي يَوْمٍ ذِي مَسْغَبَةٍ 14 يَتِيمًا ذَا مَقْرَبَةٍ 15 أَوْ مِسْكِينًا ذَا مَتْرَبَةٍ 16 ) [البلد: 11 - 16].
(To don me ne bai kutsawa cikin Aqaba ba. Kuma mene ne ya sanar da kai abin da ake wa Aqaba? Ita ce ‘yanta bawa. Ko ciyarwa, a cikin wani yini ma’abocin yunwa. Ga maraya makusanci. Ko kuwa wani miskini matalauci).
Ku yawaita salati da neman tsira a bisa ga zavavve, wanda ya shiryar da al’umma, shugabanmu abin koyinmu, Muhammad xan Abdullahi. Ya Allah ka yi daxin tsira da aminci da albarka a bisa bawanka kuma manzonKa, Muhammad da iyalansa da matansa da sahabbansa.
Huxuba Ta Biyu
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da aminci su qara tabbata a bisa mafificin manzanni, Annabinmu Muhammad da alayensa da sahabbansa gabaxaya, bayan haka:
Ya ku ‘yan’uwa! Ku sani, idan zunubai suka yi yawa, sai mutane su cancanci a halakar da su. Kuma idan zunubai suka yi yawa sai arziqi ya yi qaranci, albarka ta gushe, fasadi ya game ko’ina, cututtuka su yawaita, al’amura su cakuxe.
Wata rana manzon Allah ya fuskanci sahabbansa, sai ya ce: (Abubuwa biyar idan aka jarrabe ku da su, kuma ina neman tsarin Allah kar ku riske su. Alfasha ba za ta bayyana ba a cikin al’umma har su dinga bayyana ta, har sai annoba da cututtuka sun watsu cikinsu , irin waxanda ba su tava samun mutanen da suka gabace su ba. Kuma ba za su tauye mudu da sikeli ba, har sai an kama su da fari da tsadar abinci, da zaluncin shugaba a kansu. Kuma ba za su hana zakka ba, har sai an hana su ruwan sama. Ba don dabbobi ba, da ba za a yi musu ruwa ba. Kuma ba za su warware alqawarin Allah da manzonsa ba sai Allah ya xora abokan gabansu akansu sun wawashe musu arzikinsu. Kuma matuqar shugabanni ba su hukunci da littafin Allah kuma suka riqa zami sonka cikin abin da Allah ya saukar, har sai Allah ya sanya yaqinsu a tsakaninsu”. Ibn Majah ne da Hakim suka ruwaito shi kuma suka inganta shi, Albani ya kyautata shi.
Ya bayin Allah, lallai akwai shu’umci a cikin savon Allah, kuma zunubai suna da matsalolinsu. Nawa suka halakar daga cikin al’ummomi, kuma nawa suka rugurguza:
( وَكَمْ قَصَمْنَا مِنْ قَرْيَةٍ كَانَتْ ظَالِمَةً وَأَنْشَأْنَا بَعْدَهَا قَوْمًا آَخَرِينَ 11 ) [الأنبياء: 11]
(Kuma da yawa Muka karya wata alqarya ta kasance mai zalunci, kuma Muka qaga halittar waxansu mutane na daban a bayanta).
( كَمْ تَرَكُوا مِنْ جَنَّاتٍ وَعُيُونٍ 25 وَزُرُوعٍ وَمَقَامٍ كَرِيمٍ 26 وَنَعْمَةٍ كَانُوا فِيهَا فَاكِهِينَ 27 كَذَلِكَ وَأَوْرَثْنَاهَا قَوْمًا آَخَرِينَ 28 فَمَا بَكَتْ عَلَيْهِمُ السَّمَاءُ وَالْأَرْضُ وَمَا كَانُوا مُنْظَرِينَ 29 [الدخان:25 - 29] .
(Sun bar gonaki da maremarin idanun ruwa da yawa. Da shuke-shuke da matsayi mai kyau. Da wata ni’ima da suka kasance a cikinta suna masu raha. Kamar haka! Kuma muka gadar da ita ga waxansu mutane na daban. Sannan sama da qasa ba su yi kuma a kansu ba, kuma ba su kasance waxanda ake yi wa jinkiri ba).
Ta hanyar savo ne ni’imomi suke gushewa, azaba take sauka, bala’o’i suke yawaita, fitintinu su yi ta faruwa, Allah yana cewa:
( إِنَّ اللَّهَ لَا يُغَيِّرُ مَا بِقَوْمٍ حَتَّى يُغَيِّرُوا مَا بِأَنْفُسِهِمْ ) [الرعد: 11] .
(Lallai Allah ba ya sauyi ga al’umma har sai sun sauya abin da ke zukatansu).
Ya ‘yan’uwa, lallai hikimar Allah da mashi’arsa ta gudana cewa yana jarrabar bayinsa a cikin wannan gida na duniya. Allah Yakan jarrabe su da alheri ko sharri. Ya kan jarrabe su da kyawawa, ko ya jarrabe su da abin qi. A cikin irin waxanan masifu akwai rahamar Ubangiji da babu mai xanxanarta sai mai nagartaccen imani. Ta qarqashin irin waxan masibu ne bawa yakan tabbatar da tauhidi ya samu yaqini. Idan wahala ta yi yawa abubuwa suka girmama, sai mafita ta samu. Allah yana cewa:
( حَتَّى إِذَا اسْتَيْئَسَ الرُّسُلُ وَظَنُّوا أَنَّهُمْ قَدْ كُذِبُوا جَاءَهُمْ نَصْرُنَا ) [يوسف: 110] .
(Har lokacin da manzanni suka yanke tsammani, kuma suka yi zaton cewa an musu qarya, sai taimakonmu ya je musu).
Bala’i yakan raba zuciyar bawa mumini daga duk wani abin halitta, sai kuma ya juya zuwa ga Mai yawan kyauta, Mai yawan rahama. A cikin littafin Allah, akwai wasu mutane da aka zarge su, domin ba su qasqantar da kansu ga Allah ba yayin da wani bala’i ya same su, kuma ba sa komawa zuwa gare shi ba a lokacin qunci, Allah yana cewa:
( وَلَقَدْ أَخَذْنَاهُمْ بِالْعَذَابِ فَمَا اسْتَكَانُوا لِرَبِّهِمْ وَمَا يَتَضَرَّعُونَ 76 ) [المؤمنون: 76]
(Kuma lallai ne, haqiqa, Mun kama su da azaba, sai dai ba su saukar da kai ba ga Ubangijinsu, kuma ba su yin tawali’u).
Sannan ku ji tsoron jujjuyawar zamani. Ba komai ba ne duniya face wani buri yankakke. Farin cikin duniya haxe yake da baqin ciki. Allah yana sane ya hana mutanen kirki duniya, amma kuma ya ba da ita ga mutanen banza don su ruxu da ita.
Ku yi sauri wajen komawa ga Allah, ku yi rigegeniya wajen tuba, domin da tuba ingantacce ne ake wanke kurakurai. Kuma da istigfari ne sama take zubar da ruwa, ake samun alherai, kuma da haka ne ake saukar da albarkatu.
Kuma haka ne ga ku ya bayin Allah, kun hallara a wannan wuri mai tsarki, a gaba ga Ubangijinku kuna kai kuka matsalolinku, kuna nufi i zuwa gare shi da buqatunku, ta hanyar aikin kirki a wajenSa, don haka ku nuna taushin zuciya, da rashin qarfin jiki, da qanqan da kai a gafan mabuwayi mai gafara. Haka nan duk waxanna buqatun da damuwarku, jarrabawa daga Ubangijinku duk domin ku fuskance shi, kuma domin ku sami kusanci da ayyukan kirki zuwa gare shi. Ku yi addu’a, ku yi qanqan da kai nemi albarkarsa, domin shi mai yawan gafara ne.
Ya Allah mun zalunci kawunanmu, idan har ba ka yi mana gafara da rahama ba, za mu kasance daga cikin hasararru. Ya Allah kai ne Allah, ba wani abin bauta bisa cancanta sai kai, kai ne mawadaci, mu ne faqirai a gurinka, ka shayar da mu, kar ka sanya mu zama daga cikin masu yanke qauna. Ya Allah Ka shayar da mu, ya Allah ka shayar da mu daga abin shayarwa mai albarka, ka shayar da mu ruwa mamako. Ya Allah Ka rayar da garuruwanmu da shi, ka shayar da bayinka da shi, Ka sanya shi ya kasance mai amfani ga na kusa da na nesa. Ya Allah ka shayar da mu daga rahamarKa ba daga azaba ba, ba mai rusawa ko bala’i ko nutsarwa ba. Ya Allah ka shayar da bayinka da garinka da dabbobinka. Ka yalwatar da rahamarka, ka rayar da garinka da ya mutu. Ya Allah ka fitar mana da tsirrai, Ka samar mana da abinci. Ka saukar mana da albarkatunka, kuma ka sanya abin da ka saukar da shi ya zama qarfi a gare mu wajen yi maka xa’a. Ya Allah mu bayi ne daga cikin bayinka, kar Ka hana mu falalarka saboda zunubinmu.
Tsarki ya tabbata ga Allah, ga Allah muka dogara. Ya Allah kar Ka sanya mu fitina ga mutane azzalumai. Ya Allah ka yaye mana yunwa, da wahala da tsiraici, ka yaye mana bala’in da babu mai yaye shi sai kai. Ya Allah muna neman gafararka, lallai kai ne Mai yawan gafara. Ka saukar mana da mamakon ruwan sama. Ya Allah Ka shayar da mu ruwa, Ka amintar da mu daga tsoro, kar ka sanya mu cikin masu yanke qauna. Kar ka halaka mu da fari. Ya Allah ka yi rahama ga ‘yan yara da ake shayar da su, da dabbobi masu kiyo , da tsofaffi masu bautarka, ka yi rahama ga halittu baki xaya. Ya Ubangijinmu! Kada ka kama mu idanmun yi mantuwa, ko kuma mun yi kuskure. Ya ubangijinmu! Kuma kada Ka xora nauyi a kanmu, kamar yadda Ka xora shi a kan waxanda suke a gabaninmu. Ya Ubangijinmu kada ka sanya mu xaukar abin da ba za mu iya ba. Kuma Ka yafe mana, kuma ka gafarta mana, kuma ka ji qanmu. Kai ne Majivincinmu, saboda haka ka taimake mu a kan mutanen nan kafirai.
Ya Allah ka taimaki addininka da littafinka da sunnar Manzonka da bayinka nagari. Ya Allah ka gyara mana addininmu wanda shi ne qarfin al’amarinmu, ka gyara mana duniyarmu da abubuwan rayuwarmu suke cikinta. Ka gyara mana lahirarmu da abubuwan da ka tanadar mana suke. Ka sanya rayuwa ta zamo qari gare mu na daga kowane alheri, mutuwa kuma ta zamto hutu gare mu daga dukkanin wani sharri. Ya Allah Ka sauwaqe mana tsadar kayayyaki kana mana maganin duk wani bala’i da cututtuka da annoba ka tsare mu daga zina da girgizar qasa da munanan fitintinu waxanda suka bayyana da waxanda suke vuya, a wannan gari namu da sauran garuruwan musulmai. Ya Allah duk wanda yake nufinmu ko yake nufin garinmu ko wuraren ibadunmu da wani mugun nufi, ya Allah ka shagaltar da shi da kansa. Kuma ka sanya kaidinsa a cikin al’amuransa, kuma ka sanya rushewar cikin qulle-qullensa. Allah muna sanya katanga gare mu, kuma muna neman tsarinKa daga sharre-sharrensu. Ya Allah ka tsare daga kaidin masu kaidi, da qiyayyar masu qiyayya. Ka yanke tushen fasadi da masu yin shi. Ya Allah ka amintar da mu a garuruwanmu ka gyara shugabanninmu. Ka qarfafi shugabanmu da gaskiya da aminci, ka xaukaka su da yi maka xa’a. Ka qarfafi addininka da su. Ka azurta su da abokan shawara na gari, waxanda za su dinga shiryar da su ga ayyukan alheri kuma su dinga taimakonsu a kai. Ya Allah ka ba mu kyakkyawa a duniya Ka ba mu kyakkaywa a lahira, Ka kare mu daga azabar wuta.
Ya bayin Allah ku yi koyi da Annabinku Muhammad, ku yi qoqari wajen roqon Allah, ku roqi Allah kuna masu sakankancewa da za a amsa muku. Ku yawaita istigfari da sadaka da sadar da zumunci, ku kiyaye haqqoqin jama’a. Kada ku yi varna da kayayyakin al’umma, kuma kada ku kasance masu kawo varna a bayan qasa kuna masu lalatawa, ko Ubangijinku ya yi muku rahama. Ta haka sai Allah ya taimaki zukata ta hanyar komawa gare shi, ya taimaki gari ta hanyar saukar da rahama a cikinsa. Tsarki ya tabbata ga Ubangijinka, ubangijin rinjaye, daga barin abin da suke siffantawa. Kuma aminci ya tabbata ga Manzanni. Kuma godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu. Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, Allah Ka yi daxin tsira ga bawanka kuma manzonKa Muhammad da alayensa da sahabbansa gabaxaya.