Kwadaitarwa wajen sadar da zumunta


5364
Surantawa
Sadar da zumunci abune da Allah ke yalwata arziki dashi, kuma yake jan zamanin mutum saboda shi, kuma dukiyar mutum ke albarkatuwa ta dalilin shi. Sadadda zumunci alarmar cikar imani ne da kyautatuwar musuluni, kuma yanke zumunci sababin la’ana ne da uquba da bone da azaba, haka yana halaka albarku, kuma yana gadar da adawa da kiyayya.
Manufofin huxubar Kwaxaitarwa wajen neman ilimi mai amfani da aiki da shi. Faxakarwa a kan ladubban neman ilimi. Tsoratarwa daga jahiltar addini. Kira zuwa ga gyara manhajar karantarwa. Huxuba Ta Farko Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma muna neman tsarinsa daga shirrin kawukanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar da shi, wanda kuma ya vatar to babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaxai ne ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi Muhammad bawansa ne manzonsa ne. (Ya ku waxanda suka yi imani ku ji tsoron yadda ya cancaci a ji tsoronsa, kada ku mutu face kuna musulmi). (Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicceku daga rai guda xaya, kuma ya ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga garesu (su biyu). Ku ji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya da shi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Ya ku wanxanda suka yi imani ku ku ji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku ayyukanku, kuma ya gafarta muku zunubbanku. Wanda ya bi Allah da Manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawon shiriya shiriyar Annab Muhammad (ﷺ). Kuma mafi shirrin al'amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wani qagaggen abu (addini) bidi'a ce, duk wata bidi'a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta. Ya ku ‘yan uwana musulmi ku sani cewa addinin musulunci addini ne na ilimi. Umarni da neman ilimi shi ne farkon abin da Allah Maxaukakin Sarki ya umarci Annabinsa (S.A.W) da shi, yayin da ya saukar masa da faxinsa : (اقْرَأْ بِاسْمِ رَبِّكَ الَّذِي خَلَقَ1 خَلَقَ الْإِنْسَانَ مِنْ عَلَقٍ 2 اقْرَأْ وَرَبُّكَ الْأَكْرَمُ 3 الَّذِي عَلَّمَ بِالْقَلَمِ 4 عَلَّمَ الْإِنْسَانَ مَا لَمْ يَعْلَمْ5) [العلق: ١ - ٥]. Ma’ana : (Ka yi karatu da sunan Ubangijinka da ya yi halitta. Wanda ya halicci mutum daga gudan jini. Ka yi karatu kuma Ubangijinka shi ne mafi karamci. Wanda ya sanar da alqalami. Ya sanar da mutum abin da bai sani ba). (Alaq : 1 – 5) Addinin musulunci ya kwaxaitar da mabiyansa akan neman ilimi, domin ba zai yiwu mutum ya bauta wa Allah ba sai da ilimi. Allah maxaukakin Sarki yana cewa : (إِنَّمَا يَخْشَى اللَّهَ مِنْ عِبَادِهِ الْعُلَمَاءُ28) [فاطر: ٢٨]. Ma’ana : (Kaxai waxanda suke jin tsoron Allah daga cikin bayinsa su ne masu ilimi).(Faxir : 28). Ya sake cewa : (قُلْ هَلْ يَسْتَوِي الَّذِينَ يَعْلَمُونَ وَالَّذِينَ لَا يَعْلَمُونَ إِنَّمَا يَتَذَكَّرُ أُولُو الْأَلْبَابِ9) [الزمر: 9] Ma’ana : (Shin waxanda suka sani da waxanda ba su sani ba za su yi daidai?). (Azzumar : 9). Ya kuma umarci Annabinsa da ya nemi qarin ilimi, ya ce : (وَقُلْ رَبِّ زِدْنِي عِلْمًا114) [طه: 114] Ma’ana : “Ka ce Ubangiji qara min ilimi”. (Xaha : 114) Ya xaga darajar muminai masu ilimi a kan muminai waxanda ba su da ilimi, Allah ya ce : (يَرْفَعِ اللَّهُ الَّذِينَ آَمَنُوا مِنْكُمْ وَالَّذِينَ أُوتُوا الْعِلْمَ دَرَجَاتٍ وَاللَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ خَبِيرٌ11) [المجادلة: 11] Ma’ana : (Allah yana xaga darajar waxanda suka yi imani daga cikinku da waxanda aka ba wa ilimi). (Al- Mujadalah : 11). An karvo daga Kasir xan Qaisi ya ce, ina zaune tare da Abud Darda’i a masallacin Dimashqa, sai wani mutum ya zo wajensa ya ce masa, Ya Abud Darda’i na zo wajenka ne daga Madinar Manzon Allah (S.A.W) saboda wani hadisi da aka ce min kana faxa daga Manzon Allah (S.A.W), kuma babu wata buqata da ta kawo ni nan sai wannan. (wato jin wannan hadisin) Sai Abud Dar’da’i ya ce, “Na ji Manzon Allah (S.A.W) yana cewa : “Duk wanda ya bi wata hanya yana neman ilimi a cikinta, to Allah zai sanya shi akan hanya daga cikin hanyoyin Aljannah, kuma haqiqa Mala’iku suna sanya fika – fikansu ga xalibin ilimi, don yarda da abin da yake nema, sannan duk wanda yake sama da qasa yana nema wa malami gafara, har ma da kifayen da suke cikin ruwa. Falalar malami a kan mai bauta kamar falalar wata ne a daren goma sha huxu a kan sauran taurari, kuma haqiqa malamai magada Annabawa ne, Annabawa kuwa ba su bar gadon dinari ko dirhami ba, kaxai sun bar gadon ilimi ne, duk kuwa wanda ya kama shi, to ya kama rabo mai girma”. Abu Dawud ne ya rawaito. A cikin wannan hadisi akwai dalili bayyananne akan falalar ilimi da masu ilimi, saboda hadisin ya nuna ilimi hanya ce daga cikin hanyoyi zuwa Aljannah, kuma Mala’iku suna shimfixa fika – fikansu ga xalibin ilimi saboda yarda dawaxanda suke sama da qasa suna nema masa gafara, har da kifayen da suke cikin kogi, to shin yanzu akwai wata falala da daraja da tafi wannan da aka ambat – Yaku bayin Allah. Haqiqa – ya ku bayin Allah – fahimtar addini alama ce dake nuna Allah ya nufi bawa da alheri, An karvo daga Mu’awiya – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Duk wanda Allah ya nufe shi da alheri sai ya fahimtar da shi addini. Allah ne mai bayar wa, ni kuma mai rabawa ne. Wannan al’umma ba za ta gushe ba, tana maxaukakiya akan duk wanda ya sava mata, har sai lamarin Allah ya zo, tana maxaukakiya” Bukhari da Muslim. Kai! Saboda falalar ilimi da darajarsa ya halatta a yi hassada (gifxa) a kansa, An karvo daga Abdullahi xan Mas’ud – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Ba a yin hassada sai a kan abubuwa guda biyu (su ne) Mutumin da Allah ya bashi dukiya, kuma ya bashi dama wajen kashe ta a kan gaskiya, da mutumin da Allah ya bashi hikima (ilimi) yake hukunci da ita, kuma yake koyar da ita” Bukhari ne ya rawaito. Muxarrif xan Shikhkir yana cewa : “Falalar ilimi ta fi falalar aiki, mafi alheri a cikin addininku shi ne tsantseni”. (Ibnu Abdul – Barri ne ya rawaito a cikin “Jami’ul Bayanil Ilmi”. Imam Shafi’i yana cewa : “Neman ilimi ya fi sallar nafila zama wajibi”. Wata rana Sayyidina Umar xan Khaxxab – Allah ya yarda da shi – yana Madina, sai ga Nafi’u xan Haris Alkhuza’i – gwamnan shi na Makka – ya zo wajensa, sai Umar ya ce masa : “Wa ka bari a can madadinka?” sai ya ce, “Na bar wani bawa ne barrarre (wato wanda aka ‘yanta) sai sayyidina Umar ya ce, “Ka sanya Bawa!?” Sai ya ba shi amsa ya ce, “Saboda shi makarancin Alqur’ani ne, kuma ya san ilimin gado” sai Umar ya ce, “Haqiqa Annabi (S.A.W) ya ce, Allah yana xaga wasu mutane da wannan littafi (Alqur’ani) yana kuma qasqanta wasu mutane da shi”. Ya kai xalibi, ka sani ilimi yana da wasu ladubbai da sukan sanya shi ya zama ibada ga Allah, daga cikinsu akwai tsarkake niyya, (ma’ana neman ilimi don Allah, ba don son iyawa ba, ko birge mutane), ya zo a hadisin Abu Hurairata – Allah ya yarda da shi – Manzon Allah (S.A.W) ya ce : “Duk wanda ya nemi ilimin da ake nema don Allah (wato ilimin addini) ya zama bai koye shi ba sai don ya samu duniya, to ba zai ji qanshin Aljannah ba ranar alqiyama”. Abu Dawud ya rawaito. A wani hadisin da Muslim ya rawaito, Manzon Allah ya ce, “Alqur’ani hujja ne gareka ko a kanka”. Ibnu Jama’a – Allah ya yi masa rahama – ya ce, “Ka sani cewa duk abin da aka ambata na falalar ilimi da malamai to ya tabbata ne a kan malamai masu aiki da iliminsu, masu biyayya da tsoron Allah, waxanda suka nufi Allah da iliminsu, da samun kusanci zuwa ga Aljannah, ba waxanda suka nemi shi da mummunan niyya ba, ko don wani abu na duniya, na mulki, ko dukiya, ko kuma don alfahari ga abokai da mabiya” (Tazkiratus Sami’i) Hakanan ana so xalibi ya himmatu da abin da ya fi mahimmanci, ya fara hardace Alqur’ani da Tajwidinsa, sannan ya karanci Sunnah, ya yi aiki da abin da ya sani daidai gwargwadon iyawarsa. Sannan ya aikata abin da ya sani daidai ikonsa. Imamu Ash-Shafi’i – Allah ya yi masa Rahama – yana cewa : “Ilimi ba shi ne abin da aka hardace ba, a’a ilimi shi ne wanda ya yi amfani”. Saboda haka ilimi ingantance shi ne ilimin da ya gadar wa da mai shi tsoron Allah, da nutsuwa, da tsoron Allah, da qasqantar da kai. Sayyidina Umar – Allah ya yarda da shi – ya ce “Ku koyi ilimi, ko koyi nutsuwa tare da shi”. Allah ya yi mana Albarka cikin abinda muka ji, na Alqur’ani da Hadisi, Shi Allah Mai iko ne akan dukkan komai.
Godiya ta tabbata ga Allah, Kyakkyawan qarshe yana ga masu tsoron Allah, Tsira da Aminci su tabbata ga fiyayyen halitta, Manzon Allah (S.A.W) da iyalansa da Sahabbansa da waxanda suka bi su gaba xayansu, har zuwa ranar sakamako. Bayan haka: ‘Yan Uwana Masu Sauraro, Ga wasu misalai daga rayuwar magabatanmu na qwarai wajen jajircewa a kan neman ilimi, sun bada duk abin da suka mallaka wajen ganin sun sami ilimi : Babban Malamin hadisin nan mai suna Abdur-Rahman xan Abi Hatim yana bamu labarinsa yana cewa “Ba a samun ilimi da hutun jiki, mun zauna wata bakwai a garin Misra, bamu ci abinci mai romo ba, muna neman ilimi, domin kuwa muna sammako da sassafe zuwa majalisin malamai, mu zauna har zuwa azzahar, bayan azzahar kuma sai mu tafi wani majalinsin, haka ma da la’asar har zuwa dare, idan dare ya yi, sai mu zauna mu riqa rubuta abin da muka koyo, muna gyarawa, don haka ba mu da wani lokaci da zamu gyara wani abinci (mai romo mu ci). A tare da ni akwai wani abokina xan garin Khurasana, ina amfani da littafinsa, yana amfani da nawa, duk abin da na rubuta ba ya rubutawa, abin da ya rubuta ba na rubutawa. Wata rana muka yi sammako zuwa wajen wani malami, sai aka ce mana, baya da lafiya, don haka sai muka dawo, a hanya muka ga wani kifi, ya qayatar da mu, muka saye shi, muna zuwa gida sai lokacin zuwa wajen wani malami ya yi, saboda haka bamu samu damar gyara kifin nan ba, muka wuce zuwa majalisi, bamu gushe ba muna kai – kawo zuwa wajen malamai har tsawon kwana uku, bamu gyara kifin nan ba, har ya kusa ya lalace, saboda haka muka cinye shi xanye!!”. Sai ka ce da Abdur-Rahman, ai zaku iya bawa wani ya gyara muku shi, sai ya ce, “Ina muka samu damar yin hakan”. (Siyar J13/ sh 266). Imam Shu’uba xan Hajjaj – Allah ya yi masa rahama – ya yi tattaki daga garinsa Basrah zuwa Makkah, zuwa Madinah sannan ya dawo garinsa, saboda ya gano ingancin hadisi xaya tak!!. Ya ‘yan uwa masu sauraro : Kaxan kenan daga cikin qisoshin malamai magabata wajen neman ilimi, don haka wajibi ne a kanmu mu tashi mu nemi ilimi, kada mu ruxu da kawunanmu, mu zama shugabanni kafin lokaci, domin duk wanda ya yarda ya zama shugaba tun yana qaraminsa to alheri mai yawa zai wuce shi, kamar yadda Imam Shafi’i yake faxa. Yana daga cikin abin da yake tiamaka wa qasqantar da kai, don haka ka yi qoqari a koyaushe ka riqa jin kai xalibin ilimi ne, kuma zaka fa’idantu da kowa, wanda bai kai ba, da wanda yake sa’anka, da wanda yake samanka. Sa’id xan Jubair – Allah ya yi masa rahama – yana cewa : “Mutum ba zai gushe ba yana malami matuqar yana koyo, idan ya bar koyo, ya ji cewa shi ya wadatu da abin da ya sani to a lokacin ya fi zama jahili”. (Tazkiratus Sami’i) Da yawa daga cikin magabata suna fa’idantuwa da junansu, Imam Al – Humaidiy – Allah ya yi masa rahama – xalibin Imamu Ash – Shafi’i ne – ya ce “Na abokanci Shafi’i daga Makka zuwa Misra, Ina qaruwa da shi a wasu mas’aloli, shi kuma yana qaruwa da ni a hadisi”. Imam Ahmad xan Hanbal – Allah ya yi masa rahama – ya ce, “Imam Shafi’i ya ce da mu, ku kun fi ni sanin hadisi, don haka idan hadisi ya inganta, to ku faxa min don in yi aiki da shi”. Yaku ‘yan uwana musulmi, ku nisanci jahilci, haqiqa jahili matacce ne tun kafin ya mutu, ku nemi ilimin addini, domin da shi ne duniya da lahira suke gyaruwa. A qarshe ina kira ga duk wani mai kishin wannan addini na musulunci da waxanda nauyi yake kansu da su gyara manhajar karatu, musamman ma a vangaren addini, saboda wallahi wannan manhajar ba zata yaye xalibai ba sai raunana, babu ilimin addini ingantacce a cikinsa, abin da yake cikinsa na cutarwa yana yawa, maffi munin abin da yake cikinsa kuwa wannan aqida ta Ash’ariyya, wadda ta sava wa Alqur’ani da sunnah da abin da magabata na qwarai suke kai, saboda haka ya wajaba akan masu kishin addini, da duk waxanda suke da iko su gyara wannan tsarin, tun kafin lokaci ya wuce. Ku ji tsoron Allah yaku bayin Allah, ku koyi addininku, kamar yadda ubangijinku ya umarce ku, ku sani aikin ibada ba ya karvuwa har sai ya zama daidai kuma nagari, ba zai zama daidai nagari ba har sai an gina shi akan ilimi




Tags:




At-tahreem