Manufofin huxubar
Bayanin haqqin Maqotaka a musulunci.
Bayyana haqqin maqoci a kan maqocinsa.
Fito da Falalar kyautatawa maqoci.
Jan – kunne da razanarwa akan cutar da maqoci.
Huxuba Ta Farko
Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma muna neman tsarinsa daga shirrin kawukanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar da shi, wanda kuma ya vatar to babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaxai ne ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi Muhammad bawansa ne manzonsa ne. (Ya ku waxanda suka yi imani ku ji tsoron yadda ya cancaci a ji tsoronsa, kada ku mutu face kuna musulmi). (Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicceku daga rai guda xaya, kuma ya ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga garesu (su biyu). Ku ji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya da shi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Ya ku wanxanda suka yi imani ku ku ji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku ayyukanku, kuma ya gafarta muku zunubbanku. Wanda ya bi Allah da Manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawon shiriya shiriyar Annab Muhammad (ﷺ). Kuma mafi shirrin al'amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wani qagaggen abu (addini) bidi'a ce, duk wata bidi'a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta.
‘Yan uwa musulmi : Huxubarmu a yau tana magana ne akan wani maudu’i babba da kowa yake buqatarsa, abu ne mai girma wanda Mala’ika Jibrilu (A.S) ya yi ta yi wa Manzon Allah (ﷺ) wasici da shi, har sai da ya yi zaton za a bashi gado, wannan abu ba komai ba ne face haqqin maqotaka.
Haqiqa – yaku ‘yan uwa – maqoci yana da haqqoqi masu girma a addinin musulunci, waxanda ya wajaba a kiyaye su, a lazimce su, kada a yi sakaci da su.
Maqoci a shari’a shi ne wanda ya maqotace ka, musulmi ne shi ko kafiri, mutum ne nagari ko kuma fajiri, abokin ka ne ko kuwa maqiyinka ne, xan uwanka ne ko ba xan uwanka ba, kai koma waye, in dai ya zauna kusa da kai to ya zama maqocinka yana da haqqi a kanka.
Al – Hafiz Ibnu Hajar – Allah ya yi masa rahama – yana cewa : “sunan maqoci ya haxa musulmi da kafiri, mai bauta wa Allah da fasiqi, aboki da maqiyi, xan gari da baqo, mai amfanarwa da maras amfanarwa, makusanci ne ko wanda yake nesa, gidansa a kusa yake ko a nesa. Maqotaka tana da matakai, wasu sun fi wasu, mafi girman matsayi a maqota shi ne wanda ya haxa siffofin farko gaba xaya (ma’ana ya zama musulmi, mai bauta wa Allah, aboki, xan gari, mai amfanarwa, makusanci, kuma wanda gidansa yake kusa) sannan sai wanda yake bi ye masa a cikin waxannan siffofi har zuwa wanda yake da siffa xaya” (Duba Fathul Bari J 10 Sh 441).
Don haka, Maqocin da gidansa yake jikin naka, ba daidai yake da maqocin da gidansa yake nesa da kai ba, maqocin da yake xan uwanka ne, ba daidai yake da maqocin da yake ba xan uwanka ba, kamar yadda nagarin maqoci ba daidai yake da fasiqin maqoci ba.
Musulunci ya yi wasiyya da maqoci, ya xaukaka darajarsa, maqoci a musulunci yana alfarma da haqqoqi masu yawa. Allah ya yi umarni da kyautata wa maqoci a ayoyi da yawa : Allah ya ce:
وَاعْبُدُوا اللَّهَ وَلَا تُشْرِكُوا بِهِ شَيْئًا وَبِالْوَالِدَيْنِ إِحْسَانًا وَبِذِي الْقُرْبَى وَالْيَتَامَى وَالْمَسَاكِينِ وَالْجَارِ ذِي الْقُرْبَى وَالْجَارِ الْجُنُبِ وَالصَّاحِبِ بِالْجَنْبِ وَابْنِ السَّبِيلِ وَمَا مَلَكَتْ أَيْمَانُكُمْ إِنَّ اللَّهَ لَا يُحِبُّ مَنْ كَانَ مُخْتَالًا فَخُورًا [النساء: 36]
Ma’ana : “Ku bauta wa Allah kada ku yi shirka da shi da wani abu, ku kyautata wa iyaye, da makusanta, da marayu, da miskinai, da maqocin da yake makusanci, da maqocin da yake nesa, da wanda yake kusa da kai, da wanda yake matafiyi, da abin da hannun damanku suka mallaka, haqiqa Allah ba ya son wanda yake mai yawan girman kai mai yawan alfahari” (Annisa’i 36).
An karvo daga Abdullahi xan Umar – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Jibrilu mai gushe ba, yana ta yi min wasiyya aka maqoci, har sai da na yi zaton zai ce a bashi gadona” Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
An karvo daga Abu Hurairata – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Wanda duk ya yi imani da Allah da ranar qarshe to ya faxi alheri ko ya yi shiru. Wanda duk ya yi imani da Allah da ranar qarshe to ya gimama maqocinsa. Duk wanda ya yi imani da Allah da ranar qarshe to ya girmama baqonsa”. Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
Imam Alqali Iyad – Allah ya yi masa rahama – ya ce, “Ma’anar hadisin shi ne duk wanda ya lazimci ayyukan musulunci to ya zama wajibi a kansa ya girmama maqocinsa da baqonsa, ya kyautata musu, saboda bayanin haqqin maqoci, da kwaxaitarwa akan kiyaye shi”. (Sharhin Sahih Muslim ).
An karvo daga Abu Shuraih – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Wallahi bai yi imani ba, Wallahi bai yi imani ba, Wallahi bai yi imani ba!!. Aka ce, “Waye shi ya Manzon Allah (ﷺ)?” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “shi ne wanda maqocinsa bai aminta daga sharrinsa ba”. Bukhari ne ya rawaito.
Imam Abu Muhammad Ibnu Abi Jamra – Allah ya yi masa rahama – ya ce, “Kiyaye haqqin maqota yana cikin cikar imani, mutanen jahiliyya sun kasance suna kiyaye wannan haqqi, kamanta wannan umarni zai yi wu ta hanyar sadar da ayyukan alheri gare shi gwargwadon iko, kamar yi masa kyauta, da sallama, da sakin fuska yayin da aka haxu, da bibiyar halin da ake ciki, da taimakonsa cikin abin da yake buqata, da sauransu, da kare shi daga cutarwa ta kowace hanya” (Fathul Bari J10 sh 442).
An karvo daga Abu Hurairata - – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Haqqin musulmi a kan musulmi shida ne” Aka ce “Meye su ya Rasulallahi? Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “idan ka gamu da shi ka yi masa sallama, idan ya gayyaceka ka amsa masa, idan ya nemi nasiha ka yi masa, idan ya yi atishawa ya godewa Allah ka gaishe shi, idan ya yi rashin lafiya ka je ka duba shi, idan ya mutu ka raka shi”. Muslim ne ya rawaito shi.
Ya ‘yan uwa : Babu ko shakka cutar da maqoci haramun mai tsanani. An karvo daga Abu Shuraih – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Wallahi bai yi imani ba, Wallahi bai yi imani ba, Wallahi bai yi imani ba!!. Aka ce, “Waye shi ya Manzon Allah (ﷺ)?” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “shi ne wanda maqocinsa bai aminta daga sharrinsa ba”. Bukhari ne ya rawaito.
Hadisi ya inganta daga Abu Hurairata – Allah ya yarda da shi – ya ce, An bawa Manzon Allah (ﷺ) labarin wata mace aka ce, “Ya Manzon Allah, wance tana sallar dare, tana yi azumin Ramadana, amma tana da kaifin harshe, tana cutar da maqotanta” sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Babu alheri a tare da ita, ‘yar wuta ce”. Aka sake ce masa : “Wance kuma tana sallar farilla ne kaxai, tana azumin watan Ramadan, tana sadaka da xan abin da take da shi na cukwi, amma ba ta cutar da kowa. A riwayar Imam Ahmad “Ba ta cutar da kowa da harshenta” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Yar Aljannace”. Bukhari ne ya rawaito shi a cikin (Al’adabul Mufrad).
Kai! hadisi ya zo da tsinewa wanda yake cutar da maqocinsa, An karvo daga Abu Juhaifa – Allah ya yarda da shi – ya ce, wani mutum ya kawo wa Manzon Allah (ﷺ) qarar cewa Maqocinsa yana cutar da shi, sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Je ka, ka fitar da kayanka, ka zuba su akan hanya”. Da ya je ya zuba, sai mutane suka riqa wuce wa, suna tsine wa wannan maqoci. Sai wannan maqocin ya ruga wajen Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Ya Manzon Allah mutane suna tsine min” sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Ai Allah ya tsine maka tun gabanin mutane su tsine maka”. Sai ya ce, “Ya Manzon Allah ba zan qara ba”. Bukhari ne ya rawaito shi a cikin littafin “Al – Adab”.
Yanzu – yan uwa – bayan waxannan hadisai da wannan razanarwar akan cutar da maqoci ake samun masu yin sakaci da wannan haqqi, suna cutar da maqotansu!.
A yau abin baqin ciki da takaici an wayi gari muna ganin cututtuka kala – kala na wasa da sakaci da wannan haqqi mai girma, haqqin maqotaka, kamar takurawa maqoci ta hanyar ajiye mota a gaban qofar gidansa don takura masa wajen shiga da fita, da barin ruwa yana kwarara a gaban gidansa, da cutar da maqoci da mummunan wari da xoyi wanda yake fitowa daga wannan magudanar ruwan da sauransu. Hakanan da cutar da maqoci ta hanyar barin shara a qofar gida, ko qetare iyaka cikin haqqinsa, ko shiga iyakarsa, ko yi masa sata, da xauke masa kaya, a wurin aiki ko makaranta ko kasuwa, da sauransu.
Ya tabbata daga Miqdad xan Aswad – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce wa sahabbansa : "Me zaku ce akan sata?" sai sahabbai suka ce "Ai Allah da Manzosa sun haramta ta, don haka haramun ce". Sai Manzon Allah ya ce, "To mutum ya yi sata a gida goma, ya fi sauqi a kan ya yi sata a gidan maqocinsa".
Yana daga cikin cutar da maqoci yi masa ta'adda, da cutar da 'ya'yansa, ko yin wasa da abin hawansa, ko damunsa da qara mai tsanani, kamar sautin waqa, ko hon xin mota, musammam ma a lokacin barci da hutawa, duk waxannan cutarwa ce da aka haramta a tsakanin mutane, don haka haramcinta ga maqoci ya fi fitowa fili.
Yana daga cikin mafi girman cutar da maqoci ha'intar shi da yaudarar shi, kamar bibiyar al'amurarsa don gano laifinsa, ko kai maganarsa wurin maqiyansa, ko leqa masa wuraren alfarmarsa daga saman gida ko da taga, da sauransu, don haka ma narkon azaba mai tsanani ya zo daga Manzon Allah (ﷺ) ga wanda zai riqa yaudara da leqa al'aurar maqotansa. Manzon Allah (ﷺ) ya ce, "Mutum ya yi zina da mata goma ya fi masa sauqi da ya yi zina da matar maqocinsa".
Saboda haka waxanda suke yaudara da ha'intar maqotansa, waxanda suke jiran samun wata dama don su ha'inci maqotansu, su cutar da su, ta hanyar tare matansu, ko yi musu aike, ko kallonsu, su ji tsoron Allah, su sani yin haka laifi ne mai girma, kuma haxari babba.
Allah Maxaukakin Sarki yana cewa :
( وَالَّذِينَ يُؤْذُونَ الْمُؤْمِنِينَ وَالْمُؤْمِنَاتِ بِغَيْرِ مَا اكْتَسَبُوا فَقَدِ احْتَمَلُوا بُهْتَانًا وَإِثْمًا مُبِينًا 58 ) [الأحزاب: 58]
Ma’ana : “Waxanda suke cutar da muminai maza da mata ba ta wani abin da suka yi ba, haqiqa waxannan sun xauki qire da zunubi bayananne” (Al – Ahzab : 58).
Allah ya yi mana Albarka cikin abin da muka ji na Alqur’ani mai girma, Allah ya amfanar da mu da abin da yake cikinsa na ayoyi da zikiri mai girma, haqiqa Allah mai iko ne akan komai.
Huxuba Ta Biyu
Godiya ta tabbata ga Allah, Kyakkyawan qarshe yana ga masu tsoron Allah, Tsira da Aminci su tabbata ga fiyayyen halitta, Manzon Allah (ﷺ) da iyalansa da Sahabbansa da waxanda suka bi su gaba xayansu, har zuwa ranar sakamako. Bayan haka:
Yaku bayin Allah: Hanyoyin cutar da maqoci suna da yawa, amma waxanda suka fi afkuwa su ne : Maqoci ya yi abin da zai cutar da maqocinsa a wajensa, kamar mutum ya shuka bishiya a qofar gidansa amma reshenta ya kai kan kwanon maqocinsa, yana cutar da shi, ko ya gina rijiya da riqa tsotse wa maqocinsa ruwa, ko maqoci ya yi wani wurin sana’a a wajensa, amma yana cutar da maqota da hayaqi ko qura, ko wani sauti maras daxi, ko ya yi window yana leqen gidan maqotansa. Ko ya yi qatuwar katangar da za ta kare musu rana da iska, da sauran iri waxannan ayyuka. Duk waxannan cutarwa ne ya wajaba a kawar da su.
Yana daga cikin babbar cutar da maqoci mutum ya ba da hayar gidansa ga mutanen da ba sa sallah, ba sa tsoron Allah, haqiqa irin waxannan mutane suna takura wa maqota, suna iya yin tasiri akan 'ya'yansu da duk wanda ya cakuxa da su, don haka waxanda suke bawa kafirai da fasiqai haya kusa da gidajen musulmi su ji tsoron Allah, kuma su sani hayar da suke karva haramun ne, sannan musulmi suna yi muku addu'a mummuna, kuna samun alhaki da zunubi.
Yana daga cikin cutar da maqoci, mutum ya hana maqocinsa amfanuwa da kayansa a yanayin da ba zai cutar da shi ba, kamar maqoci ya buqaci zai sanya katako a jikin katangar maqocinsa, katangar da zata iya xaukar wannan katakon, to wajibi ne ya bashi dama, saboda hadisin da Bukhari da Muslim suka rawaito daga Abu Hurairata – Allah ya yarda da shi – Manzon Allah (ﷺ) ya ce, "Kada xayanku ya hana maqocinsa ya kafa katakonsa a jikin katangarsa".
Yana daga cikin cutar wa ga maqota hana su amfanuwa da abin da aka yi don jama’a, kamar hana su xibar ruwa daga qoramu da wuraren da ruwa yake taruwa, ko ya hana su kiwo a jeji, ko yin ciyawa da itace a wuraren da bana kowa ba ne, ko hana su amfanuwa da ma'adinan da suke qasa wanda na kowa – da – kowa ne, kamar gishiri da waninsa. Hadisi ya tabbata a cikin Bukhari da Muslim daga Abu Hurairata – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, "Kada ku hana yin amfani da ruwan da ya rage muku, don ku hana fitowar ciyawa da shi".
‘Yan uwa musulmi : Magabanta na qwarai sun buga kyakkyawan misali wajen kyautatawa maqoci, daga cikin su, akwai wanda Imam Az – Zahbi – Allah ya yi masa rahama – ya ambata a cikin litattafinsa (Siyari A’alamin Nubala’i J 13 sh 433). Ya ce, Wani Maqocin Abu Hamzatas Sukkari ya yi niyyar sayar da gidansa, da aka tambaye shi, “Nawa zai sayar?” sai ya ce, “Dubu biyu kuxin gida, dubu biyu kuma kuxin maqotaka da Abu Hamza”. (ya faxi haka ne saboda irin yadda yasan daxin zama da Abu Hamza). A lokacin da Abu Hamzata ya ji labari, sai ya aiko wa da wannan maqocin nashi dubu huxun da ya nema kyauta, ya ce, kada ka sayar da gidanka”.
Allahu Akbar!, waxannan su ne magabatanmu na qwarai, masu taimaka wa maqotansu a lokacin da suke da buqata, ba irin maqotan da suke jiran wata dama ba, da maqoci zai xaga gidansa, su kuma su saye su qara da nasu, shi kuma ya san inda ya yi!.
Hakanan an rawaito cewa Ibrahim xan Huzaifa ya sayar da gidansa, a lokacin da mai sayen ya so ya kafa shaida cewa ya saya, sai Ibrahim ya ce, “ba zaka kafa shaida ba har sai in zaka sayi maqotakar Sa’id xan Asi daga gareni (ma’ana har sai ya qara masa kuxi saboda wannan gida da ya sayar masa yana kusa da Sa’id xan Asi, shi kuma Sa’id mutum ne mai kyautata wa maqota) sai mutane suka cewa Ibrahim “Yanzu ka tava ganin wanda ya saya ko ya saida maqotaka?” Sai ibrahim ya basu amsa da cewa : “Ba zaku sayi maqotakar wanda idan ka munana masa, shi sai ya kyautata maka, idan ka yi masa wauta, shi sai ya yi haquri da kai, idan ka shiga tsanani, sai ya baka kyauta. Kai! Ba na buqatar cinikinku, ku bani gidana”. Da labari ya je wa maqocin nasa Sa’id sai ya aika masa da dirmahi dubu xari kyauta!.
An tambayi Imam Ahmad xan Hanbal – Allah ya yi masa rahama – dangane da Walid xan Qasim xan Walid, sai Imamu Ahmad ya ce, “Amintacce ne, na rubuta hadisi daga wajensa, kuma maqocin Ya’ala xan Ubaid ne, kuma ni na tambayi Ya’ala xan Ubaid akan maqocinsa Walid xan Qasim xan Walid Al-hamdaniy sai ya ce min “Madallah da wannan mutumin, maqocina ne tsawon shekara hamsin, amma ban tava ganin komai a tare da shi ba sai alheri”. (Duba Siyar ).
Wannan kaxan kenan daga cikin iri yadda magabatanmu suke zama da maqotansu, don haka ina kira ga ‘yan uwa musulmi da mu ji tsoron Allah, ku kyautatawa maqotanmu, mu tuna cewa Allah Maxaukakin Sarki yana cewa :
( وَتَعَاوَنُوا عَلَى الْبِرِّ وَالتَّقْوَى وَلَا تَعَاوَنُوا عَلَى الْإِثْمِ وَالْعُدْوَانِ وَاتَّقُوا اللَّهَ إِنَّ اللَّهَ شَدِيدُ الْعِقَابِ 2 ) [المائدة: 2]
Ma’ana : “Ku taimakekkiniya da junanku akan ayyukan alheri da tsoron Allah, kada ku taimaki juna akan laifi da qetare iyaka (zalunci) ku ji tsoron Allah, Haqiqa Allah mai matsananciyar uquba ne” (Al – Ma’ida : 2). Allah Maxaukakin Sarki ya sa mu dace.