Gaskiya Dokin Qarfe


4472
Surantawa
Haqiqa gaskiya dabia ce me kyau, kuma tana daga cikin cikamakin imani, kuma ita me kammala musuluncin mutum ce, domin Allah yayi umarni da ita , kuma ya yabi masu siffantuwa da ita. Ita gaskiya wata irin dabia ce da take dokin karfe ga maabuta ita, kuma kwalliya ce ga duk wanda ya yafa ta. Ita kuwa karya a bangare daya, alamuce babba ta hainci, kai tana cikin ma alamomin munafinci, kuma bata kara ma bawa komi face nisa da Allah. Bawa be gushewa yana gaskiya har sai Allah ya rubuta shi a matsayin me gaskiya a wajensa, hakanan baze gushe ba yana karya face Allah ya rubuta shi a matsayin makaryaci a wajen sa.

Manufofin huxubar

Koyar da gaskiya a mu’amalar jama’a.

Tsawatarwa daga yin qarya.

Samar da aminciwa tsakanin mutane.

Huxuba Ta Farko

Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma muna neman tsarinsa daga sharrin kawukanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar da shi, wanda kuma ya vatar to babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaxai ne ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi Muhammadu bawansa ne manzonsa ne. (Yaku waxanda suka yi imani ku ji tsoron Allah yadda ya cancaci a ji tsoronsa, kada ku mutu face kuna musulmi). (Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicceku daga rai guda xaya, kuma ya ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga garesu (su biyu). Ku ji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya da shi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Yaku wanxanda suka yi imani ku ku ji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku ayyukanku, kuma ya gafarta muku zunubbanku. Wanda ya bi Allah da Manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawon shiriya shiriyar Annab Muhammadu (ﷺ). Kuma mafi shirrin al'amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wani qagaggen abu (a addini) bidi'a ce, duk wata bidi'a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta".

Bayan haka,

Ya bayin Allah! Ina yi mana wasiyya da jin tsoron Allah, ni da ku gaba xaya. Sannan ku sani asalin tsiyacewar wannan al’umma shi ne rashin yin gaskiya a dukkan al’amura. Tare da cewa gaskiya ita ce tushen dukkan alheri, bisa ga misali gaskiya ita ce ke haifar da tataccen imani na qwarai, wanda mai shi yake dogaro da Allah, ya mai da al’amuransa gare shi. Gaskiya ita ke sa bawa ya zama mai haquri a kan jarraba, mai godiya yayin samun ni’ima, mai gaggawar aikata alheri, mai qauna don Allah, mai qiyayya don Allah. Kai babu wata halayyar imani da za ta tabbata face sai da tabbatar gaskiya. Shi ya sa Allah ya umarci bayinsa muminai da jin tsoronsa, da kuma shiga cikin masu gaskiya sai ya ce:

(يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا اتَّقُوا اللَّهَ وَكُونُوا مَعَ الصَّادِقِينَ119) [التوبة: 119]

(Ya ku waxanda suka ba da gaskiya, ku ji tsoron Allah, kuma ku zama tare da masu gaskiya).

Abin nufi masu gaskiya a imaninsu, da maganganunsu, da ayyukansu, da alqawuransa.

Gaskiya na kawo albarka da qauna, da aminci cikin al’umma. An karvo hadisi daga Hakeem bn Hizam ya ce: “Haqiqa Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Mai saye da mai sayarwa suna da zavin (yiwuwar ciniki ko fasawa) matuqar dai ba su rabu da juna ba (a yayin ciniki). Idan suka yi gaskiya, kuma suka bayyana komai, sai a sanya musu albarka a cikin cinikinsu. Idan kuma suka yi qarya suka rufe gaskiya a cinikin nasu, sai a tafiyar da albarkar cinikin nasu”. Bukhari da Muslim suka ruwaito shi.

Tabbatattun abubuwa kaxai ne ya zama dole su bayyana a cikin tabbatar da mabambantan abubuwan da muke gudanarwa a tsakaninmu, kuma samun yardar Allah ta rataya da haka ne a kodayaushe.

Ambaton gaskiya a cikin Alqur’ani ya zo a ayoyi masu yawa. Wasu na ambata kwaxaitarwa a kan gaskiya, wasu kuma nuna zamantowar gaskiya xan itaciyar tsoron Allah da yin abu dominsa. Daga cikin ayoyin, ba da jimawa ba aka ambaci xaya ba. Sai kuma faxin Allah maxaukakin sarki:

(لِيَجْزِيَ اللَّهُ الصَّادِقِينَ بِصِدْقِهِمْ24) [الأحزاب: ٢٤].

(Domin Allah ya saka wa masu gaskiya da gaskiyarsu).

Kuma Allah ya ce:

(قَالَ اللَّهُ هَذَا يَوْمُ يَنْفَعُ الصَّادِقِينَ صِدْقُهُمْ لَهُمْ جَنَّاتٌ تَجْرِي مِنْ تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا أَبَدًا رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمْ وَرَضُوا عَنْهُ ذَلِكَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ) [المائدة: 119]

(Allah ya ce, «Wannan ita ce ranar da masu gaskiya, gaskiyarsu za ta amfane su, suna kuma da aljannatai waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu, suna madawwama a cikinsu har abada, Allah ya yarda da su, kuma sun yarda da Allah. Wannan shi ne babban rabo).

Don haka gaskiya ce take tseratar da bawa daga azabar Allah a ranar alqiyama.

Kuma Allah mai girma da buwaya ya ce:

(وَبَشِّرِ الَّذِينَ آَمَنُوا أَنَّ لَهُمْ قَدَمَ صِدْقٍ عِنْدَ رَبِّهِمْ2) [يونس: 2] (Kuma ka yi wa waxanda suka imani albishir cewa suna da babban matsayi a wurin Ubangijinsu).

Wato bin gaskiyarsu da gaske shi ya jawo musu samun wannan babban matsayi.

Kuma Allah ya ce,

(وَالَّذِي جَاءَ بِالصِّدْقِ وَصَدَّقَ بِهِ أُولَئِكَ هُمُ الْمُتَّقُونَ33) [الزمر: 33]

“Wanda kuwa ya zo da gaskiya kuma ya gaskata ta, waxannan su ne masu tsoron Allah”.

Allah ma kansa ya siffata Kansa da gaskiya, Ya ce:

(قُلْ صَدَقَ اللَّهُ95) [آل عمران: ٩٥].

(Ka ce Allah ya yi gaskiya).

Kuma Allah ya ce:

فَلَوْ صَدَقُوا اللَّهَ لَكَانَ خَيْرًا لَهُمْ21) [محمد: 21] ((To da sun yi wa Allah gaskiya, lallai da hakan ya zama alheri a gare su(.

Kuma Allah ya ce,

(وَجَعَلْنَا لَهُمْ لِسَانَ صِدْقٍ عَلِيًّا50) [مريم: 50]

(Kuma muka sanya musu ambato na gaskiya, maxaukaki).

Allah maxaukaki ya ce:

(إِنَّ الْمُتَّقِينَ فِي جَنَّاتٍ وَنَهَرٍ54فِي مَقْعَدِ صِدْقٍ عِنْدَ مَلِيكٍ مُقْتَدِر55) [القمر: ٥٤ – ٥٥].

(Haqiqa masu tsoron Allah suna cikin aljannatai da qoramu a cikin mazaunin gaskiya).

Da kuma faxin Allah maxaukakin Sarki:

(وَقُلْ رَبِّ أَدْخِلْنِي مُدْخَلَ صِدْقٍ وَأَخْرِجْنِي مُخْرَجَ صِدْقٍ80) [الإسراء: ٨٠].

(Kuma ka ce: “Ubangiji ka shigar da ni mashiga ta gaskiya, kuma ka fitar da ni mafita ta gaskiya).

Abin nufi a wannan aya shi ne, ka sanya dukkan wani wurin shiga ta, da fita ta, ya zama cikin biyayya gare ka ne, da neman yardaarka.

Ya bayin Allah! Gaskiya nau’o’i ce da yawa. Akwai gaskiya a magana, da gaskiya a aiki da kuma gaskiya a hali.

Allah maxaukakin sarki ya ce:

(إِنَّمَا الْمُؤْمِنُونَ الَّذِينَ آَمَنُوا بِاللَّهِ وَرَسُولِهِ ثُمَّ لَمْ يَرْتَابُوا وَجَاهَدُوا بِأَمْوَالِهِمْ وَأَنْفُسِهِمْ فِي سَبِيلِ اللَّهِ أُولَئِكَ هُمُ الصَّادِقُونَ15) [الحجرات: 15]

(Haqiqa ba wasu ba ne muminai sai waxanda suka ba da gaskiya da Allah da Manzonsa, sannan ba su yi kokwanto ba, suka kuma yi yaqi da dukiyoyinsu da rayukansu a cikin hanyar Allah, waxannan su ne masu gaskiya).

Sannan kuma mafi xaukakar matakin gaskiya shi ne matakin Siddiqanci wato cikar jawuwa ga manzon, tare da cikar tace aiki ga wanda ya aiko Manzon wato Allah.

Ya ku bayin Allah! Ku yi gaskiya, domin haqiqa gaskiya tsira ce daga kowane abin qi, kuma hanyar isa ce ga ayyukan kirki, ayyukan kirki kuma na shiryarwa zuwa ga aljanna.

Ya ‘yan’uwa masu sauraro ina neman gafarar Allah gare ni da ku daga kowane irin zunubi, kuma ku nemi gafararsa haqiqa shi Allah mai yawan gafara ne, mai yawan jinqai ne.

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, kuma kyakkyawan qarshe yana ga masu tsoron Allah. Kuma babu uquba sai ga azzalumai. Tsira da aminci su tabbata a kan mafi xaukakar manzanni, Annabinmu Muhammad, da iyalansa da sahabbansa, da duk wanda ya bi shiriyarsa, kuma ya yi kira irin kiransa har zuwa ranar sakamako.

Bayan haka: Ya ‘yan’uwa musulmai, tabbas musulunci ya kere dukkanin wasu dokoki, kuma ya murqushe qarya da maqaryata. Qarya tambarin ha’inci ce, kai uwa uba ma, qarya alama ce daga alamomin munafunci. Manzon Allah ya ce: “ Alamomin munafuqi guda uku ne, idan ya yi magana ya yi qarya, idan ya yi alqawari ya sava, idan aka amince masa ya yi ha’inci”.

Sannan kuma sam-sam musulunci da qarya ba sa haxuwa, don haka matuqar dai da imani mai qarfi, da kuma tsoron watsi da daraja, da fatali da addini, ba za ka ga musulmi ya xabi’antu da qarya da yaudara ba.

Ya ku bayin Allah! Duk wanda ya kalli halin da mutane suke rayuwa a cikinsa a yau, zai ga gazawarsu a fili ta vangaren gaskiya. Ina ganin ba komai ya jawo haka ba sai raunin imani a zukata da kuma tsananin son duniya. Tabbas Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Gaskiya nutsuwa ce, qarya kuwa fargaba ce”. Ahmad da Tirmizi ne suka rawaito shi.

Yana daga cikin qarairayi mabayyana: Na farko shi ne qaryar iyaye ga ‘ya’yansu, tare da cewa addininmu ya nuna cewa dole ne a guji yin qarya a cikin tarbiyyar ‘ya’ya, domin su tashi a cikin gaskiya kuma su saba da ita. Wanda hakan kuma zai sa su qarfin hali a wajen faxar gaskiya da kuma aiki da ita. Sahabin Annabi, Abdullahi Xan Amir, ya ce: Wata rana babata ta kira ni, a lokacin ina qarami a lokacin Manzon Allah (ﷺ) yana zaune, sai ta ce da ni, "Zo ungo". Sai manzon Allah ya tambaye ta ya ce, "Me za ki ba shi?" Sai ta ce, "Dabino zan ba shi". Sai ya ce da ita, "Da ba ki ba shi komai ba, da an rubuta miki qarya”.

Kuma sahabin Annabi, Abu Huraira ya ce: “Haqiqa manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Duk wanda ya kira yaro ya ce da shi, zo ungo, sannan sai bai ba shi komai ba, to ya yi qarya”.

Ya ke ‘yar’uwa, da irin wannan shiryarwar ta manzon Allah ne ya dace a tarbiyyanci ‘ya’ya domin su sami rainon musulunci tsantsa.

Abu na biyu, shi ne yaxuwar qarya a tsakanin mutane a zantukansu da kuma ayyukansu, ga shi kuma haka na daga cikin manya-manyan zunubai. Allah maxaukakin sarki Yana cewa:

فَنَجْعَلْ لَعْنَةَ اللَّهِ عَلَى الْكَاذِبِينَ61) [آل عمران: 61]) (Sannan kuma mu sanya tsinuwar Allah a kan maqaryata).

Kuma a cikin Sahihul Bukhari da Muslim, an karvo daga Anas xan Malik ya ce: “Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Abubuwa uku duk wanda yake yin su ya zama munafuqi, idan ya yi zance sai ya yi qarya, idan ya yi alqawari sai ya sava, idan kuma aka amince masa ya yi ha’inci".

Abu na uku, yaxuwar karya alqawari, ba tare da wani uzuri karvavve ba. Kamar misali, ku yi alqawari da wani qarfe takwas, sai ya zo qarfe tara ya gabatar maka da uzurin ya biya ne ta wani wuri ya yi saye-saye. Wani babban abin baqin cikin ka ga waxanda suke da kama ta kamala da alheri, amma sai ka ga sava alqawari ya zama ba komai ba a wurinsu.

Sannan kuma savawa ‘ya’ya alqawarin sayo musu ko ba su wani abu ma na daga cikin sava alqawari. Abdullahi xan Mas’ud ya ce, "Qarya ba ta dace ba ko da wasa ko ba da wasa ba. Ko da kuwa wani ya yi wa xansa alqawarin wani abu ne, sannan kuma ya qi cika masa.

Abu na gaba shi ne, cin amana da ha’inci. Ma’aikaci ba ya zuwa wajen aikinsa da wuri, kuma in ya je ba ya yin aikinsa yadda ya dace, shi ne karatun jarida, ko kallon talabijin, ko yin waya da amsa ta, kai sai ya rasa wai shin da wane haqqi yake karvar albashin nasa?

Abu na biyar shi ne algus da voye kaya, wato abin sayarwa.

Na shida kuwa shi ne, qaryar talauci da kiran babu don son tara abin duniya. An karvo daga Abu huraira Allah ya yarda da shi ya ce: “manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Wanda yake roqon mutane don tara abin duniya yana roqarwa kansa garwashin wuta ne, ko dai ya qaranta ko kuma ya yawaita, (shi ya so).

Rufewa juna, a yayin aure, tsakanin mai neman da wacce yake neman aurenta. Kowanne a cikinsu yana qoqarin rufe aibunsa, na halitta ko na halayya. Ya kuma kambama kansa ta vangaren yabo wanda hakan na tafiyar da albarkar aure ya lalatar da ita.

Ya bayin Allah! ‘yan’uwanmu ‘yan kasuwa Allah ya shirye su, su suka fi kowa afkawa a wannan sabo su yi qarya game da kuxin abin sayarwa, su yi a kan samfirin abin sayarwa, wani lokacin ma su haxa duka. Mafi munin haka kuwa qarawa da rantsuwa a kan qaryar da suka yi. Allah ka kiyaseh mu wannan ganganci.

Manzon Allah (ﷺ) ya qirga wannan savo a cikin manya-manyan savon da suke halaka masu yin su. An karvo daga Abdullahi xan Amr, daga Annabi, (ﷺ) ya ce: “Manya-manyan laifuka su ne; yin tarayya da Allah, da wulaqanta iyaye, da kisan kai, da kuma rantsuwar da ke cusa mai yinta cikin wuta, wato rantsuwa a kan qarya”. Bukhari ne ya rawaito shi.

Ya bayin Allah! Ta yaya kuwa Allah zai sa albarka a kasuwancin maqaryaci? Don haka mu ji tsoron Allah mu kiyaye shi a kowane hali.

Ya bayin Allah! Bin dokokin Allah dole ne, saboda haka ya zama lallai ku yi riqo da gaskiya a kowace irin sana’a. Kuma mu dimanci yin gaskiya ga duk abokan hulxarmu, in mun tabbata a kan haka za mu ga buxi da yalwar arziqi a kai a kai. Allah ya ce:

(وَلَوْ أَنَّ أَهْلَ الْقُرَى آَمَنُوا وَاتَّقَوْا لَفَتَحْنَا عَلَيْهِمْ بَرَكَاتٍ مِنَ السَّمَاءِ وَالْأَرْضِ وَلَكِنْ كَذَّبُوا فَأَخَذْنَاهُمْ بِمَا كَانُوا يَكْسِبُونَ96) [الأعراف: 96] (Da dai mutanen alqaryu sun yi imani, sun kuma ji tsoron Allah, to da mun buxe musu albarkatai daga sama da kuma qasa).

Kuma Allah ya ce:

(وَمَنْ يَتَّقِ اللَّهَ يَجْعَلْ لَهُ مَخْرَجًا 2وَيَرْزُقْهُ مِنْ حَيْثُ لَا يَحْتَسِبُ 3)[الطلاق: ٢ – ٣].

(Duk wanda ya ji tsoron Allah, zai sanya masa mafita (daga qunci), kuma ya azurta shi ta inda ba ya tsammani).

Kuma qaya a shaida xaya ce daga cikin qarairayin da suka wajaba a gujewa. Allah Yana cewa:

(وَاجْتَنِبُوا قَوْلَ الزُّورِ30) [الحج: 30]

(Kuma ku nisanci faxar shaidar zur).

Allah Ya qara faxa a wata ayar:

(وَلَا تَكْتُمُوا الشَّهَادَةَ وَمَنْ يَكْتُمْهَا فَإِنَّهُ آَثِمٌ قَلْبُهُ وَاللَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ عَلِيمٌ283) [البقرة: 283]

)Kada ku voye shaida, duk kuwa wanda ya voye ta, to haqiqa shi mai kangararriyar zuciya ne, kuma Allah masanin abin da kuke aikatawa ne).

Ya bayin Allah! Gaskiya na da matuqar amfani, a duniya da lahira, daga cikin amfaninta sun haxar da:

Na farko shigar da mai yinta gidan aljanna. An tambayin Annabi, (ﷺ), menene aikin ‘yan aljanna? Sai ya ce, “Gaskiya”. Iman Ahmad ne ya rawaito shi.

Na biyu kuvutar da mai yin ta daga halaka. Ya zo a cikin hadisin mutanen nan da dutse ya toshe musu qofar kogon da suka shiga cewa xayansu, ya ce da su, “Babu abin da zai tseratar da ku sai gaskiya, kowannenku ya roqi Allah da abin da ya san ya yi gaskiya a cikinsa. Bukhari ne ya rawaito shi.

Na uku, nagartar zuciya, duk wanda ya yi gaskiya a ayyukansa na fili to tabbas kuwa zuciyarsa na cike da gaskiyar nufi, domin kuwa komai bawa zai yi, to sai nufi ya rigaye shi.

Na huxu, gadarwa da mai yinta nutsuwa da kwanciyar rai.

Na biyar, kuvutar da mai yinta daga afkawa cikin fitintinun rayuwa.

Na shida, takan zama ga mai yinta, tushen aikata ayyukan alheri.

Na bakwai, korewa mai yinta siffantuwa da munafurci.

Na takwas, datar da mai yin a wajen hasashe da hangen nesa.

Na tara, qarfafar hujjar mai riqo da ita da kuma yinta.

Na goma, samun yabo da kirari da kyakkyawan ambato daga mutane.

Na sha xaya, jawo albarkar kasuwanci da san’o’i.

Allah ka sa mu a cikin bayinka masu gaskiya, kuma ka tsare mu daga yin qarya da biyewa masu yinta amin.





Tags:




Abdulazeez Al-ahmad