Rahama


5166
Surantawa
Haqiqa jin qai da rahama siffofine guda biyu daga cikin siffofin Ubangiji maxaukaki, kuma sunayene daga cikin sunayensa mafiya kyau, shi yasa ya siffantu dasu, kuma ya umarci bayinsa da siffantuwa dasu, domin samar da tausayi da rangwame tsakaninsu.

Manufofin huxubar

Kwaxaitar da mutane akan su siffantu da siffar rahama, domin siffa ce da Allah ya siffantu da ita a bisa kamala.

Shiryar da Mutane abisa fatan samun rahama.

Nesantar xebe tsammani da samun rahama.

Huxuba Ta Farko

Dukkan yabo ya tabbata ga Allah muna gode masa muna neman taimakonsa muna neman gafararsa muna neman tsarinsa daga sharrance-sharrancen kawunanmu da kuma munanan aiyukanmu. Wanda duk Allah ya shirye shi babu mai vatar da shi wanda duk ya vatar da shi babu mai shiryar da shi, ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kaxai ba shi da da abokin tarayya, ina shaidawa kuma Annabi Muhammad bawansane kuma manzonsane.

“Ya ku waxanda sukai imani kuji tsoron Allah matuqar tsoronsa kada ku kuskura ku mutu face kuna musulmai”.

“Ya ku mutane kuji tsoron Ubangijinku wannan da ya halicceku daga rai guda xaya sannan ya halitta masa matarsa daga, ya yaxa zuriyya daga su biyun maza da mata, don haka ku ji tsoron Allah wannan da kuke yin roqo da shi da kuma zumunci haqiqa Allah ya kasance a kanku mai tsaro”.

“Ya ku waxanda suka yi imani kuji tsoron Allah ku faxi magana ta dai dai sai Allah ya gyara muku aiyukan ku kuma ya gafarta muku zunubanku duk wanda ya bi Allah da Manzonsa haqiqa ya rabauta rabo mai girma”

Bayan haka:

Ya ku bayin Allah! Haqiqa jin qai da rahama siffofine guda biyu daga cikin siffofin Ubangiji maxaukaki, kuma sunayene daga cikin sunayensa mafiya kyau. Kamar yadda sunan “Arrahmaan” ya fi kaiwa matuqa akan sunan “Arraheem” domin shi sunan “Arrahmaan” yana nufin mai rahma gamammiya da ta shafi dukkanin halittu a nan gidan duniya, da kuma muminai a can gidan lahira. Amma sunan “Arraheem” yana nufin mai rahma ga bayinsa muminai a can ranar alqiyama. Wannan ita maganar mafiya yawancin malamai.

A cikin rahmarsa ne muke jujjuyawa inda muke so ba tare da iyaka ba. Ubangiji maxaukaki ya ce,

(مَا يَفْتَحِ اللَّهُ لِلنَّاسِ مِنْ رَحْمَةٍ فَلَا مُمْسِكَ لَهَا وَمَا يُمْسِكْ فَلَا مُرْسِلَ لَهُ مِنْ بَعْدِهِ وَهُوَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ2) [فاطر: 2]

(Idan Allah ya buxe qofar rahmarsa ga bayinsa to babu mai riqeta. Idan kuma ya riqe ta babu mai buxe ta bayan shi. Kuma shi ne mabuwayi mai hikima).

Malam Shanqiyxiy (R.A) ya ce: “Rahmar da ake nufi a wannan ayar ta haxa dukkan abin da Allah yake jin qan bayi da shi na ni’imarsa ta duniya ko ta lahira, kamar saukar musu da ruwan sama. Kamar yadda Allah (S.W.T) ya ce,

(فَانْظُرْ إِلَى آَثَارِ رَحْمَةِ اللَّهِ كَيْفَ يُحْيِي الْأَرْضَ بَعْدَ مَوْتِهَا إِنَّ ذَلِكَ لَمُحْيِي الْمَوْتَى وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِير50)ٌ [الروم: 50]

(Ka yi duba izuwa gurbin rahmar Ubangiji, ka ga yadda yake rayar da qasa bayan mutuwarta).

Da faxin Maxaukakin sarki:

(وَهُوَ الَّذِي يُرْسِلُ الرِّيَاحَ بُشْرًا بَيْنَ يَدَيْ رَحْمَتِهِ57) [الأعراف: ٥٧].

(Shi ne wanda yake turo da iska wacce take mai yin bishara da rahamarsa (ruwan sama)). Ya ce a wani ayar,

(وَرَحْمَتِي وَسِعَتْ كُلَّ شَيْءٍ فَسَأَكْتُبُهَا لِلَّذِينَ يَتَّقُونَ وَيُؤْتُونَ الزَّكَاةَ وَالَّذِينَ هُمْ بِآَيَاتِنَا يُؤْمِنُونَ156) [الأعراف: 156] (Rahamata ta wadaci dukkan komai. Sannan zan bayar da ita ga waxannan da suke jin tsorona kuma suke bayar da zakka da waxannan da suke yin imani a game da ayoyinmu).

Wannan rahamar wadda ta wadaci dukkan komai, rahama ce ta gabaxaya, domin babu wani abin halitta face wannan rahama ta shafe shi a nan duniya ko kuma a lahira.

Ya ku Musulmi! Haqiqa ana buqatar da mu yi rahama da tausayi a junanmu saboda daliali dadama.

Daga cikin dalilan akwai cewa, Allah shi ne ya umarcemu dayin hakan, don haka ya zama dole a gare mu mu bi umarninsa. Kamar yadda Annabi (ﷺ) ya faxa a halin yana kan mimbarinsa: “Ku ji qai, kuma sai a ji qanku. Kuma ku yi gafara kuma sai a yi muku gafara azaba ta tabbata ga masu qin jin magana, masu dagewa akan abinda suka aikata na savo alhalin sun sani” [Ahmad da Xabarani].

Idan muka xabi’antu da wannan xabi’a mai kyau sai Allah ya kawo wanda zai jiqanmu a nan duniya da lahira, kuma daman shi Allah shi yake jin qan mu. An karvo daga Abdullahi xan Amr xan Ass, daga Annabi (ﷺ) ya ce: “Masu jin qai Allah mai jin qai yana jin qansu, don haka ku ji qan waxanda suke qasa, sai Allah wanda yake sama ya ji qanku”. [Imam Ahmad da Abu Dawud da Tirmizi da al-Hakim suka ruwaito shi. Tirmizi ya ce, wannan hadisin kyakkyawa ne ingantacce].

An karvo daga Jarir ya ce, “Na ji Manzon Allah (ﷺ) yana cewa: “Duk wanda baya jin qan mutane ba, to shi ma Allah ba zai ji qansa ba”. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.

Daga cikin nau'ukan rahamar Ubangiji, akwai samar da halittu abisa mafi kyawun tsari da kuma karrama xan Adam da fifita shi bisa mafi yawan halittu. Allah maxaukakin sarki ya ce,

(لَقَدْ خَلَقْنَا الْإِنْسَانَ فِي أَحْسَنِ تَقْوِيمٍ4) [التين: 4]

Ma’ana: (Haqiqa mun halicci mutum a cikin mafi kyawun zubi).

Sannan da faxinsa,

(وَلَقَدْ كَرَّمْنَا بَنِي آَدَمَ وَحَمَلْنَاهُمْ فِي الْبَرِّ وَالْبَحْرِ وَرَزَقْنَاهُمْ مِنَ الطَّيِّبَاتِ وَفَضَّلْنَاهُمْ عَلَى كَثِيرٍ مِمَّنْ خَلَقْنَا تَفْضِيلًا70) [الإسراء: 70]

(Haqiqa mun girmama ‘yan Adam, mun xauke su a kan tudu da teku kuma mun azurta su daga daxaxa abubuwa, sannan muka fifita su sosai akan dayawa daga cikin waxanda muka halitta).

Yana daga cikin rahamarsa ya xorawa kansa nauyin azurta bayinsa. Bai xora nauyin wani akan wani ba. Ba xora nayin abin cin ‘ya’ya akan iyayensu ba, hakanan suma iyayen ba bar su da ‘ya’yansu ba. A’a kowa yana rayuwa ne qarqashi inuwar falalarsa da kyautatawarsa. Allah ya ce,

(وَكَأَيِّنْ مِنْ دَابَّةٍ لَا تَحْمِلُ رِزْقَهَا اللَّهُ يَرْزُقُهَا وَإِيَّاكُمْ وَهُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ60) [العنكبوت: 60]

(Da yawa daga cikin halitta ba sa xauke da arzikinsu. Allah ne ke azurtasu da kuma ku. Kuma shi ne mai ji kuma masani).

Ubangiji ya ce:

(وَمَا مِنْ دَابَّةٍ فِي الْأَرْضِ إِلَّا عَلَى اللَّهِ رِزْقُهَا وَيَعْلَمُ مُسْتَقَرَّهَا وَمُسْتَوْدَعَهَا كُلٌّ فِي كِتَابٍ مُبِينٍ6) [هود: 6]

(Babu wata dabba a cikin qasa face arzuqinta na wajen Allah kuma ya san matabbatarta da makwantarta duk wannan yana cikin littafi mabayyani).

Yana daga cikin rahamarsa da ya hore mana duk abin da yake cikin sama da qasa domin kyautatuwar rayuwarmu, da kuma tsarin rayuwarmu. Allah ya ce,

(وَسَخَّرَ لَكُمُ اللَّيْلَ وَالنَّهَارَ وَالشَّمْسَ وَالْقَمَرَ وَالنُّجُومُ مُسَخَّرَاتٌ بِأَمْرِهِ إِنَّ فِي ذَلِكَ لَآَيَاتٍ لِقَوْمٍ يَعْقِلُونَ12) [النحل: 12].

Ma’ana: “Ya hore muku dare da wuni, da rana da wata da taurari dukkanin wannan da umarninsa. Lalle a cikin wannan akwai ayoyi ga mutanen da suke da hankali).

Allah (S.W.T) ya ce,

(هُوَ الَّذِي خَلَقَ لَكُمْ مَا فِي الْأَرْضِ جَمِيعًا29) [البقرة: ٢٩].

(Shi ne wannan da ya halitta muku duk abin da yake bayan qasa baki xaya).

Ya ku musulmi yana daga cikin rahamar Allah aiko mana da manzanni masu bushara masu gargaxi. Suna sanar da bayi Ubangijinsu, suna kiransu zuwa ga bautawa Allah shi kaxai. Suna sanar da su gaskiya, suna tsoratar da bin hanyar vata da varna. Allah maxaukaki ya ce,

(لَقَدْ أَرْسَلْنَا رُسُلَنَا بِالْبَيِّنَاتِ وَأَنْزَلْنَا مَعَهُمُ الْكِتَابَ وَالْمِيزَانَ لِيَقُومَ النَّاسُ بِالْقِسْطِ وَأَنْزَلْنَا الْحَدِيدَ فِيهِ بَأْسٌ شَدِيدٌ وَمَنَافِعُ لِلنَّاسِ وَلِيَعْلَمَ اللَّهُ مَنْ يَنْصُرُهُ وَرُسُلَهُ بِالْغَيْبِ إِنَّ اللَّهَ قَوِيٌّ عَزِيزٌ25) [الحديد: 25]

(Haqiqa mun turo manzannin mu da hujjoji bayyanannu, sannan mun saukar musu da littafi da mizani (abin awo), don mutane su tsayar da gaskiya. Muka saukar da qarfe, a cikinsa akwai qarfi mai tsanani, da kuma abin amfani ga mutane, don Allah ya san waye wanda zai taimake shi da manzanninsa a fake).

Maxaukakin sarki ya ce,

(رُسُلًا مُبَشِّرِينَ وَمُنْذِرِينَ لِئَلَّا يَكُونَ لِلنَّاسِ عَلَى اللَّهِ حُجَّةٌ بَعْدَ الرُّسُلِ وَكَانَ اللَّهُ عَزِيزًا حَكِيمًا165) [النساء: 165]

(Manzanni masu bushara da gargaxi don kada ya kasance mutane suna da wata hujja a wajen Allah bayan manzanni sun zo).

Yana daga cikin rahamarsa da ya yi mana shi ne, turo mana shugaban mutanen farko da na qarshe, kuma shugaban masu tsoron Allah Annabi Muhammad (ﷺ) wanda manzancinsa gamammiyar rahama ce ga duniya baki xaya. Kuma littafin da aka saukarmasa gargaxi ne ga duniya duka. Allah maxaukakin sarki ya ce:

(وَمَا أَرْسَلْنَاكَ إِلَّا رَحْمَةً لِلْعَالَمِينَ107) [الأنبياء: 107]

(Bamu aiko ka ba face rahama ga mutanen duniya baki xaya).

Yana daga cikin rahamarsa ga bayinsa, ita kanta wannan shari’a cikakkiya, mai cikakken tsari da kamala, mai tattare kyawawan xabi’u. Ubangiji ya sanya ta ta zamana ta dace da kowa ne zamani da kowa ce al’umma. Allah ta’ala ya ce,

ﭽ ﭻ ﭼ ﭽ ﭾ ﭿ ﮀ ﮁ ﮂ ﮃ ﮄ ﮅﮆ ﭼ [المائدة: ٣].

(A yau ne na cika muku addininku, kuma na cika ni’imata gareku, kuma na yarje muku musulunci shi ne addini).

Allah ya ji tausaya mana da wannan shari’ar haxaxxa, wacce Allah ya xauke qunci da tsanani daga cikinta, irin wanda yake cikin shari’o’in da suka gabace ta. Allah yana faxa dangane da siffanta Annabinsa:

(الْيَوْمَ أَكْمَلْتُ لَكُمْ دِينَكُمْ وَأَتْمَمْتُ عَلَيْكُمْ نِعْمَتِي وَرَضِيتُ لَكُمُ الْإِسْلَامَ دِينًا) [الأعراف: ١٥٧]

(Kuma yana sauke musu nauyi da ququmin da yake kansu).

Wannan shari’a ce da aka gina ta akan sauqi da sauqaqewa:

(يُرِيدُ اللَّهُ بِكُمُ الْيُسْرَ وَلَا يُرِيدُ بِكُمُ الْعُسْرَ185) [البقرة: ١٨٥].

(Allah yana nufin sauqi gare ku, baya nufin tsanani).

Annabi (ﷺ) yana cewa sahabbansa: “Ku sassauta kada ku tsananta, kuyi bishara kada ku kore”. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.

Ya ku bayin Allah! Haqiqa rahamar Annabi zavavven Allah wacce aka ruwaito ta hanyoyi da yawa kuma wanda yake nesa da wanda yake kusa duk sun shaida da ita. Allah ya yi gaskiya cikin faxinsa:

(لَقَدْ جَاءَكُمْ رَسُولٌ مِنْ أَنْفُسِكُمْ عَزِيزٌ عَلَيْهِ مَا عَنِتُّمْ حَرِيصٌ عَلَيْكُمْ بِالْمُؤْمِنِينَ رَءُوفٌ رَحِيمٌ128) [التوبة: 128]

(Haqiqa wani manzo ya zo muku daga cikinku, duk abin da zai cutar da ku baya son sa, kuma yana yin kwaxayin alheri a gare ku shi mai tausayi ne mai jin kai dangane da muminai).

Yana daga cikin irin jin qan Annabi (ﷺ)

Akan abokan gabasa: Yayin da ya kirawo mutanen garin Xa’ifa zuwa ga Musulunci sai basu amsa masa ba, suka sanya wawayensu suka cutar da shi, har takai Annabi (ﷺ) ya fito dugadugansa masu albarka suna zubar jini. Allah ya turo Mala’ikan da yake kulawa da duwatsu yana don ya zartar da duk wani umarni da Annabi zai yi masa, yana cewa, “In ka so zan jefo musu manyan duwatsu guda biyu su rufe su”. Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Kada ka aikata haka, babu mamaki Allah ya fitar da wanda zai bauta masa daga cikin tsatsonsu".

Rahamarsa ga Jahilai: Wani Balaraben qauye ya yi fitsari a cikin masallaci, sai sahabbai suka tashi don su hora shi. Sai Ma’aiki ya hana su. Har sai da ya gama fitsarinsa, sannan Manzo Allah (ﷺ) ya ce, "A kawo cukin guga na ruwa a kwarara akan fitsarin". Sannan sai ya ce da sahabbai, "Ku sani fa an taso ku ne don ku zama masu sassauci ba a tasu ku ba don ku zama masu tsanani, don haka ku sassauta kada ku tsananta". Sai ya ce da Balaraben qauyen: "Waxannan masallatan an gina su ne kawai domin ambaton Allah, da Sallah”. Bayan wannan baqauye ya yi samu cikakkiyar tarbiyya ta musulunci ya zan yana cewa, “Na fansheka da uwata da Ubana ya Ma’aikin Allah! Bai kyare ni ba, bai hantare ni ba”.

Hakanan kuma wani baqauyen shi ma ya zo wajen Manzon Allah (ﷺ) ya caka faratansa a kafaxar Manzon Allah (ﷺ). Annabi ya waiwaya ya kalle shi yana murmushi).

Wani kuma zai bawa Manzon Allah (ﷺ) bashi, sai kuma ya zo karvar bashinsa kafin wa’adin ya cika, kuma ya ce ya Muhammad ba ni bashina domin ku iyalan Abdulmuxxalib kuna da taurin bashi. har sahabbai su harzuqa, su tashi domin dukansa, sai Manzon Allah (ﷺ) ya hana su, kuma ya ce “Lalle mai gaskiya yana da ikon magana akan haqqinsa”.

Rahamarsa ga sauran muminai: An karvo daga Malik xan Huwairis (R.A) ya ce: “Mun zo wajen Manzon Allah (ﷺ) kuma mu duka samari ne tsarekun juna. Muka zauna a wajensa har tsawon kwana ashirin. Sai Annabi Muhammad ya fahimci kamar muna da buqata zuwa ga iyalanmu, sai muka faxa masa hakan. Ya kasance mai sauqin hali ne da tausayi. Sai ya ce: "Ku koma wajen iyalanku, ku koyar da su addinin musulunci. Kuma ku yi sallah kamar yadda kuka ganni ina sallah. Kuma idan lokacin sallah ya yi ku umarci xayan ku ya yi kiran sallah, sannan babbanku ya yi maku limanci".

Ya ku bayin Allah, ku sani tausayin shugaba akan al’ummar Annabi Muhammad (ﷺ) tilas ne.

Annabi (ﷺ) yana addu'a yana cewa, “Ya Allah duk wanda ya sami wani shuganci na al'ummata, kuma ya tausaya masu, to ka tausaya masa. Wanda ya shugabanci wani al'amari na al'umma ta sannan ya quntata musu, to shi ma ka quntata masa”. (Bukhari da Muslim).

Haka kuma musulunci yayi bayanin irin rahamar da za ayiwa dabbobi da kuma hani akan cutar da su kamar:

Tsare su ba tare da ba su abin ciba: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Wata mata ta shiga wuta saboda wata mage da ta tsare ta har ta mutu. Ba ta ba ta abinci ba, kuma ba ta barta ta nema da kanta ba".

Haxa dabbobi faxa. Yin haka haramun ne. Annabi (ﷺ) ya hana a riqa haxa faxa tsakanin dabba da dabba.

Koyon harbi akan wata dabba. Yin haka shi ma haramun ne. Domin Manzon Allah (ﷺ) ya tsinewa wanda ya ke koyon harbi akan wani abu mai rai).

Kashe daba don wasa kwai. Wannan shi ma haramun ne a musulunci. Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Lalle tsuntsu zai nuna rashin yardar sa ranar gobe alqiyama, ya riqa cewa “Ya Ubangiji wane ya kashe ni don wasa kwai, ba don ya yi amfani da ni ba”.

Kuma har a wajen yanka Manzon Allah ya ce: “Idan za ku yi kisa (hadi) to ku kyautata kisan. Idan kuma za ku yi yanka, to ku kyutata abin yankan. Kuma xayanku ya wasa abin yankansa, domin ya hutar da abin da zai yanka".

Sannan Manzon Allah (ﷺ) ya ga wani mutum ya danne akuyarsa da qafarsa, kuma yana wasa wuqarsa, sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce masa: “Tir da kai! Har sau biyu za ka kashe ta!! Mai ya hana ba ka wasa wuqar ka ba kafin ka danne ta domin yanka?”.

Ina faxin abinda kuke ji, ina kuma neman gafarar Allah da ni da ku, daga dukkan zunubi, ku nemi gafarar sa domin shi mai gafara ne mai jin qai.

Yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyen halitta Annabin Muhammad da alayensa da sahabbansa, da duk waxanda suka bi tafarkin su har zuwa tashin qiyama. Bayan haka:

Ku sani ya ku musulmi, babu wanda yake da tabbacin dawwamar wani hali da yake ciki, domin wadata tana zuwa bayan talauci. Haka kuma talauci yana zuwa bayan wadata. Rashin lafiya tana zuwa bayan lafiya, haka kuma lafiya tana zuwa bayan rashin lafiya. Don haka babu wani hali da yake dawwama ga mutum, Allah (S.W.T) ya na cewa:

(قُلِ اللَّهُمَّ مَالِكَ الْمُلْكِ تُؤْتِي الْمُلْكَ مَنْ تَشَاءُ وَتَنْزِعُ الْمُلْكَ مِمَّنْ تَشَاءُ وَتُعِزُّ مَنْ تَشَاءُ وَتُذِلُّ مَنْ تَشَاءُ بِيَدِكَ الْخَيْرُ إِنَّكَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ26) [آل عمران: 26]

(Ka ce, Ya Allah mamallakin mulki, kana bayar da mulki ga wanda kake so, kana karve mulki ga wanda kake so, kuma kana buwayar da wanda kake so, kuma kana qasqantar da wanda kake so ga hannunka alheri yake. Lallai ne kai akan kowane abu, mai ikon yi ne).

Manzon Allah (ﷺ) ya ga aba Mas’ud ya na dukan xansa, sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce masa “Kaji tsoron wanda yafi ka qarfi, akan sa”.

Sannan babu makawa sai mun dinga yin wannan tausayin a aikace, kamar yadda wani mutum ya zo wajen Annabin Allah yana kukan qeqashewar zuciyarsa, sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce masa “Ka shafi kan maraya, kuma kaciyar da miskini".

Sannan ka riqa tuna batun sakamako, domin duk abin da ka yi, shi za a yi maka. Annabi (ﷺ) ya ce, “Duk wanda ya yayewa wani baqin cikinsa, a nan duniya, to shi ma Allah zai yaye masa baqin cikinsa a lahira. Sannan kuma duk saurayin da ya taimaki tsoho, shi ma Allah zai haxa shi da wanda zai karrama shi idan ya tsufa.

Ya ku bayin Allah! Ribar rahama shi ne samun tausayi da soyayya tsakanin ‘yan uwa. Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Misalin muminai wajen soyayyarsu da jin qan junansu da da tausyinsu kamar jiki guda ne, idan wata gaba ta kamu da rashi lafiya duk sauran jikin sai ya amsa da rashin barci da zazzabi” [Bukhari ne ya ruwaito].

Kuji tsoron Allah ya ku musulmi, ku sani cewa, ana nemanku da ku yiwa juna rahama da tausayi gwargwadon abin da za ku iya. Kuma mutum ya tausayawa iyalansa da makwabtansa da abokan aikinsa, kada ku taimakawa matanku akan yin sharri ko ‘ya’yanku.

Ku sani yana daga cikin faxin Manzon Allah (ﷺ) yana cewa:“Yana daga cikin girmama Allah ta’ala girmama musulmi mai furfura. da mahaddacin Qur’ani wanda baya qetare iyaka ko jafa’i. Da kuma girmama shugaba mai adalci. [Abu Dawud ne ya ruwaito shi].

Ku gu ji faxa cikin abin da Manzon Allah (ﷺ) ya hana inda yake cewa, “Baya tare da mu wanda ba ya tausayin na qasan mu, kuma bai san mutuncin manyan mu ba”. [Abu Dawud ne ya ruwaito shi].

Yana daga cikin amfanin tausayawa samun rabuta da yardar Allah a nan duniya da lahira. Allah yana cewa,

(وَمَنْ يُطِعِ اللَّهَ وَالرَّسُولَ فَأُولَئِكَ مَعَ الَّذِينَ أَنْعَمَ اللَّهُ عَلَيْهِمْ مِنَ النَّبِيِّينَ وَالصِّدِّيقِينَ وَالشُّهَدَاءِ وَالصَّالِحِينَ وَحَسُنَ أُولَئِكَ رَفِيقًا69) [النساء: 69]

(Duk wanda ya yi wa Allah xa’a da Manzonsa, to waxannan suna tare da waxanda Allah ya yi masu ni’ima daga Annabawa da masu gaskiya da shahidai da salihan bayi. Madallah da waxannan abokan tafiyar. Wannan falalace daga Allah kuma Allah ya isa ya zama masani).





Tags:




Abdurrahman Al-sudais