Tsoratarwa daga laifuffukan harshe


5988
Surantawa
Harshe niima ne daga cikin niimomin Allah a bayinsa, don haka ne ya wajabta akan bayi suyi godiya game da wannan niimar, wajen lura da hakkokin Allah game da shi, mutum ya kame shi daga barin abinda zai fusata ubangijinsa, hakanan yayi amfani dashi cikin abinda ze yardar da Allah. Haqiqa muhimmancin da manzon Allah ya baiwa wannan sashe baze kirgu ba, domin ya nuna cewa kiyaye harshe, ja-gaban dukkan alherai ne, kuma yana yawan nanatawa iyalinsa hakan, kai mafi yawan abinda ze shigar da mutane wuta ma , daga santsin harshensu ne. Don haka sai a kiyaye.
Manufofin huxubar Sabawa kai da faxar kyakkyawar magana da take yardar da Allah. Rabauta da yardar Allah. Nisantar miyagun maganganu. Huxuba Ta Farko Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma muna neman tsarinsa daga sharrin kawukanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar da shi, wanda kuma ya vatar to babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaxai ne ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi Muhammadu bawansa ne manzonsa ne. (Yaku waxanda suka yi imani ku ji tsoron Allah yadda ya cancaci a ji tsoronsa, kada ku mutu face kuna musulmi). (Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicceku daga rai guda xaya, kuma ya ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga garesu (su biyu). Ku ji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya da shi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Yaku wanxanda suka yi imani ku ku ji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku ayyukanku, kuma ya gafarta muku zunubbanku. Wanda ya bi Allah da Manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawon shiriya shiriyar Annab Muhammadu (ﷺ). Kuma mafi shirrin al'amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wani qagaggen abu (a addini) bidi'a ce, duk wata bidi'a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta". Ya bayin Allah: harshe ni’ima ce daga ni’imomin da Allah ya yi wa xan adam, an halittawa xan adam shi domin xanxanar abubuwa da kuma yin bayani. Allah yana cewa, أَلَمْ نَجْعَلْ لَهُ عَيْنَيْنِ8 وَلِسَانًا وَشَفَتَيْنِ9 وَهَدَيۡنَٰهُ ٱلنَّجۡدَيۡنِ10) [البلد: ٨ - ١٠] Ma’ana: “Shin ba mu sanya masa idanuwa biyu ba ne? da harshe da kuma lavva biyu, muka kuma shiryar da shi hanyoyi biyu, (ta alheri da ta sharri)..) Shi harshe dai shi ake gane mai azancin magana, kuma mai nuna hankali da shiriyar mai iya sarrafa shi ne. Amma duk da haka wasu da dama harshen su ne ya kai su ga qabari. Gwaraza ma suna tsoron haxuwa da illar harshe. Lallai kam babu abin da ke kifa fuskokin mutane a wuta sai abubuwan da harasansu suka girba musu. Ya ‘yan uwa! Ku sani cewa mumini, bawan da yake tsoron Ubangijinsa, ba ya sakin harshensa yadda ya ga dama, saboda Allah ya wajabta masa kame harshensa a kowane hali kuma ya hana shi yin dukkan abin da yake kishiyantar hakan, kamar yadda Allah ya hana shi yi da wani inda yake cewa: (وَلَا يَغْتَبْ بَعْضُكُمْ بَعْضًا أَيُحِبُّ أَحَدُكُمْ أَنْ يَأْكُلَ لَحْمَ أَخِيهِ مَيْتًا فَكَرِهْتُمُوهُ وَاتَّقُوا اللَّهَ إِنَّ اللَّهَ تَوَّابٌ رَحِيمٌ12) [الحجرات: 12] (Kuma kada shashinku ya riqa yin gibar shashi. Yanzu xayanku ya so ya ci naman xan uwansa yana matacce? Kun qyamaci hakan). An karvo daga Abu Barzatal Aslami, Allah ya yarda da shi ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ya ku taron waxanda suka yi imani da baki amma imani bai shiga zukatansu ba, kada ku yi da musulmai, kuma kada ku bibiyi tsiraicinsu, haqiqa duk wanda yake bibiyar tsiraicinsu, to shi ma Allah zai bibiyi tsiraicisa, duk kuwa wanda Allah ya bibiyi tsiraicinsa, to zai kunyatar da shi har a cikin gidansa”. Abu Dawud ne ya rawaito shi. Kuma Allah Ya hana mumini yin gulma, kamar yadda ya zo a hadisin Abdullahi xan Abbas, cewa haqiqa Annabin (ﷺ) ya gifta wasu qaburbura biyu sai ya ce: “Tabbas ana azabtar da waxanda suke cikisu kuma ba a kan wani abu mai wuyar bari ake azabtar da su ba. Laifin xayansu ba ya kaffa-kaffa da fitsari, xayan kuma yana yaxa gulma ne”. Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi. Bayan haka, yawan tsinuwa na daga cikin abubuwan da ke afka mata a cikin wuta, donn haka suka fi kowa yawa a wuta, kamar yadda yatabbata a cikin hadisin da aka karvo daga Abu Sa’idil Khudri cewa manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ya ku jama’ar mata ku yi ta yin sadaka, haqiqa na ga ku ne mafi yawan ‘yan wuta, sai suka ce: "Menene ya jawo hakan ya manzon Allah?" Sai ya ce: "Saboda kuna yawan tsinuwa da kuma butulcewa zama da miji”. Bukhari ne ya rawito shi. Ita kuwa kyakkyawar kalmar da take yardar da Allah, tana xaukaka darajar bawa ne. Ya tabbata a hadisin Abu Huraira da ke cikin Sahihil Bukhari, daga Annabi (ﷺ) ya ce, “Haqiqa bawa kan furta kalamar da take jawo fushin Allah, ba tare da bwan ya xauki kalmar a bakin komai ba, amma kuma sai ta jawo masa shiga wutar jahannama”. Ya bayin Allah! Haqiqa Annabin (ﷺ) ya bai wa wannan vangare matuqar muhimmanci inda ya xauki tsare harshe a matsayin mallakar alkhairi gaba xaya, kamar yadda ya zo a cikin hadisin Mu’az xan Jabal, Allah ya yarda da shi, wand Imamu Ahmada ya ruwaito ta hanya ingantacciya da lafazin kamar haka: “Ba na sanar da kai mamallakin dukkan alheri ba! Ka kame wannan"- Sai ya yi nuna harshensa-. Mu’az ya ce, "Ya Annabin Allah yanzu mu ababan kamawa ne da abin da muke yin magana da shi?" Annabi ya ce: A aha! Ya Mu’az ba ka sani babu abin da ke sa a kifa fuskoki mutane ko hancinsu a wuta ba, sai abubuwan da harasansu suka girba musu". Manzo ya kasance yana sa ido a kan iyalan gidansa a game da haka, yana tsaftace su da kare su daga afkawa maganganun da Allah ba ya so. An karvo daga A’isha Allah ya yarda da ita ta ce: "Na ce da Annabi ko ba komai Hafsa ‘yar duqurqusa ce". Sai manzon Allah ya ce: “Haqiqa kin faxi kalmar da inda za a cakuxa ta da ruwan kogi da ta jirkita shi”. Kuma na labarta masa labarin wani mutum sai ya ce “Ni ba zan yi gulmar wani ba, ko mai za a ba ni”. Tirmizi ne ya rawaito shi, kuma ya ce hadisi ne mai kyau ingantacce. Kuma Imamul Bukhari ya rawaito hadisi a cikin littafinsa na Al Adabul Mufrad ta ingantacciyar hanya, daga Anas Allah ya yarda da shi ya ce, Wani mutum ya yi jawabi a wajen Umar, sai ya yawaita magana, sai Umar ya ce: “Haqiqa yawan magana na daga ratatar shaixan". (wato surutunsa). Ya xan uwa, yi qoqari ka shagaltar da harshenka da ambaton Allah, da umarni da kyakkyawan aiki, da hani ga mummuna, da kuma daddaxan zance mai albarka wanda zai sama maka lada mai girma. Barin sa baki a cikin abin da ba zai amfane ka ba alama ce da ke nuna cikar musuluncinka. Kamar yadda yake cikin hadisin Abi huraira da yake cewa, “Yana daga kyauwn Musuluncin mutum ya bar abin da ba ruwansa”. Tirmzi ne ya rawaito shi. Kutsawa cikin tava mutuncin musulmai sifa ce daga sifofin munafukai, don haka ka nisanci shi iya iyawarka saboda hadisin Wasila Xan Asqa’i, daga Annabi (ﷺ) ya ce: “Haramun ne ga musulmi a kan musulmi zubar da jininsa, da cin mutuncinsa, da cin dukiyarsa. Musulmi xan uwan musulmi ne, don haka ba ya zaluntarsa, ba ya tavar da shi. Tsoron Allah a nan yake". Sai ya nuna zuciya, da hannunsa. Ahmad ne ya rawaito shi. Miyagun maganganu na daga cikin abubuwan da suka yaxu a cikin al’ummar musulmi a wannan zamani. Ina ganin babban abin da ya jawo hakan shi ne yaqar mu da Yahudawa suke yi ta kafofin yaxa labarai wanda a kodayaushe suke kai hari ga musulmai ta inda ba sa zato. An karvo daga Abud Darda’ daga Annabi (ﷺ), ya ce : “Babu abin da ya fi nauyi a ma’aunin ladan mumini a ranar alqiyama irin kyawawan xabi’u. Kuma haqiqa Allah na fushi da mai yin miyagun maganganu mai kaifin harshe". Tirmizi ne ya rawaito shi, kuma ya ce, hadisi ne kyakkyawa ingantacce. Yin raki kuwa a lokacin afkuwar musibu maguzanci ne, wanda musulmi aka hana mu yinsa, don haka ne ma aka umarce mu da yin haquri tun a karon farko a yayin arangama da musiba. Kuma aka sanya lada gwaggwava a kan hakan. An karvo daga Sabit ya ce: “Na ji Anas yana cewa da wata daga cikin iyalinsa, ko kin san wance? Haqiqa manzon Allah (ﷺ) ya wuce ta tana kuka a kan wani qabari, sai ya ce da ita, “Ki ji tsoron Allah ki yi haquri”, sai ta ce da shi, "Tafi ka ban wuri! kai ba ka ma damu da musibar da ta dame ni ba". Anas ya ce ba ta san Manzon Allah ne ba, sai aka ce da ita, ai manzon Allah (ﷺ) ne, sai tai ajiyar zuciya. Sai ta je qofar gidansa ta tarar babu mai gadi, sai ta ce, "Ya Manzon Allah ai ban san kai ba ne".Sai ya ce: “Ai haquri yana amfani ne a lokacin karon battar farko da masifa”. Ahmad da Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi. Ya bayin Allah! Haqiqa qarya da yaxa ta a tsakanin al’umma haramun ne, kuma laifi ne babba daga cikin manya-manyan laifuka. An karvo daga abdullahi xan Mas’ud daga Annabin (ﷺ) ya ce: “Na hana ku yin qarya, haqiqa qarya na kai bawa ga ayyukan kangara, kangara kuma na kai bawa ga wuta, haqiqa mutum yakan dinga yin qarya, kuma yana kirdadon qarya, har a kai ga rubuta shi maqaryaci a gurin Allah”. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi. Kuma dai an karvo daga Xan Mas’ud ya ce: “Qarya ba ta halatta ba da gaske ko da gangan, kuma bai halatta xayanku ya yi wa xansa alqawari ba, sannan ya qi cika masa”. Kuma Allah Maxaukaki ya umartar bayinsa muminai da tantance gaskiyar labari idan sun ji shi, ya ce:: (يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا إِنْ جَاءَكُمْ فَاسِقٌ بِنَبَأٍ فَتَبَيَّنُوا أَنْ تُصِيبُوا قَوْمًا بِجَهَالَةٍ فَتُصْبِحُوا عَلَى مَا فَعَلْتُمْ نَادِمِينَ6) [الحجرات: 6] “Ya ku waxanda suka imani, idan fasiqi ya zo muku da labari to ku tabbatar da (gaskiyarsa) don kada ku farma wasu jama’a bisa rashin sani sannan ku wayi gari kuna masu nadama bisa abin da kuka aikata”. Babban malami, sheikh Assa’idi ya ce a tafsirin wannan aya: “Wannan na daga cikin ladubban da suka zama lallai masu hankali su ladabtu da su, da yin aiki da su, wato idan wani fasiqi ya ba su labari su tabbatar da gaskiyar labarin, kada su kama shi daga jinsa haqiqa, kama labari daga jinsa haxari ne mai girman gaske, kuma faxawa ne cikin savo. Haqiqa idan aka xauki labarin fasiqi irin xaukar da ake yi wa labarin mai gaskiya da adalci za a kai ga yin hukunci da abin da labarin ya qunsa, ta dalilin haka sai a yi asarar rayuka da ta dukiya ba tare da dacewar hakan ba, a saboda wancan labari da ke jawo da-na-sani. Abin da yake wajibi yayin jin labarin fasiqi, shi ne tantance gaskiyarsa, idan dalilai da alamomi sun yi nuni gaskiyarsa sai a yi aiki da shi kuma gaskiya ya faxa. Idan kuwa dalidai suka yi nuni qaryarsa to ba a yin aiki da shi, kuma qarya ya faxa. Kuma hakan na xauke da cewa, labarin mai gaskiya abin karva ne, na maqaryaci kuwa abin watsi da shi ne, na fasiqi kuma abin a tsaya a yi bincike game da shi ne, kamar yadda muka ambata. Kuma don haka ne magabata suke karvar ruwayoyi da dama daga wajen Khawarijawa da aka san su da gaskiya ko da kuwa fasiqai ne». Allah ya yi mana gamon katar, ya ba mu dacewa cikin maganganunmu da ayyukanmu. Amin.
Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su tabbata a mafi xaukakar annabawa, kuma cikamakin annabawa da iyalansa da sahabbansa da wanda ya bi turbarsa har zuwa ranar sakamako. Bayan haka: Ya bayin Allah! Dalilai sun yin nuni a kan cewa Allah yana da mala’iku masu tsaron mutane, kamar yadda yake a cikin faxin Allah maxaukaki: (وَيُرْسِلُ عَلَيْكُمْ حَفَظَةً61) [الأنعام: ٦١]. (Kuma yana aiko muku da masu tsaro (daga mala’iku)) Kuma Allah ya ambata a cikin abubuwan da suke tsarewa xan adam sun haxa da dukkanin ayyukan mutum na alheri da na sharri da kuma maganganunsa, Allah ya ce: وَإِنَّ عَلَيْكُمْ لَحَافِظِينَ10) [الإنفطار: 10])Ma’ana: (Babu shakka akwai masu tsaronku). Kuma ya ce: (إِذْ يَتَلَقَّى الْمُتَلَقِّيَانِ عَنِ الْيَمِينِ وَعَنِ الشِّمَالِ قَعِيدٌ17 مَا يَلْفِظُ مِنْ قَوْلٍ إِلَّا لَدَيْهِ رَقِيبٌ عَتِيدٌ18) [ق: ١٧ – ١٨]. “Yayin da masu haxuwa biyu suke haxuwa ta hagu da kuma ta dama a zaune, ba wata magana da zai furta face tare da shi akwai mai tsaro halartacce”. Kuma dai Allah ya ce: (أَمْ يَحْسَبُونَ أَنَّا لَا نَسْمَعُ سِرَّهُمْ وَنَجْوَاهُمْ بَلَى وَرُسُلُنَا لَدَيْهِمْ يَكْتُبُونَ80) [الزخرف: 80] (Ko suna tsammanin cewa mu ba ma jin asirinsu da ganawarsu ne? Ba haka ba ne, manzanninmu ma sun tare da su suna rubutawa). A cikin Sahihul Bukhari da Muslim an karvo daga Abu Huraira ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Akwai mala’ikun da suke maye wasunsu a cikinku da daddare, da kuma mala’ikun da suke maye wasunsu a cikinku da rana, suna tattaruwa a lokacin sallar asuba da lokacin sallar la’asar, sannan sai waxanda suka kwana a cikinku su hau sama, sai Ubangijinsu ya tambaye su, duk da ya fi su masaniya game da ku, ya ce: "Yaya kuka baro bayina?" Sai su ce,"Mun baro su suna yin salla, kuma da muka je ma mun tarar da su suna yin salla”. Mai littafin Kasshaf, ya ce: “In da za ka ce: Ai Allah wadatacce ne da iliminsa game da rubutun mala’iku, wane amfani rubutn nasu yake da shi? Sai ince, amfanisa yin luxufi ga bayi, domin kuwa idan suka san Allah na sa ido da bibiya a kansu, kuma mala’ikunsa da su ne mafi xaukakar halitttarsa za a wakilta su a kan rubuce ayyukansu da kiyaye su don bijiro da su gaban shaidu a yinin qiyama zai fi sa su tsawatuwa da nisantar miyagun ayyuka". Ya bayin Allah! Bibiyar daidai a dukkanin maganganu shi ne kaxai mafita daga matsalokin da muka ambata, kuma da haka ne ayyuka za su kyutatu, kuma bawa ya dace da gafarar zunubansa, ya kuma dace da rabauta da samun yardar Allah. Allah yana cewa: (يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا اتَّقُوا اللَّهَ وَقُولُوا قَوْلًا سَدِيدًا70 يُصْلِحْ لَكُمْ أَعْمَالَكُمْ وَيَغْفِرْ لَكُمْ ذُنُوبَكُمْ وَمَنْ يُطِعِ اللَّهَ وَرَسُولَهُ فَقَدْ فَازَ فَوْزًا عَظِيمًا71 )[الأحزاب: ٧٠ – ٧١]. (Ya ku waxanda suka yi imani, ku ji tsoron Allah, kuma ku faxi maganar da take daidai ce, zai kyautata muku ayyukanku, ya kuma gafarta muku zunubanku, duk kuwa wanda ya bi Allah da manzonsa, to haqiqa ya rabauta tabauta mai girma). Kuma kamar yadda magana kan zamo mabuxin alheri, to haka kuma takan zamo mabuxin sarri. Kamar yadda Manzon Allah ya faxa a cikin hadisin Mu’azu wanda ya gabata, “Shin akwai abin da yake kifa mutane a cikin wutar jahannama a kan fuskokinsu, in ba abubuwan da harasansu suka girba ba). Ya zo cikin hadisi: “Wanda ya yi imani da Allah ranar lahira to ya faxi alheri ko ya yi shiru”. Don haka, karantar da mutane Alqur’ani madaidaiciyar magana ce, haka rawaito hadisan Manzon Allah, da karantar da shi, madaidaiciyar magana ce, haka kuma yaxa maganganun sahabbai, da na shugabannin malaman Fiqihu da hikimomin malamai, madaidaciyar magana ce, kamar yadda girmama Allah da tsarkake shi da yi masa kirari, wannan ma madaidaiciyar magana ce. Haka ma dai, kiran salla da iqama, Allah maxaukaki yana cewa: (إِلَيْهِ يَصْعَدُ الْكَلِمُ الطَّيِّبُ وَالْعَمَلُ الصَّالِحُ يَرْفَعُهُ10) [فاطر: ١٠]. (Zuwa gare shi daxaxan maganganu suke hawa). Kuma da yaxa madaidaiciyar magana ne darajoji da tabbatattun al’amura ke yaxuwa a tsakanin mutane, sai ya zama su ma suna kwaxayin xabi’antuwa da su. Ta hanyar yaxuwar mummunar magana ne vata da gurvatattun abubuwa suke yaxuwa. Daga nan sai ka mutane su canja, sun riqa aikin varna, suna kuma zaton su masu kyutata aiki ne. Ya bayin Allah mu riqa tuna faxar Allah: (لَا يَعْزُبُ عَنْهُ مِثْقَالُ ذَرَّةٍ فِي السَّمَاوَاتِ وَلَا فِي الْأَرْضِ وَلَا أَصْغَرُ مِنْ ذَلِكَ وَلَا أَكْبَرُ إِلَّا فِي كِتَابٍ مُبِينٍ3) [سبأ: 3]Ma’ana: (Babu wani abu koda kamar qwayar komayya yake ko mafi qanqanta ko mafi girma a sama yake ko a qasa da zai vuya ga Allah, face yana cikin littafin mai bayyanawa).




Tags:




Azumin Nafila